‘Yar uwa ki jiƙa abu kaza da kaza ki sha domin ki fitar da zaƙin da ke mararki kafin naƙudar haihuwa, ko kuwa wane karɓi wannan maganin ka kai wa iyalinka ka ce ta jiƙa ta rika sha maganin zaƙi ne.
Waɗannan su ne irin maganganun da za ka ji suna zagawa musamman tsakanin mu mata in sun haɗu da mai juna biyu. Toh amma fa mu a likitance ba mu san wani abu wai shi zaƙi a marar mace ba ballantana fitarsa a jikin mace gabatowar haihuwa.
Duk da irin wannan al’ada ta jima amma duk da haka mun shigo wani zamani yanzu da gurɓatattun labarai da bayanai marasa sahihanci na ilimi suka yawaita kuma ke kai komo tsakanin al’umma cikin kafafen sadarwa iri-iri. Ko me mutane suka ji ba duk ke tsayawa su yi nazari da binkice ba a kan:
Shin kaza ɗin nan da aka ce ya ma dace da ni kuwa?
Sannan daɗin abun aka faɗa amma menene illar da ka iya biyo baya in an sami kuskure?
Shin haka ma batun yake a ilmance ko kuwa ya ne?
Shin ita ko shi me wannan bayanin meye matakin iliminsa, da me ya dogara, medical doctor ce ita?
Rashin wannan nazarin yasa da zarar haihuwa ta gabatowa mace kowa sai ka ga shawara yake ba ta akan komi ma, wanda 99% an ce ka ce ne ba wani sahihanci, musamman ma a tsakanin mu mata. Eh mun san ana yi ne bisa kyakkyawar manufa da son mu ga na haihu lafiya…. amma fa ba duk ‘yan Adam ba ne zubin halittarsu tare da komi nasu yai daidai da na juna ba.
Ba mamaki wata kuka ji ta yi irin hakan ta wanye lafiya, amma muke tunawa fa idan wani ya yi abu ya kwana lafiya toh fa wani in ya yi wahala zai sha. Babu wani abu me suna zaƙi jikin mai juna biyu, in aka ce zaƙi a jika to fa mu ko yaushe a likitance abunda muka shina; ana batu ne na ciwon suga a jikin mutum, wato yawaitar sinadarin glucose a cikin jini.
Shi ko ciwon suga yayin goyon ciki “gestational diabetes” sunansa, kuma muddin aka gano shi ba a wata-wata ake ɗora mace kan shawarwarin abinci ko magunguna wasu lokutan allura domin ba ta kariya daga hatsarin suga da ka iya tasowa! Wanda cikin irin wannan hatsarin akwai mutuwar jariri a ciki, mutuwar macen wajen haihuwa, zubewar ciki, ko haihuwar yaro babu ƙafafu, ko sanya jariri ya yi girma fiye da kima a ciki ta yadda ba zai iya haifuwa ta farji ba sai dai a yi aiki a ciro shi, ko kuwa sai an ƙara faɗin farjin mace kafin kan jariri ya iya wucewa.
Domin wasu kan ɗauka kowanne ƙatoton jariri lafiya ce ta sa, amma inaa wani girman ba na ƙa’ida ba ne larura ce, galibi alama ce ta larurar suga yayin goyon ciki a uwar musamman a macen da ba ta riƙa zuwa awo ba, ko kuwa ba ta sami duk gwaje-gwajen da suka dace ba, kurum an auna arziki ne. Duk jaririn da nauyinsa ya wuce 4.0 kilogram lafiyar mahaifiyarsa abin tuntu6a ce a yayin goyon cikinsa.
Ita kuwa wannan sugar a jini take ba za ta ta6a fita ta farji ko ta hanyar fitar da wani ruwa ba. Don haka abinda muka sani na ruwa a jikin mkace da ke fara leaking gabatowar haihuwa shi ne ruwan da ake kira AMNIOTIC FLUIDS wanda kuma wannan ruwa ne da jariri kan fara taruwa tun daga sanda ciki yai sati 4 inda ake fara iya ganinsa a scanning daga sati 8 na juna biyu.
Wannan ruwan amniotic cikinsa jariri ke rayuwa, yana kuma samuwa ne daga abinda macen ke sha na abinci da kuma fitsarin jaririn. Eh jariri na fitsari tun a ciki wanda shi ne wannan amniotic ɗin ke taruwa kuma a ƙarshe shi ne zai shanye abinsa yayin ƙishirwa da kansa sannan ya ƙara fitsarar da shi, haka zai ta recycling ɗin abinsa duk bayan awa 3, saboda mabiyiya (placenta) ɗinsa na tace masa shi. A kullum sai jariri ya yi fitsari kwatankwacin moɗa biyu wato 500milliliter.
Wannan ruwan har ila yau da taimakonsa; Jariri ke motsi da juyi a ciki, shi ke taimakawa huhun jariri samuwa, shi ke sa ciki girma, shi ke samarwa da jariri kyakkyawan yanayi wato temperature, sauƙin naƙuda tare da samuwar cikakkiyar halittarsa ta ɗan Adam a jika ya zamto ba a haife shi da tawaya ba irin; ƙaramin ƙoƙon kai, guntulallen hannu, yamutsatsiyar fata, kayan ciki a waje, da dai sauran ababen gudu masu illah.
Toh menene ma yasa ake kiran ruwan da sunan zaƙi ne?
Wataƙila sakamakon kalar ruwan amniotic ɗin ne da takan canza ya zamo ya yi kalar ƙasa-ƙasa kamar dafaffen ruwan sikari me kauri shi yasa mutane ke kiransa da ruwan zaƙi tunda ya yi kalar dafaffen sugar amma ba zaƙin ne da shi ba suffarsa ce kurum kamar abin zaƙi a ido. Hasali ma in da mutum zai ɗanɗana shi zai ji kamar ɗanɗanon kori yake.
Ruwa ne da a farkon ciki kalarsa haske ne da shi kamar ruwan sha, sai dai yayin da ciki ya tsufa yakan canza launi sannan yawansa ya fara raguwa ta yadda yake fara fita a yayin da ciki ya gama cika watannin isa haihuwa wato sati na 37, 38, 39, ko 40.
Wannan ruwan yana fara fita alama ce ta bakin mahaifar mace na shirin soma buɗewa (cervix dilatation) wato naƙuda, wanda hakan ke nuni da ta shirya cikinta zai fara murdawa (contraction) domin juye lodin da ke cikin mahaifarta na tsawon watanni (jariri).
Abin tsoro shi ne a ce wannan ruwan ya soma fita alhalin ciki bai gama cika watanninsa ba koma a ce sam ba kusa da watannin haihuwa mace take ba, ko kuwa a ce ba haihuwar ba ce ta gaske, shi ne ma muke kiran irin wannan mummunan yanayi da premature membrane rupture wanda hakan na nuna za a haifo bakwaini ko kuwa wanda dai bai gama cika halitta ko watannin haihuwa ba.
Infact yaron ma na iya mutuwa tun a ciki, sannan hakan zai iya barin ki da infection me tsanani da zai iya keta mahaifarki ya yi miki illa ko bayan haihuwa, ko nan gaba zaman wani cikin ya yi wahala.
Don haka a nan nake jan hankalin mu mata game da wannan kuskuren na shaye-shayen abubuwa da sunan wannan ruwan ya fashe ya rika fita tun kafin lokacin haihuwa bisa tunaninsu na cewa zaƙi ne kuma abu ne da ya dace a fitar don kar ya jawo matsala wajen haihuwa da su daina.
Gaskiya karatun ba haka yake ba yadda kuke tunani ko ake ɗoraku a kai. In wannan abin ya fashe alhalin ba naƙuda ba ce ta to wannan ke iya sa yaro ya maƙale wajen haihuwa sai dai a yi wa mace aiki, ko ta haihu a wuyace, koma ta haihu jini ya ɓalle ta zo ita ta rasa ranta, ko yaron ya haɗu da infection kwana 1 ko biyu ko ɗan sama da haka da haihuwa jariri ya mutu, ko kuwa a haifo yaro ya taso a wani dolo-dolo ko shasha saboda wahalar naƙuda.
Ya dace ai hankali a san cewa yanzu kullum ƙara wayewa al’ummar duniya ke yi, ko a likitance duk minti guda sai wani sabon abu ya ɓullo, wannan tasa hatta bayanai wasu za ku ga suna canzawa.
Kuma kema da hankalinki tunda kike zuwa awo wato “antenatal care” kin taɓa jin cewa an gano wai kina zaƙi a mara? Ba ki taɓa jin ma’aikatan lafiya sun ce miki ga wani magani da za ki sha ba saboda ki fitar da zaƙi gabannin haihuwa don gudun matsala… toh ko wannan bai isa ku gane ba.
In ma al’ada ce aka gada su ma ku sani cikin duhu suka riƙa yi, iya iliminsu kenan, sannan rayuwarsu ta bambanta da tamu. Daga cikin al’ada yau ina al’adar zubar da colostrum wato ruwan nono na farko me ruwan rawaya-rawaya ko zallar madara me kauri da mace ke fara samarwa bayan haihuwa….! Ko kun san da iyayen mu matse shi ake a zubar a ce ai illah ne da shi ba a bai wa jariri, in ma mace ta kasa matso shi babba ne zai sa baki ya zuƙe mata shi har sai sun tabbatar sun zubar da shi.
Amma bayan binkicen masana akan hakan sai ga shi an gano ai wannan ruwan nonon da ake zubarwa na farkon ya fi duk wani abu da jariri zai ci ko ya sha inganci, ya fi kowanne ruwan nono inganci tare da haɓɓaka lafiyar jariri da ba shi kariya daga cuttuka. Yau ba ga shi sai tarihi ba, wasu ma basu san an riƙa hakan ba a baya.
Kusani wannan ruwan ba zai ta zama har abada ba, shi a karan kansa da lokacin haihuwa ya zo zai huje ya soma fita wanda hakan shi zai sa bakin mahaifa taushi ya buɗe yai santsi yadda jariri zai fita cikin aminci. Wannan shi ne saƙon, ku daina shan komai, in kuma an ƙi to Allah raba bawa da wahala.
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu
