Sun dai kai mu sun bari sun dawo
Kuma ni sai nake ga mu muka jawo
Wani sunansa Baba wani Babawo.
Alƙawari sukai na za su yi aiki
Har ma rantsuwar mutanen kirki
Yau mun wayi kanmu ba imfaƙi.
Babu tsaro ƙasarmu komin haske
To in kai dare kwa sai dai waske
Sai a siye ka tsaf kamar ɗanwake.
Yau mun wayi kanmu ba jin daɗi
Wai kuma gwamnati akai tajdidi
Ko mu sai a lahira jin daɗi?
Wancan shi ya fara kai mu kushewa
Muka jure mukai ta daddagewa
Har ya gama ya bai wa ɗan yarabawa.
Al’umma tana cikin lahaula
Babu abinci kana babu sulalla
Ba nutsuwa gare mu bayin Allah.
Magidanci babu ba mai ba shi
Ba mai ba shi sadaka ko bashi
Kai wallahi dole sai an tashi!
Yau talakan ƙasarmu ba shi da hali
Na siyan taliya catorn ko kwali
Ko shinkafa-kaza ba shi da hali.
Yau in ya siya ana daɗa kuɗɗi
Gobe siyanta sai su Alhaji Mudi
Jibi kwa sai irin gidan ɗanmoɗi.
Mun ji kuna da bindigar hana bore
Kuma ku ne da kurkuku mai ƙyaure
Naman ‘ƴan maza fa shi ne gyare.
Ku ba kwa sanin muna ƙunci ne?
Ba ku ganin abin yana yin worse ne?
Anya ku kwa ma mutane ku ne?
Ku yi sata amma ku bar mu mu rayu
Amma kun ci kun hana mu mu rayu
Ko so duk kuke mu zamma marayu?
Yanzu a ce abinci ya wuce kanmu
Ba mu babu cin abin ƙaunarmu
To wa za ya share duk kukanmu?
Ba doka ƙasarmu sai kurari
Sai cewa anai kamar mai bori
Mu fa aradu sai mu ɗau gorori.
Abban Marke
Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu
