Tag: Kosan Dankali Mai Hade Da Nama

  • Yadda Ake Ƙosan Dankali Mai Haɗe Da Nama

    Yadda Ake Ƙosan Dankali Mai Haɗe Da Nama

    KAYAN HAƊI

    • Dankali
    • Nama
    • Kwai
    • Attaruhu
    • Albasa
    • Maggi
    • Gishiri
    • Man gyaɗa
    • Fulawa ko garin busashen buredi

    *YADDA AKE HAƊAWA*

    Da farko ki wanke nama ki zuba a tukunya, sai ki zuba maggi da gishiri, ki tafasa sai ki kwashe ki zuba a turmi ki jajjaga tare da albasa da attaruhu, idan ya yi laushi, sai ki kwashe a kwano ko roba, sannan ki dawo ɗan dankalin Turawa ki tafasa ya yi laushi, sai ki murmushe shi ko kuma ki jajjaga a turmi, sai ki kwashe shi a cikin kwanon da kika kwashe naman da kika jajjaga, sai ki ɗauko ƙwai ɗanye ki fasa a kai, ki zuba fulawa ko garin busasshen buredi a ciki, ki sa gishiri da maggi ki juya sosai, ki ɗauki farantin suya ki zuba man gyaɗa ki ɗora a kan wuta ki dinga ɗiba kina zubawa a cikin man gyaɗa mai zafi idan ya soyu za ki ga ya yi brown sai ki kwashe ki yi wa Oga ya yi breakfast da shi.

    ƘOSAN DANKALI

    *KAYAN BUƘATA*

    • Dankalin Turawa
    • Nama
    • Fulawa
    • Kwai
    • Albasa
    • Attaruhu
    • Gishiri
    • Maggi
    • Man gyaɗa

    *YADDA AKE YI*

    Ki jajjaga albasa da attaruhu, ki kwashe a kwano ko roba, sai ki ɗauki dankali, ki tafasa ki zuba a turmi ki daka shi, amma kar ya yi laushi sai ki kwashe a cikin kwanon da kika zuba jajjagen attaruhu da albasa, ki tafasa nama shi ma ki daka a turmi, duk ki hada da sauran kayan haɗin ki juya, sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan ƙwai, ki juya shi a cikin fulawa ki jefa a cikin man gyaɗa mai zafi ki soya , akwai daɗi matuƙa.