Tag: Dale

  • Yadda ake haɗa Dale

    Yadda ake haɗa Dale

    KAYAN HAƊI 

    • Karfatar rago 
    • Ruwan Kal (vineger) 
    • Habbatus sauda 
    • Kayan ƙamshi 
    • Tafarnuwa 
    • Sinadarin ɗanɗano 
    • Albasa 
    • Tumatir 

    Yadda Za A Haɗ

    A sami karfatar rago da ƙashinta a jikinta, a riƙa tsattsaga ta, sai a shasshafa mata vineger ko lemon tsami a daka habbatus sauda kaɗan da masoro da garlic da maggi da mai a cakuɗa, a shafe naman dashi. 

    Sai a ɗora a kan a farantin gashi da ruwa kaɗan, idan ya fara dahuwa sai a yanka albasa amma slicing ɗinta za a yi, sai a ɗora a kan naman, sai a yanka tumatir shima irin yadda kika yi ma albasar, sai a mayar cikin oven ya ɗan ƙara gasuwa. Idan ya dahu a kashe a fito da shi.

    Domin karanta cikekken littafin Girke Girke  Danna nan