Tag: Huɗubar Juma’a

  • Fassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya daga Masallaci mai Alfarma 7th Nuwamba 2025

    Fassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya daga Masallaci mai Alfarma 7th Nuwamba 2025

    Fassarar huɗubar Juma’a kai daga Masallaci mai alfarma, ta yau Juma’a 16 Jumadal Ula, 1447 H / 07 November, 2025 M

    Mai Huɗuba:  Sheikh Dr. Abdallah bin Awwad Aljuhani

     Mai Fassara: Dr Abdullahi Yunusa Machina

    Transcribe: Aminu Bashir

    Huɗuba ta farko:

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, muna yaba masa, muna neman taimakonsa, kuma muna neman gafararsa. Kuma muna neman tsarin Allah daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar da shi, to babu mai ɓatar shi, kuma duk wanda ya batar, to babu mai shiryar da shi.

    Kuma ina shaidawa lallai babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa. ((Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku ji tsoron Allah matuƙar tsoronsa, kuma kada ku mutu face kuna musulmi)).

    ((Ya ku mutane! Ku ji tsoron Ubangijinku wanda Ya halicce ku daga rai guda ɗaya, kuma Ya halicci matarsa daga gare shi, kuma Ya yaɗa maza da mata masu yawa daga gare su, kuma ku ji tsoron Allah wanda kuke yi wa juna magiya da shi, kuma ku kiyaye yanke zumunta, lallai Allah Ya kasance Mai kula da ku ne)).

    ((Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku ji tsoron Allah kuma ku faɗi magana wacce take daidai, Zai gyara muku ayyukanku, kuma Ya gafarta muku zunubanku, kuma duk wanda ya yi ɗa’a ga Allah da Manzonsa to haƙiƙa ya rabauta rabauta mai girma)).

    Bayan haka: Ina yi muku wasiyya da ni kaina da duk wanda ya ji maganata da jin tsoron Allah Mai girma da ɗaukaka, wanda Ya halicci bayi, kuma zuwa gare shi makoma take, kuma gare shi ake neman dacewa da shiriya, domin jin tsoronsa riba ce, kuma kariya ce daga azabarsa, kuma hanya ce ta samun kusanci zuwa gare Shi.

    Kuma ku kiyayi sauyawar ni’imar Allah gare ku, kuma ku lizimci jama’arku, kuma kada ku kasance ƙungiya ƙungiya, kuma lallai mafi wayo cikin mutane shi ne wanda ya yi wa kansa hisabi, kuma ya yi aiki don abin da ke bayan mutuwa, kuma ya nemi hasken da zai haskaka duhun kabarinsa da shi daga hasken Allah.

    Kuma lallai bawa ya ji tsoron Allah Ya tashe shi makaho ranar ƙiyama alhali ya kasance yana gani a duniya. Kuma ku sani cewa lallai duk wanda Allah yake tare da shi, to ba zai ji tsoron komai ba; kuma duk wanda Allah baya tare da shi, to wa zai yi fatan samun kariya daga gare shi koma bayansa.

    Ya ku taron muminai maza da mata: Lallai daga cikin manyan ni’imomin Allah ga halittunsa akwai cewa Ya shiryar da su kuma ya nusar da su zuwa ga yin imani da Shi, kuma Ya bayyana musu falalar da Ya yi musu, Allah Maɗaukaki ya ce: ((Gori suke maka don sun musulunta?; to ka ce: “Kada ku yi min gorin musuluntarku; a’a, Allah ne ma zai yi muku gori don Ya shiryar da ku zuwa ga imani, idan kun kasance masu gaskiya”)).

    Kuma imani da Allah Maɗaukaki shi ne tabbataccen gaskatawa da ƙudurta cewa lallai Allah shi ne Ubangijin dukkan komai kuma Mamallakinsu, kuma Mahaliccinsu, kuma Mai gudanar da su; da kuma cewa lallai Shi kaɗai ne wanda ya cancanci bauta, kamar Salla da Azumi da addu’a da fata da tsoro da ƙasƙantar da kai da rusunawa, da kuma cewa lallai Shi ne wanda ya siffantu da dukkan siffofin kamala, Wanda Ya tsarkaka daga kowane aibu da tawaya.

    Kuma ku sani – Allah Ya ya muku rahama – cewa lallai imani ba wata magana ce mai daɗi da ake furtawa da baki kawai ba, ko wasu burace-burace ba tare da aiki ba, bari dai, shi ne abin da ya tabbata a cikin zuciya kuma ayyuka suka gaskata shi, kuma shi furuci ne da harshe, da gaskatawa da zuciya, da kuma aiki da gaɓɓai da sassan jiki, yana ƙaruwa da ayyukan ɗa’a kuma yana raguwa da ayyukan saɓo.

    Kuma imani da Allah Maɗaukakin sarki shi ne tushen dukkan rabauta, domin ba a saukar da littattafai ba, kuma ba a aika manzanni ba, face don tabbatar da shi, da kuma dasa shi a cikin zukata, domin shi ne tushe mafi girma kuma rukuni na farko daga cikin rukunan imani guda shida.

    Kuma shi imani kyauta ce daga Allah, kuma ni’ima ce mai girma a rayuwar musulmi, ni’ima ce wacce take tsarkake shekaru, kuma ta sanya albarka a cikin rayuwa, kuma ta bada lamunin samun rabauta a lahira, kuma ta ɗaga darajar ma’abocinta a duniya da lahira, domin a cikinta ne rayuwa ta gaskiya da farin cikin lahira suke.

    Kuma wannan ni’ima babu wanda ya san ta sai wanda ya ɗanɗana ta, kuma babu wanda zai ji daɗinta sai wanda ya rayu a cikinta, kuma shi imani haske ne mai shiryarwa mai haskakawa, Allah yana ba da shi ga wanda Yake so daga cikin bayinsa, kuma Yana hana ta ga wanda Ya ga dama.

    Allah Maɗaukaki Ya ce: ((Ka ce: “Lallai Allah Yana ɓatar da wanda Ya ga dama, Yana kuma shiryar da wanda ya koma gare Shi)), kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa ya ce: (Duk wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, kuma ya yarda da Musulunci a matsayin addini, kuma ya yarda da Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa a matsayin Annabi, to lallai ya ɗanɗani daɗin imani). Muslim ne ya rawaito shi.

    Kuma imani na gaskiya wanda Allah yake so, shi ne tushen kowane alheri, kuma maɓuɓɓugar ɗaukaka, kuma asalin karama da daraja da jagoranci, ma’abocinsa yana rayuwa cikin ɗaukaka da farin ciki da ƙarfi da tabbata a kan hanyar gaskiya.

    Kuma haƙiƙa Allah Maɗaukaki ya yi wa masu imani da kuma ɗa’a alkawarin samun nasara da kafuwa a doron ƙasa a cikin bayani mai daraja inda Ya ce: ((Wannan bayani ne don mutane, kuma shiriya ce da kuma wa’azi ga masu taƙawa. Kuma kada ku yi rauni, kada kuma ku yi baƙin ciki, kuma ku ne mafiya ɗaukaka in dai har kun kasance muminai Idan ma wani miki ne ya same ku a jiki, to haƙiƙa miki irinsa ya samu mutanen Makka.

    Kuma waɗannan kwanaki ne da muke jujjuya su tsakanin mutane domin Allah Ya bayyanar da waɗanda suka yi imani, kuma Ya riƙi shahidai a cikinku. Allah kuwa ba Ya son azzalumai Kuma don Allah Ya tace waɗanda suka yi imani, kuma don Ya halakar da kafirai.))

    Kuma masu imani suna farin ciki da jiɓantar Allah Maɗaukaki a gare su, kuma suna ni’imtuwa da daddaɗar rayuwa, kuma Allah yana son su, kuma muminai ma suna son su, kuma Allah Maɗaukakin sarki yana basu kariya, kuma suna da albishir a rayuwar duniya da lahira, kuma imani na daga cikin mafi girman abababen da ke sanyaya musu zuciya yayin masifu, Allah Maɗaukaki ya ce: ((Ba wata musiba da za ta samu sai da izinin Allah. Duk kuwa wanda ya yi imani da Allah zai shiryi zuciyarsa. Allah kuma Masanin komai ne)).

    Kuma su ne ma’abota tsaro da kwanciyar hankali, kuma suna gaggawar zuwa ga imaninsu, kuma suna samun ƙarfi da shi cikin duk abin da ya same su na alheri ko na sharri, na ɗa’a ko na saɓo, na sauƙi ko na wahala. Kuma suna amfana da wa’azi da tunatarwa, kuma suna cikin kulawar Allah Maɗaukaki.

    Kuma imaninsu yana kare su daga faɗawa cikin alfasha, kuma da hasken imaninsu suke bambance tsakanin gaskiya da ƙarya, da shiriya da ɓata, da kuma bidi’a da sunna.
    Kuma haƙiƙa Allah Maɗaukaki ya yi musu alkawarin samun nasara da kafuwa, kuma su ne ma’abota buwaya da ɗaukaka, Allah Maɗaukaki Ya ce: ((kuma taimakon muminai ya zama haƙƙi ne a kanmu)).

    Kuma Mala’ikun da suke ɗauke da Al’arshin Allah Mai rahama suna nema musu gafara, kuma Allah Maɗaukaki yana shiryar da su da imaninsu zuwa hanya madaidaiciya.
    Kuma Allah Maɗaukaki yana musu albishir da samun aminci da farin ciki a duniya da lahira, da kuma dawwamammiyar ni’ima a lahira.

    Allah Maɗaukaki Ya ce: ((Lalle waɗanda suka ce: “Allah ne Ubangijinmu”, sannan suka tabbata, to mala’iku za su sauko musu lokacin mutuwa suna cewa: “Kada ku tsorata, kuma kada ku yi baƙin ciki, kuma ku yi farin ciki da Aljanna wadda kuka kasance ana yi muku alƙawarinta “Mu masoyanku ne a rayuwar duniya da kuma ta lahira; kuma a cikinta za ku samu duk abin da rayukanku suke marmari, za kuma ku samu duk abin da kuke nema a cikinta“Liyafa ce daga Allah Mai gafara, Mai jin ƙai”)).

    Bayan haka, ya ku muminai: Haƙiƙa hikimar Allah Maɗaukaki ta hukunta cewa Ya sanya wannan al’umma ta zamo mafi alherin ul’umma wacce aka fitar ga mutane, tana umarni da kyakkyawan aiki, kuma tana hana mummuna, kuma tana imani da Allah.
    Kuma Allah tsarki ya tabbata a gare Shi Ya umurce su da yin ayyuka nagari inda Ya ce: ((Kuma ku aikata ayyuka nagari, lallai Ni Masanina abin da kuke aikatawa ne)).

    ma’abocinsa dukkan alheri a duniya da lahira, kuma shi garkuwa ne da bawa yake kare kanshi daga sha’awace-sha’awace da shubuhohi da manyan fitintinu da shi, kuma shi waraka ne ga zukata.

    Wanda duk lokacin da mutum ya gafala daga barin shi saboda kwaɗayin wani abin duniya mai ƙarewa, sai rayuwarshi ta ƙuntata, kuma zuciyarshi ta kamu da jinya, kuma lallai idan ka dubi dayawa daga cikin koke-koke da damuwowi da baƙin ciki da tsoro da taɓarɓarewar al’amura a rayuwar mutane, za ka ga alamomin nisantar imani da Allah Mai girma da ɗaukaka da bijire wa addininsa da shari’arsa a cikinsu.

    A’uzu billahi minash-shaiɗanir-rajim, Bismillahir Rahmanir Rahim: ((Waɗanda suka yi aiki nagari, na miji ne ko mace, alhalin suna muminai, to tabbas za mu raya su rayuwa mai daɗi, kuma tabbas za mu saka musu ladansu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa)).

    Allah Ya amfanar da mu da Alƙur’ani mai girma, da shiriyar shugaban Manzanni, ina faɗi abin da kuka saurara, kuma ina nema mana gafar Allah, da sauran musulmi daga kowane zunubi, don haka ku nemi gafarsa, lallai shi Mai yawan gafara ne Mai jin ƙai.

    Huɗuba ta biyu:

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah bisa kyautarsa da kyautatawarsa, kuma godiya ta tabbata gare shi bisa falalarsa da ni’imominsa, kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa, ya Allah Ka yi daɗin tsira da aminci ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu da alayensa da sahabbansa.

    Bayan haka:

    Ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah, kuma ku tabbatar da imaninku da Ubangijinku, kuma ku sani cewa lallai Imani da Allah Mai girma da ɗaukaka yana sanya yarda da Allah Mai grima da ɗaukaka a zuciyar mumini a kowane hali, kuma yardar bawa ga Mahaliccinsa shi ne farkon sababi daga cikin sabuban natsuwar zuciya, wacce ita ce asalin rabauta, domin da yardar mutum da kansa da abin da Allah Ya ƙaddara masa ne zai samu natsuwa a kan hali da yake ciki yanzu, da kuma yaƙininsa da lahira da sakamako na adalci ne zai samu natsuwa game da gobenshi.

    Ma’anar haka, shi ne cewa lallai mumini ba ya cizon yatsa a kan abin da ya shuɗe ta hanyar kuka ko baƙin ciki, kuma ba ya rayuwa cikin baƙin ciki a kan yanayi da yake ciki, kuma ba ya fuskantar gobe da tsoro, saboda a cikin addininsa akwai makamai da zai yi dogaro da su wurin dogewa a kan gwagwarmayar rayuwa, kuma ya fuskanci masifunta da raɗaɗinta da bala’o’inta da su.

    Saboda haka, ahir ɗinka kuma ahir ɗinka da rabuwa da yarda da Ubangijinka ko da daidai da ƙiftawar ido ne, sai darajarka ta faɗi a wurinsa, saboda akwai ƙarfin rai da yarda da shi, da natsuwar zuciya a cikin ƙulla alaƙa da Allah, Allah Maɗaukaki Yana faɗi a cikin littafinsa mai girma: ((Ya ku waɗanda kuka yi imani ku nemi taimako ta hanyar haƙuri da salla. Lallai Allah Yana tare da masu haƙuri)).

    Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan wani abu ya tsananta a gare shi, sai ya garzaya zuwa ga salla, kuma sallarsa ba ta kasance wani abu na al’ada ne kawai da yake yi ba, bari dai, ta kasance kaiwa maƙura ne wurin ganawa da Allah, har ma ya kasance idan lokacinta ya yi sai ya ce wa sahabinsa Bilal Allah Ya ƙara masa yarda: (Ka hutar da mu da salla), wato ita wannan salla ya ku muminai tana ɗauke da makullan rayuwa da wani sashi na hanyoyin rayuwa cikin nutsuwa, don haka, ku dogara da ita saboda ku rabauta.

    Ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah, kuma ku kiyaye shi, kuma ku ɗau izina daga waɗanda suka shuɗe gabaninku, kuma ku sani cewa lallai babu makawa sai kun haɗu da Ubangijinku kuma zai muku sakamako a kan ayyukanku ƙananansu da manyansu sai dai abin da Allah Ya gafarta shi, lallai Shi Mai gafara ne Mai jin ƙai, saboda haka, ku kula da kawunanku, ku kula da kawunanku, kuma ku nemi taimakon Allah, kuma ba mu da wata dabara ko ƙarfi face da Allah.

    ((Lallai Allah da Mala’ikunsa suna salati ga Annabi. Ya ku waɗanda kuka yi imani ku yi salati a gare shi da sallama mai yawa)). Ya Allah Ka yi salati ga Annabi Muhammadu da alayen Annabi Muhammadu, kamar yadda Ka yi salati ga Annabi Ibarahim da alayen Annabi Ibrahim, Lallai Kai Sha yabo ne Mai girma, kuma Ka yi albarka ga Annabi Muhammadu da alayen Annabi Muhammadu, kamar yadda Ka yi albarka ga Annabi Ibrahim da alayen Annabi Ibrahim, lallai Kai Sha yabo ne Mai girma.

    Ya ku bayin Allah, ku Yawaita salati da sallama ga mafakar halittu a matsaya mai girma ranar alƙiyama, Annabinmu kuma mai cetonmu Annabi Muhammadu tsira da maincin Allah su tabbata a gare shi, kuma Ka masa sallama mai yawa.

    Kuma ya Allah Ka ƙara yarda da halifofi huɗu shiryayyu da sauran sahabbai gaba ɗaya, da tabi’ai, da waɗanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako, ya Allah Ka amfanar da mu da son da muke musu, kuma ya Allah Ka tashe mu a cikin tawagarsu, kuma kada Ka kautar da mu daga bin sunnarsu da tafarkinsu, ya Mafi karamcin masu karamci.

    Ya Allah Ka ƙarfafi Musulunci da musulmai, kuma Ka ɗaukaka kalmar gaskiya da addini da falalarka, ya Allah Ka taimaki shugabanmu kuma majiɓincin lamuranmu hadimin Masallatai biyu masu alfarma da gaskiya da dace da daidai, kuma Ka datar da shi ga abin da Kake so kuma Ka yarda da shi, kuma Ka yi riƙo da hannunsa zuwa ga ayyukan nagarta da taƙawa.

    Ka azurta shi da mashawarta nagartattu, Ka ɗaukaka addininka da kalmarka da shi, kuma ka sanya shi ya taimaki musulunci da musulmai, kuma ka haɗa kan musulmai bisa gaskiya da shiriya ta dalilinsa ya Ubangijin talikai, ya Allah Ka datar da shi da magajinshi da ‘yan’uwansa da mataimakansa zuwa ga gaskiya da shiriya, da dukkan abin da gyara ne ga bayi da ƙasa.

    Ya Allah Ka datar da shugabannin musulmai zuwa ga aiki da littafinka da sunnar Annabinka Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Ka sanya su su zama rahama ga bayinka muminai, kuma ya Allah Ka haɗa kawunansu a kan gaskiya ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah Ka ƙarfafa kariyarka ga ƙasarmu da dukkan ƙasashen musulmi, kuma ya Allah Ka datar da jami’an tsaronmu da masu dako a kan fagage da iyakoki, kuma Ka zama Mai taimako da kawo ɗauki da agazawa da ba da nasarar a gare su.

    Ya Allah lallai muna tawassuli da yardarka, Ka tsare mu daga fushinka, kuma muna tawassuli da amincinka, Ka tsare mu daga azabarka, kuma muna neman tsarinka daga damƙarka, ba za mu iya ƙididdige yabo a gare Ka ba, Kana nan kamar yadda Ka yabi kanka.

    Ya Allah kada Ka mana uƙuba da munanan ayyukanmu, kuma kada Ka kama mu da abin da wawayen cikinmu suka aikata, kuma Ka isar mana a kan dukkan wani lamari da yake damun mu, kuma Ka zama mai taimako da ba da nasarar gare mu. Ya Allah Ka taimaki addininka, da littafinka, da sunnar Annabinka tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a kowane waje, ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah lallai muna neman gafararka, lallai Kai Ka kasance Mai yawan gafara ne, Ka sauko mana da ruwan sama mai yawa, ya Allah Ka saukar mana da ruwa, ya Allah Ka saukar mana da ruwa, ya Allah Ka saukar mana da ruwa, ya Allah lallai mu halittu ne daga cikin halittunka, kada Ka hana mana falalarka saboda zunubanmu.

    Ya Allah Ka gafarta mana, da iyayenmu, da dukkan musulmai maza da mata, da muminai maza da mata, rayayyu daga cikinsu da mamata. Ya Allah Ka karɓa daga gare mu, lallai Kai Mai ji ne kuma Masani, kuma Ka karɓi tubanmu, lallai Kai Mai yawan karɓar tuba ne Mai jin ƙai.

    Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin buwaya daga abin da suke siffanta shi da shi, kuma aminci ya tabbata ga Manzanni, kuma dukkan yabo ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

    Karanta Fassarar Huɗubar Juma’a Rubutacciya Daga Masallaci Mai Alfarma 31st Octoba 2025

    Edita@rumasau-kallamu

  • Fassara Huɗuba Daga Masallaci Mai Alfarma 24th January 2025

    Fassara Huɗuba Daga Masallaci Mai Alfarma 24th January 2025

    Sheikh Dr Saleh Bin Abdullahi Bin Humaid

    Mai Fassara:
    Dr Abdullahi Yunusa Machina

    Shugaban Shashi
    Dr Abdurrahman Muhammad Sani Yakubu

    Huɗubar Masallaci Mai Alfarma
    Sheikh Bandar Abdul-Aziz Balila 23/07/1446H

    HUƊUBA TA FARKO
    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, mafakar waɗanda ke cikin tsoro da ƙa-ƙa-ni-ka-yi, Mai ba da kariya ga masu neman mafaka. Ina yaba Masa, kuma ina gode Masa, tsarki ya tabba a gare Shi, Mai taimakon mabuƙata, Mai rarrashin waɗanda suka karaya, kuma Mai karbar tuban masu tuba.

    Ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, Ubangijin masu rauni, mai taimakon waɗanda aka zalunta, kuma Mai karɓar addu’ar waɗanda suke cikin tsanani. Kuma ina shaidawa lallai Shugabanmu kuma Annabinmu Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa, jagoran masu hasken fuska, Mai shiryar da dukkan halittu, tsira da aminci da albarkar Allah su tabbata a gare shi, da Alayensa tsarkaka nagartattu, da Sahabbansa masu ɗa’a da albarka, da Tabi’ai, da waɗanda suka bi bayansu da kyautatawa har zuwa ranar ƙiyama.

    Bayan haka:
    Ya ku mutane!
    Ina yi mana wasiyya da tsoron Allah, saboda haka, ku ji tsoron Allah, Allah Ya rahamce ku, ku yi riƙo da igiyarSa, kuma ku nemi mafaka a wajenSa, sai burukanku su cika, kuma ku ji daɗin haɗuwa da Shi, lallai duk wanda ya kira Shi kuma ya roƙe Shi, to, ba zai taɓe ba, kuma duk wanda ya ƙasƙantar da kansa gare Shi kuma ya yi fatan haɗuwa da shi, to, ba zai yi nadama ba, ta yaya hakan ba zai kasance ba, alhali Shi ne Mai cewa: (Shin wanene zai amsa wa wanda ya shiga cikin halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi yayin da ya kira Shi?).

    Sannan ku sani, Allah Ya yi muku rahama, cewa lallai duniya tana gudana ne bisa ƙaddarawarSa da hukuncinSa, kuma gudanar da al’amuran halittu tana kasancewa ne bisa nufinSa da yardarSa, kuma zukatan mutane suna tsakanin yatsun Ubangijimmu Mai rahama, yana jujjuya su yadda ya so a cikin ƙasa da sama, don haka, ku kyautata zato ga Ubangijinku, kuma ku yi fatan samun alheri daga Mahaliccinku, domin lallai wanda ya kyautata zato ga Allah, to, zai isar masa, kuma Zai jiɓinci lamuransa, kuma Ya ba shi abin da yake fata da buri.

    Allah Ya ce a cikin Hadisi Ƙudusi: “Ni ina daidai da zaton bawana gare Ni, kuma Ina tare da shi idan ya ambace Ni, idan ya ambace Ni a asirce, sai na ambace shi a asirce, idan kuma ya ambace Ni a cikin dandazon jama’a, sai In ambace shi a cikin dandazon da ya fi wancan alheri, idan kuma ya kusance Ni da ɗani ɗaya, sai In kusance shi da zira’i, idan kuma ya kusance Ni da zira’i, sai in kusance shi da gaba guda, idan kuma ya zo gare Ni yana tafiya, Zan zo masa da gaggawa. (Bukhari da Muslim suka rawaito)

    Ya ku bayin Allah!
    Kyautata zato ga Allah ibada ce daga cikin manyan ibadu, kuma aiki ne daga cikin mafi girman ayyukan neman kusanci ga Allah, wanda yake nuni a kan cikar imani, da kyawun zuciya, da yarda da abin da Allah Mai rahama Ya ƙaddara.

    An rawaito daga Abdullahi ɗan Mas’ud Allah Ya ƙara masa yarda, ya ce: “Ina rantsuwa da wanda babu abin bauta bisa cancanta koma bayansa, ba a ba wa wani bawa mumini wani abu da ya kai kyautata zato ga Allah Maɗaukakin Sarki alheri ba, ina kuma rantsuwa da wanda babu abin bauta bisa cancanta koma bayansa, bawa ba zai kyautata zato ga Allah Maɗaukakin Sarki ba, face sai Allah Ya ba shi abin da ya zata, hakan ya kasance ne saboda alheri a hannunSa yake”. Ibnu Abid-dunya ne ya rawaito.

    Kuma shi ne ƙudurce abin da ya dace da Allah Maɗaukakin Sarki na ma’anonin kyawu da buwaya, a sunayenSa da SiffofinSa, da maganganunSa da ayyukanSa masu daraja, tare da cikar iko a cikin abinda ya gabata da wanda zai zo nan gaba, da abin da yake ginuwa a kan haka na tasiri da ɗabi’u kyawawa.

    Shi Allah Maɗaukakin Sarki Shi ne Mai rahama, Mai jinƙai, Mai karamci, Mai yawan baiwa, Mai tausayi Mai yawan kyauta, Mai tausasawa, Mai yawan tagomashi, Mai tsananin ƙarfi Mai cikakken iko, Mabuwayi Mai girma, Mai amsa addu’ar masu tsananin buƙata, Ubangijin uwayengiji, Mai gudanar da gizagizai, Mahaliccin halittunSa daga turɓaya, rayayye da ba ya mutuwa, tsayayye da ba ya bacci.

    Shi ne Makusanci tare da ɗaukakarSa, Maɗaukaki tare da kusancinSa, Masanin abin da Ya rubuta kuma Ya gudanar da shi, halin halittunsa da ke ƙasa ko sama ba ya ɓuya a gare Shi, Mai hikima a ayyukanSa, Mai tausayin bayinSa, Mai taimakon wanda ya nemi kariyarSa da jiɓintarSa.

    Zuwa ga wanda jinya ta kwantar da shi kuma ta wahalar da shi, ta danƙwafar da shi a kan gadajen asibitoci, har suka zama su ne gidansa da makwancinsa, ga addu’ar Annabi Dawuda lokacin da jinya ta tsananta gare shi, lokacin da ta rinjaye shi ta ramar da shi, sai ya risina ga Allah Maɗaukakin Sarki ya kira Shi, yana mai bayyana buƙatarsa zuwa ga Ubangijinsa Majiɓincinsa:

    ((Kuma ka tuna) Ayyuba lokacin da ya roƙi Ubangijinsa (yana cewa): “Lallai cuta ta same ni, kuma Kai ne Mafi jinƙan masu jinƙai” () Sai Muka amsa masa (roƙonsa) sannan Muka yaye cutar da take tare da shi, Muka kuma ba shi (madadin) iyalansa (da ya rasa) da kuma kwatankwacinsu tare da su don jinƙai daga gare Mu da kuma wa’azi ga masu bauta (ga Allah)).

    Zuwa ga wanda aka haramta masa mai ɗebe kewa daga ƙawa ta rayuwa, wanda aka sanya masa kewa saboda kaɗaici, da shagaltuwar kowane ma’abocin iyali da duniyarsa, a ina ka bar addu’ar Annabi Zakariyya tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yayin da ya risina wa Majiɓincinsa Allah, ya roƙe Shi a boye, ya nemi agajinSa kuma ya yi fatan samun rahamarSa, da wata addu’a da duk wani ma’abocin rayuwa zai raurawa da ita, kuma idanuwa su kwaranyo da hawaye saboda ita:

    ((Ka tuna) kuma Zakariya’u lokacin da ya roƙi Ubangijinsa (cewa): “Ya Ubangijina, kada Ka bar ni ni kaɗai (ba magaji), Kai ne kuwa Fiyayyen magada”. () Sai Muka amsa masa Muka ba shi Yahya, Muka kuma gyara masa (mahaifar) matarsa. Lallai su sun kasance suna gaggawa wajen yin alheri, suna kuma roƙonmu suna masu kwaɗayin (rahamarmu) kuma masu tsoron (azabarmu), sun kuma zamanto masu ƙasƙantar da kai gare Mu).

    Haka kuma zuwa ga wanda bashi ya durƙusar da shi kuma ya gajiyar da shi, samunsa ya yi ƙaranci, matsalolin rayuwa suka yi masa dabaibayi suka taɗe ƙafafuwansa a hanyar neman abinci, ina ka bar karamcin Mai karamci! da arziƙin Mai yawan azurtawa da kyautar Mai yawan kyauta! Wanda Yake cewa a cikin Littafinsa: (kuma idan bayina sun tambaye ka game da Ni, To Ni kusa nake da su, ina amsa kiran mai kira idan ya kira Ni; to, su amsa Min nawa kiran, kuma su yi imani da Ni, don su shiryu) kuma Shi ne Mai cewa: (Sai na ce: “ku nemi gafarar Ubangijinku, lallai Shi Ya kasance Mai Yawan gafara ne() Zai saukar muku da ruwan sama mai yawa() kuma Ya daɗe ku da dukiyoyi da ƴaƴaye Ya kuma sanya muku gonaki Ya gudanar muku da ƙoramu).

    Zuwa ga wanda ya shiga cikin tsanani, abokan gaba suka haɗe masa, duniya ta yi masa ƙunci, ku ɗaga hannu, ku yi ƙanƙan da kanku, ku roƙi Allah kuna masu yaƙini da cewa Zai amsa muku, domin Allah Maɗaukakin Sarki yana ganin bigirenku, Ya san cututtukanku kuma Yana ganin hawayenku Yana jin kokenku, Shi ne kuma Mai ikon cin galaba a kan abokan gabarku, idan Allah Mai girma da ɗaukaka Ya yi nufin wani abu, sai Ya samar masa da sanadi.

    Don haka sai ku kyautata zato ga Ubangijinku, ku yi riƙo da LittafinSa da kuma Sunnar Annabinku tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, saboda a nan ne nasara da tabbatuwa suke, kuma dai da su ne ake samun kuɓuta ta gaskiya (Har yayin da Manzanni suka ɗebe ƙauna da imanin mutanensu, su kuma kafiran suka yi zaton an faɗa musu ƙarya ne game da zuwan azabar Allah, sai taimakonmu ya zo musu, sai Muka tserar da wanda Muka ga dama; ba kuwa za a kawar da azabarmu daga mutane masu laifi ba).

    Ya ku bayani Allah! Ahir ɗinku da ɗebe ƙauna da kuma fitar da rai daga rahamar Allah, domin su ne hanyar kafirci da ɓata, kamar yadda Ma’abocin girma da buyawa Ya ce: (Kada ku ɗebe ƙauna daga rahamar Allah, lallai ba mai ɗebe ƙauna daga rahamar Allah sai mutane kafirai).

    Kuma Ya ce: (Ba wanda zai ɗebe ƙauna daga rahamar Ubangijinsa sai ɓatattun mutane), domin lallai ɗebe ƙauna daga rahamar Allah yana daga cikin munana zato ga Allah, Allah Ya ce: (Kuma idan Muka yi wa mutum ni’ima sai ya bijire ya kuma juya kwuiɓinsa; idan kuwa sharri ne ya same shi sai ya zama mai yawan yanke ƙauna).

    Kuma ku kiyayi masu sa yanke ƙauna, masu kashe gwuiwa, masu sa cire rai daga rahamar Allah: Ka ce wa wanda ya cika zuciyarsa da munanan zace-zace, wanda yake ƙuntata mana duniya cewa: sirrin rabauta shi ne: Kyautata tsammaninka ga wanda ya halicci rayuwa ya kuma raba arziki.

    Imam ibnul Ƙayyim Allah ya yi masa rahama ya ce: Duk lokacin da bawa ya kasance mai kyautata tsammani ga Allah, mai kyautata fata gare Shi, mai dogoro na gaskiya da Shi, to, lallai Allah ba Zai tozartar da fatansa ba har abada, domin Shi Allah Tsarki ya tabbata a gare Shi baya tozarta fatan mai fata, Baya kuma lalata aikin mai aiki.

    Ina faɗin wannan magana tawa, kuma ina neman gafarar Allah gare mu da sauran Musulmi daga kowane laifi, saboda haka ku nemi gafararSa, lalle Shi ne Mai yawan gafara Mai yawan jinƙai.

    HUDUBA TA BIYU

    Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, kamar yadda ya dace da cikarSa da wadatarSa, kuma ina gode Masa godiya da za ta yi daidai da kyautarSa da baiwarSa. Kuma ina shaidawa lallai babu abin bauta bisa cancanta sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya a ƙasa da sama, kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad BawanSa ne kuma MazonSa, ya kai maƙura cikin kamala ta bil’adama, tsira da amici da albarkar Allah su tabbata a gare shi, da Alayensa, da Sahabbansa, da waɗanda suka bi tafarkinsu da hanyarsu.

    Sa’annan, ku sani, ya ku bayin Allah! Lallai a cikin wuraren da kyautata wa Allah zato yake ƙarfafa, kuma ake rinjayar da fatanSa akan tsoronSa da fargabarSa, idan mutuwa ta zo wa bawa, ya yi dab da rabuwa da duniya, saboda lallai shi Mumini duk yadda ya kai da sakaci, duk yadda ya kusanci saɓo da munanan ayyuka, manya da ƙanana, ya sani cewa lallai Allah Mai ji ne Mai gani ga bayinSa, kuma Mai cikakkiyar masaniya ne game da rauninsu, Kuma Shi Mai tausayin su ne da suturta su.

    An karɓo daga Jabir bin Abdullahi Al’ansari Allah Ya ƙara musu yarda, ya ce: “Na ji Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi kafin ya rasu da kwana uku yana cewa: (Kada ɗayanku ya kuskura mutuwa ta riske shi face yana kyautata wa Allah Maɗaukakin Sarki zato). Muslim ne ya ruwaito shi.

    Malamai Allah Ya yi musu rahama sun ce: “Wannan jan kunne ne game da yanke tsammani, da kuma kwaɗaitarwa a kan kyakkyawan fata a yayin cikawa, wato shi ne ya sa rai cewa lallai Allah Zai ji tausayin sa, kuma Ya yafe masa”. Sannan ku yi yi salati da sallama ga mafi alherin halittun Allah, Muhammad bin Abdillah, domin haƙiƙa Ubangijinku Ya umurce ku da haka, Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce: (Lallai Allah da Mala’ikunsa suna salati ga Annabi, Ya ku waɗanda kuka yi imani ku yi salati a gare shi da sallama mai yawa).
    Ya Allah Ka yi daɗin tsira da aminci da albarka ga BawanKa kuma ManzonKa Annabinmu Muhammadu.

    Ya Allah Ka ƙara yarda da Halifofi guda huɗu, Jagorori nagartattu, Abubakar da Umar da Usman da Ali, da sauran Sahabbai goma da aka yi wa bushara da Aljanna, da waɗanda suka yi mubaya’a ƙarƙashin bishiya, da sauran Sahabbai baki ɗaya, da Tabi’ai, da waɗanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

    Ya Allah Ka ɗaukaka Musulunci da Musulmi, Ka kiyaye shingen Addini, Ka taimaki bayinKa masu Tauhudi, Ya Mai tsananin ƙarfi. Ya Allah, Ka kawar da damuwar masu damuwa daga cikin Musulmi, Ka yaye ƙunci ga waɗanda ke cikin tsanani, Ka biya bashin masu bashi, Ka warkar da marasa lafiya daga cikin Musulmi.

    Ya Allah, Ka ba mu tsaro a ƙasashenmu, Ka gyara shugabanninmu da majiɓinta al’amuranmu, Ka ƙarfafi shugabanmu, majiɓincin al’amuranmu, Hadimin Masallatai biyu masu alfarma, Ya Allah! Ka tsawaita rayuwarsa cikin lafiya da kwanciyar hankali, da ni’ima mai yawa.

    Ya Allah, Ka datar da shi tare da Yarimansa amintacce, akan dukkan abin da zai kawo gyara ga ƙasa da al’umma, da kuma ɗaukaka ga Musulunci da Musulmai, Ya Ubangijin talikai.
    Ya Allah, Ka zama mai ƙarfafa da ba da nasara da taimako ga ‘yan’uwanmu masu Rauni.
    Ya Allah, Ka taimake su a Falasɗinu da duk inda suke, Ya Ubangijin talikai. Ya Allah, Ka kare sojojinmu masu tsaron iyakoki da fagagemmu.

    Ya Allah, Ka kiyaye su da idanunka waɗanda ba sa barci, Ka ƙarfafe su da ƙarfi daga gareKa wanda ba ya gushewa, Ya Ubangijin talikai. Ya Allah, Ka sanya mu cikin waɗanda za a tsawaita rayuwarsu, kuma ayyukansu su yi kyau, cikin lafiya da Imani da alheri da kyautatawa. Ya Allah, Ka sanya mafi kyawun ayyukanmu su kasance na ƙarshe, mafi alherin lokutan rayuwarmu su kasance ƙarshensu, kuma mafi kyawun ranakummu ranar da za mu haɗu da Kai, kuma Ka karɓi rayukanmu alhalin Kana yarda da mu, ba Ka fushi da mu, Ya Ubangijin talikai.

    Ya Allah, Ka sanya zukatanmu su ratayu da yardarKa, Ka raya su da tsoronKa da kiyaye dokokinKa, Ka sanya mu cikin masu kyautata zato gare Ka a duniya da Ranar haɗuwa da kai, Ya Mafi tausayin masu tausayi. Ya Ubangijinmu, Ka ba mu kyakkyawa a duniya, kuma Ka bamu kyakkyawa a lahira, Ka tsare mu daga azabar wuta. Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin buwaya daga abin da suke siffantawa, aminci ya tabbata ga Manzanni, godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai.

    Don karanta Tsarabar Makon Sabbai 2025 danna nan

    Edita; Rumasa’u M. Kallamu