Tag: SHAYIN DANYAR CITTA DA LEMON TSAMI

  • Yadda Ake Shayi Kala-Kala (TEA)

    Yadda Ake Shayi Kala-Kala (TEA)

    Yadda ake Shayin abarba

    Abarba
    bawon Abarba
    citta
    kaninfari
    ganyen shayi

    Yadda ake haɗawa:

    Ki ɓare abarbarki ki yanka kaɗan, ba da yawa ba, ki haɗa da ɓawon abarbarki, ki zuba a tukunya, bayan ya fi abarbar yawa, sai ki saka citta da kaninfarin da kika dɗan daddaka su ki saka Lipton, ki haɗa ki tafasa sosai, ki sa sugar sai sha.

    GORIBA TEA

    Goriba
    citta
    kaninfari
    ɓawon bayan lemon zaƙi
    Lipton

    Yadda ake haɗawa

    Za ki samu goriba irin ɓararriyar nan, wadda aka fidda ta daga jikin ƙwallonta, sai ki wanke ta, ki sa a tukunya, ki zuba citta Da kaninfari sannan ki samu ɓawon lemo, ki ɗan goga shi a ciki da abun goga carrot, amma fa kar ki cika da yawa, don ƙamshin muke buƙata kaɗan, sai ki saka Lipton Da dan sugar, ki barsu su yi ta dahuwa, sai ki bar shi ya dahu, sosai komai na jikin goribar ya futo sosai, wannan shayin na da daɗi sosai, kuma yana ƙara wa maza da mata lafiya ƙwarai da gaske.

    SHAYIN ƊANYAR CITTA DA LEMON TSAMI

    Danyar citta
    Lemon tsami
    Lemon grass
    kaninfari
    Na’ana,
    Lipton

    Yadda ake haɗawa

    Ki goga cittarki daidai misali ya danganta da yadda kike son yajinta, ki saka Lemon grass Da na’ana, ki yanka Lemon tsaminki gida biyu ki jefa a ciki, kisa Lipton da sugar ki tafasa sosai. In kina Da bukatar tsamin, kya iya matsa ruwan lemon tsamin in kin zo sha.

    CINNAMON AND HONEY TEA

    cinnamon (girfa)
    honey (zuma)
    citta
    kaninfari
    lemon grass

    yadda ake haɗawa:

    Ki zuba ruwa a tukunya ki zuba garin cinnamon ko wanda ba a niƙa ba, ki saka kaninfari Da citta Da Lemon grass, ki tafasa sosai, in ya dahu, ki zuba zuma ki bar shi ya yi ta tafasa, da ya tafasa sai ki sauke.