Tag: egg

  • Yadda Ake Bread-egg Toast A Sauƙake

    Yadda Ake Bread-egg Toast A Sauƙake

    Barkan mu da  kasancewa  a fannin girke-girkenmu na WikiHausa, za mu  koyi yadda ake bread-egg toast. Tare da ni Hafsat Shettimah.

    Abubuwan haɗawa:
    • Bread (na alkama)
    • Ƙwai
    • Gishiri
    • Pepper (yaji)
    • Mai
    Yadda ake haɗawa:
    1. Da farko Uwar gida za ki fasa ƙwanki, sai ki sa ɗan gishiri da yaji, sai ki kaɗa.
    2. Ki tsoma bread ɗin a cikin ƙwai, sannan ki ɗora pan ɗinki mara zurfi, sai ki shafa mai da tissue paper ba a so mai ya yi yawa. Idan ya yi, sai ki juya ɗayan gefen, haka za ki ta yi har ki gama.
    3. A sha da lemo ko shayi ko kuma a saka a lunch box ɗin yara na makaranta.

    Domin koyan Yadda Ake Rainbow Cake Doughnut Sabon Salo  danna koren rubutu nan