Tag: Cinikin Bayi

  • Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Biyar

    Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Biyar

    Cinikin Bayi a Afrika ya ɗauki salo daban-daban kamar yadda na yi bayani a baya babu abin da ya kassara Afrika kamar wannan, ta hanyoyi daban-daban har da canja wa mutane da kuma canja yanayin zamantakewa. To kowanne sashe na Afrika akwai irin nau’in bautar da ake yi ta inda mutane tsakaninsu ma ko kuma su da maƙotansu wasu su je su sato wasu.

    Duk wannan abu yana faruwa, kafin masu waɗannan su zo su waɗannan mutanen Portugal, da bayan ma sun zo waɗanda su suka kawo cinikayyar Bayi gadan-gadan da kuma su mutanen Ingila Dens da Dutch su ma suka zo suka shiga cikin wannan ciniki.

    A ɓangaren abinda ya kama daga Senegal har zuwa Port Sudan da kuma Yammacin Tsakiyar Sudan (Western Central Sudan) wanda yawancin su duk musulmai ne nan ma an yi cinikin Bayi kuma an bautar da mutane, an yi yaƙe -yaƙe a tsakanin juna, an sayar da mutane, kafin ma zuwan Turawan Portugal da bayan zuwan su.

    Saboda su waɗannan da suke wannan sashe na Afrika yawanci idan sun kama Bayin suna amfani da su a tsakanin su wasu kuma su kai su su sayar a tafi da su ta Sahara. Tunda akwai ƙasashe manya a wannan nahiya, kama tun daga kan Ghana, Mali, Songhai da Borno idan aka zo Sokoto ƙasashe ne masu ƙarfi kuma suna da dawakai suna amfani da su akan maƙwabtan su, wannan abu ya ɗauki salo iri-iri da hanyoyi daban-daban, kuma bayan zuwan su da kuma kafin jihadi da kuma bayan jihadin Shehu Ɗan Fodio.

    Tunda a cikin tarihi ma wasu daga cikin malamai sun ce ɗaya daga dalilin da yasa su Shehu Ɗan Fodio suka yi jihadi saboda ana ɗiban musulmi ana sayar da su Bayi, wannan abu ya tayarwa da malamai da sauran mutane hankali, kuma da aka yi Daular Sokoto an yi ƙoƙari a hana wannan, waɗanda kawai suka yarda a dinga siyarwa su ne waɗanda ba musulmai ba.

    Sun mayar da mutanen da suke ƙananan ƙabilu da suke a tsakiya su aka rinƙa farauta a na sayar da su, wannan abin ya jawo musu baƙin jini a wajen sauran mutane bayan zuwan Mishan, wanda Mishan sun yi amfani da wannan don su ƙarfafi ko su dasa ƙiyayya tsakanin musulmin Arewa da waɗanda ba musulmi ba, cewa dama can iyayen su, idan mutum ya karanta littattafan su zai ga duk irin waɗannan abubuwa da irin abin da suka nuna sai suka mayar da abin cewa, gaba ɗaya a wannan nahiya ba abin da aka yi sai dai kashe su da mayar da su Bayi.

    Wannan abu ya shiga zukatan waɗanda ba musulmi ba, wanda daga baya suka zo suka karɓi addinin kirista. Mun san irin waɗannan cewar wancan zamanin da yanzu ba ɗaya ba ne, to amma wannan abin ya yi tasiri gare su da mutanen su ya kuma cunkusa ƙiyayya daban-daban.

    A irin wannan yanayi na yadda ake kama Bayi a wannan nahiya ta Sudan, an yi rubuce rubuce daban-daban musamman Turawan da suka zo a da can kafin su yi mulkin mallaka, har da wanda ya ba da labarin irin abubuwan da suka faru a Borno, tunda babbar  ƙasa ce kuma suna da ƙarfi a lokacin da suke kai hari wurin irin waɗannan ƙananan ƙabilu, kuma in ba su bayar da kai ba za a ɗebo su da matan su da yaran su, manya-manyan mazan duk a karkashe su. Yara da mata a ɗebo su a sayar da su, waɗanda suke sha’awarsu su mayar da su ƙwarƙwarori ko su bayar da su duk wannann ya faru.

    Daga cikin irin waɗannan mutanen da suka ga abin da ya faru akwai Harith Barth, ya faɗi abin da ya gani da Borno ta kai hari Mandara wurin mil 300 daga ƙasar Borno (Kukawa) da irin abubuwan da suka faru aka dinga ɗebo mutanen. Duk wannan sun rubuta su kuma sun bayar da bayanai a kansu a irin wannan yanayi, mun ga shi ma kansa Luggard da sauran su abin da suke ta cewa su Turawan Ingila cewa su sun zo ne don su kawar da cinikin Bayi.

    Bayan an yi jihadin Shehu Ɗan Fodio an ci nasara waɗanda aka kama aka mayar da su Bayi, wasu a faɗace-faɗace inda wasu har ma an sayar da su an tafi da su wata ƙasa kamar irin su Nicolas wanda aka sayar da shi har ya kai Rasha, wanda Sir Nicolas ya yi Baptising ɗin sa daga nan ya tafi Spain bayan ya ‘yantar da shi, inda daga nan ya tafi America aka yi yaƙi da shi.

    Duk irin wannan ya sa a zagi Shehu Dan Fodio da cewa jihadi ne da irin wannan bautar ta sa aka kama shi ya tafi, duk mun san irin wannan idan ma ƙasashen an samu waɗanda suke son Shehun kuma suka yi amfani da wannan abin da aka yi na jihadi su ma suka tayar da rigima kamar Ab-bahiya a ƙasar Brazil. Wannan duk ya nuna mana irin yadda wannan ƙasa ta Afrika take da yanayin zamantakewa na rigingimu da faɗace-faɗace da abubuwan da suka jawo.

    A wannan nahiyar ƙasashen musulmi kenan wanda yawancin Bayin su suna sayar da su ne a Sahara wasu suna shiga Europe ɗin wasu suna shiga nan iyakar Magrib da Misra, yawancin irin waɗannan Bayin nan ake kai su, mun san cewa a irin bauta ta ƙasashen musulmi daban take da ta sauran ƙasashe tun da akwai ƙa’idoji na shari’a waɗanda aka gindaya ba za ka iya yi wa Bawanka ba da sauran su, kuma a can ƙasashen musulmi su na da tsarin cewa, mutum zai iya nemo ‘yancin sa.

    Duk da dai a nan nahiyar Sudan abin bai fiye tabbata ba, kuma da su kan su Bayi a nan waɗanda aka haife su a cikin bauta ba a sayar da su saboda sun musulunta sun zama Bayi na gida, wanda a hankali suna shiga gida har ma ya zama su mata a mayar da su ƙwarƙwarori, ko wasu da suke fara mulki suna samun ‘yanci su ma su zama wasu abu kamar yadda muke ganin Bayi a Fada. Wannan yana daga cikin abubuwan da suke faruwa a irin bautar ƙasashen musulmi da kuma nan ƙasar Sudan daban suke da sauran wurare.

    Ana ɗiban su su ma ana kai su can ƙasashen Larabawa, wasu su mutu a hanya, wasu kuma su tsira da wahala dai iri-iri. A irin ƙasashensu su ma ana samun bauta da kuma yaƙe-yaƙe a wurare irin su Upper Volta ɗin nan wanda aka ce ita ce ta zama Burkina Faso, wanda waɗannan ƙasashen ma yawanci ba ɓarin musulmi ba ne, har ma aka ga cewa a ƙididdigar da aka yi kashi 17 bisa ɗari na ƙasar gaba ɗaya an bautar da su, kafin Turawa su zo lokacin da aka hana waɗannan abubuwan.

    Kowacce nahiya da irin nata, saboda idan ka tafi can ɓangaren su Ethopia nan ma da take babbar ƙasa ce ta kirista su ma sun bautar da mutane wasu an kama su wasu kuma an sayar da su wasu an mayar da su Bayi. Akwai ƙasashen da suke na musulmi su ma suna ɗiban Bayi. Kiristocin Ethopia bayan da suke ɗiba ma suna bautar da su wasu, sun kashe wasu kuma su sayar da su tunda su ba tsarin su ɗaya da musulmi ba.

    Su ma musulmin da suke wannan nahiya ta Gabashin Afrika, Bayi ana tafiya da su can Gulf da kuma sauran ƙasashen Asia ma duk ana ɗiban ‘yan Afrika. Waɗannan abubuwa ne da suke dama kafin zuwan Portugees ɗin su fara wannan cinikayya tasu kuma har su canja yanayin yadda ma bautar da ɗiban zai kasance a wannan nahiya ta Afrika.

    Kamar yadda na faɗa su ma ƙasashen kurmi yadda suke ɗiban nasu Bayin ya sha bamban da irin namu na Savannah, saboda su ƙasashen kurmin nan yawancin su ba su da dauloli masu ƙarfi in banda irin su Benin da Oyo da France. Waɗannan manyan dauloli kuma da sauran waɗanda suke kusa da su da ‘yan Uyo su idan sun ɗiba sayar wa da Turawa suke, kuma a irin wannan wurare irin su Oyo Bayin ana yayyanka su a ba wa ababen bautar su, tunda duk sun yarda da sadaukarwa saɓanin irin  ƙasashen musulmi ko na kirista na gabashin Afrika inda ba a yanka mutum a sadaukar da shi da irin shirka da suka saba.

    Wannan yana daga cikin abubuwan da suka sha bamban da bautar musulmi da waɗanda ba musulmi ba, ta inda su musulmi idan sun ɗiba Sahara suke kaiwa su kuma waɗannan suna ɗiba ne su kai Atlantic. Duk wannan kafin zuwan Turawan Potugal waɗanda lokacin da suka zo kurmi suka yi da kuma inda yake suna da ruwa suka dinga ɗiba su da ƙabilun da suke a waɗannan wurare da mutane masu ƙarfi, amma duk kusan abin da ya faru shi ne, su waɗannan ƙasashe da na Arewacin Sudan da na Kudu na can bakin teku suna shigowa tsakiya ne suna ɗiban ƙananan ƙabilu su suke sayarwa.

    Saboda haka suka ragargaji wurin da ake cewa Middle Belt ba ma kaɗai a Nijeriya ba, inda ita kanta Middle Belt ɗin an canja mata suna kuma mun san cewa ita Nijeriya ita ta fi kowacce ƙasa yawa da yadda su waɗannan mutanen aka dinga ɗiba, waɗanda suke a bakin teku cikin ƙasa suka dinga shigowa shi yasa za ka ga yawanci su ƙabilar Igbo su aka fi yi wa wannan farmaki tunda su ne suke kusa da Ijo kuma ba su da ƙarfi ba su da tsarin gwamnati irin na waɗannan ƙasashe.

    Yawancin waɗanda aka fi kai wa farmaki ana ce musu Stateless ko kuma non-State, waɗanda ba su da tsarin hukuma irin na waɗannan ƙasashe su aka dinga ɗiba ana sayarwa a ko ina a Afrika, su suka shiga wannan tsari na ɗiban Bayi da rashin albarka na cutar da su tun ma dai kafin su Turawan Portugal ɗin su zo, tunda dama mutane suna faɗa a tsakanin su, wannan ya ɗebi wannan wancan ya ɗebi wannan, zuwan Turawa sai ya zama ya canja wannan abin gaba ɗaya yanda za mu gani su kuma wane irin tasiri abin su ya yi wa al’ummar Afrika.

    Danna nan don karanta cinkin bayi a tarihin Afrika kashi na huɗu

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Huɗu

    Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Huɗu

    Great Britain, Ingila ke nan duk da yake ita ta zama ta fi kowacce cin ribar cinikin Bayi, ba ta soke bauta ba da wuri, sai bayan an ɗauki lokaci, inda sauran ƙasashen Turai suka ce sun haramta cinikin Bayi. 

    Ƙasar da ta fara yin doka ita ce, Denmark a shekara ta 1804, Ingila ta yi a shekara ta 1807, sai Amerika ta yi a shekara ta 1808, sai Sweden a shekara ta 1817, sai Holand a shekara  ta 1814, an ba da dalilin da yasa su Turawa ba su damu da cinikin Bayi ba da azabar bautar da mutane da ake yi saboda su ma a ƙasar su ana azabtar da mutane da suka yi ɗan laifi kaɗan, sai ka ga mutum ana bin sa kuma a ƙarshe an zo an kashe shi, ko an tsire shi, ko an ɗauke shi an jefar da shi a wata ƙasa.

    Duk wannan zaluncin su ma ya dame su sai ya zamanto ma ba sa ganin zaluntar da ake yi wa Bayin, sai da abubuwa suka fara kankama tukunna, aka fara sanin cewa lallai fa Bayi suna shan wuya, wani lauya ana ce masa Grandba Shap  ne ya fara ƙoqarin maganar ‘yantar da Bayi, ya taimakawa wani Bawa da ya gudu ana ce masa Somaset.

    Wannan Bawan ya gudu aka je aka kamo shi za a dawo da shi, sa ya shigar da ƙara a gaban alƙali wato Lord…. inda aka yi wani abu da ake ce masa Read of Habees copus cewa lallai a kawo shi wannan bawa kotu, kawo shi kotu da hukuncin da shi Lord Chief Mans… ya bayar ne ya fara jawo mutane su san cewa lallai akwai azaba a harkar cinikin Bayi. Kuma abin ya samu karɓuwa, cewa a san yadda za a yi a hana wannan.

    Bayan shekara goma sha biyar ana ta wannan gwagwarmaya da mutane irin su Williams Wilberforce da wannan Grandba Shap da Thomas Clascis suka yi wata ƙungiya suka kira ta da Society for the Revolution of  Slave Trade, kuma shi Willberforce ya zama shi ne mai magana da yawun su a majalisa, har yasa dai aka yi wannann doka ta shekarar 1907.

    Amma dai sun ci gaba da yin gwagwarmaya da sauran mutane da yin wannan, inda daga baya Ingila ta ce lallai za ta hana wannan cinikin, amma dai ba wai sun hana ne don tausayi kaɗai ba,  akwai maganar tattalin arziki da maganar sun samu ci gaban masana’antu (Industrial revolution). Bayin dai buƙatar su ta ragu a ɓangaren tattalin arziki a Ingila, tunda Ingila ta ci gaba kuma suna ganin cewa, gwanda mutane a ƙyale su a Afrika su dinga yin noma don a samu wanda ake yin amfani da shi a masana’antu (Factories).

    Ingila da sojojin ta na Ruwa suka ɗauki gabaran hana wannan ciniki tunda ta fi kowa ƙarfi a ruwa, su za su yi maganin cinikin Bayin nan. Duk da haka dai abin ya ba su wahala yadda mutane suke ta ƙoƙarin su kauce mu su, sun fito da dabaru da yawa na kaucewa inda za a kama su, duk da dai an kama jirage da yawa.

    A cikin shekara 20 daga 1818-1838 an kama jirage 280 da wani abu, haka dai kullum jiragen da ake kamawa ƙaruwa suke inda a shekarar 1845 ma an kama jirage 30, amma duk da haka sun ci gaba da yin dabaru su masu ɗiban Bayin nan domin su kaucewa sojojin ruwa na Ingila, domin duk jirgin da suka kama saisu kai shi Freetown Sierra Leon a nan a ke yi masa hukunci.

    Wani lokacin ma su masu cinikin Bayin sai su ɓoye su ko su zubar da su a ruwa domin kada a kama su, sai da aka canja dokar aka ce idan an ga wasu abubuwa da suka yi kama da kayan cinikin Bayi a kama jirgin shi ma a yi masa shari’a. 

    Wasu idan an kama su an kai su Sierra Leon ɗin nan to sai a saki Bayin tun da wannan gari ana ce masa Freetown, wasu idan an sake su Mishan suna ɗaukan su su koya mu su karatu su mayar da su Kirista da sauransu. Har ma aka samu wani babban Kirista da aka taɓa yi a Najeriya ana ace masa Bishop Samuel Ajayi Crowther wanda shi ma aka sace shi aka mayar da shi Bawa a shekarar 1821. 

    Haka aka ɗauke su daga wannan hannu zuwa wannan tun da yana da rabon zai tsira aka kai shi Sierra Leon daga nan kuma dai ya samu ya kuɓuta tunda an kama jirgin da yake ɗauke su, aka mayar da shi Kirista a shekarar 1825 aka yi baptizing ɗinsa ya zama Samuel Crowther, wanda yasa aka sa masa wannan su na shi ne shugaban Cochi a nan Sierra Leon.

     Kowa ya san gwagwarmayar da ya yi wajen kawo addinin Kirista Najeriya, shi ne ɗan Afrika na farko ɗan asalin Najeriya da ya zama Bishop na Angalican kuma ya shahara, yana ɗaya daga cikin mutanen da aka kuɓutar da su daga hannun masu cinikin Bayi.

    Haka dai suka yi da aka gama cinikin Bayin nan sai ya zama cewa, Mishan sun duƙufa sosai wurin yaɗa addinin kirista, saboda su wanke laifukan su da suka yi wa mutanen Afrika su kawo mu su addinin kirista. Wannan abu ya yi tasiri da yadda su Turawan mulkin mallaka suka yi amfani da Mishan don su tabbatar da mulkin su a Afrika ta yin amfani da Mishan da cinikayya da dabaru da sauran su har suka zo suka tabbata, tun da an gama cinikin Bayi an shiga wata marhala ta danniya daban (mulkin mallaka).

    Don karanta tarihin Afrika danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Uku

    Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Uku

    Yawancin cinikin Bayin da aka yi a wannan ƙarni na 16 ana ɗiban su ne ana kai su Satomi inda suke noman rake da sigari  tobacco taba kenan, sai kuma waɗanda ake kai su Elmina  ƙasar Ghana inda suke haƙo gwal, a wannan lokacin dai Bayin da aka dinga ɗiba wannan abin suka dinga yi abin bai kankama ba sosai, kuma a sauran shekaru da suka biyo baya.

    Abin ya yi tsamari dalili kuwa shi ne, na farko su Spain da Portugal sun kafa sansanin su wato Colonies ɗin su a Brazil da kuma wasu ƙasashe na ƙasar Amerika, wannan ya sa sun fara neman mutane da yawa don su je su yi wannan aikin noma saboda su mutanen ƙasar Brazil ba su da ƙarfi kamar mutanen Afrika a ɗauke su su yi aikin wahala, saboda haka  wannan ya sa cinikin ya bunƙasa ana ta ɗiban mutanen Afrika ta Yamma ana kai su. 

    Dalili na biyu kuma shi ne, su waɗannan Turawa masu cinikin bayi sun ta kawo kayayyakin su suna sayarwa da sarakuna na wannan ƙasashe, su kuma waɗannan sarakunan wannan dukiya da suka samu ta ƙara musu ƙarfi da kuma bindigogi da suka dinga sayar musu musamman da sarkin Dahome da Oba na Lagos da Oba na Benin da kuma Sarakunan Ifik na can kusa da Calabar.

    Suna ba wa mutane suna shiga suna ɗebo musu bayi  daga  sauran ƙasashe, wannan kayan yaƙi da Turawa suka kawo ya sake ragargaza mutanen Afrika, saboda ƙarfin da suka ba wa waɗannan sarakuna su kuma suna yin amfani da shi su na ɗebo mutane, inda har ta kai aka ɗebi mutum miliyan ashirin (20 million)  a wannan lokaci. 

    Waɗannan shekaru ƙarni na 17 da 18 da na 19 fiye da ƙarni na 16 inda  kawai mutum miliyan ɗaya ne (1million) aka ɗiba. Kuma su Turawan Ingila ba su shiga ba, to shigar Turawan Ingila ma shi kenan magana ta canja, saboda a wannan lokaci sun samu Amerika sun fara ɗiban mutane suna kai su Amerika suna yi mu su noma.

    Sai Ingila ta zo ta wuce ma Spain da Portugal a harkar sayen bayi, saboda ita ta samu Amerika kuma wannan ya taimaka ya ƙara ƙarfin Ingila, saboda cinikin bayi shi ne tabbatar Ingila da suka yi amfani da shi suka samu ƙarfi a Amerika suka samu dukiya har suka zo suka caccanja abubuwan suka samu sauyin arzikin masana’antu (Industrial Revolution).

    Kuma an ce daga Liverpool ma kawai bayin da aka ɗauka a shekara goma 1783-1793 sun kai dubu ɗari uku aka ɗiba daga gaɓarta. Dalilin cinikin bayi ma har ta zama cewa ta samu ɗaukaka a duniya, kuma su kansu Turawan nan su suka yi rubutu suka dinga ba da labarin yadda ake yin cinikayyar Bayin nan da yadda ake yi wa mutane azaba da sauran su.

    Har ma akwai wani Kaftin John Adams shi ma ya rubuta littafin sa mai suna Scaches taken 10…. Of Africa between 1786 and 1800, ya yi maganar irin abubuwan da ya gani a Lagos da cewa mutane an yi faɗa ko ana yaƙi, an ɗebo Bayi waɗanda suka yi faɗa an sossoke kawunan su a kan bishiya ga shi nan kana ganin kawunan mutane, kuma ga wasu irin ɓera su ma saboda mushen mutane da suke ci sun bunƙasa sun yi yawa.

    Ya ce wani lokacin ma idan Turawa sun zauna in dai ba ka ɗaga kaya ba za ka dinga ganin ɓerayen su na shigowa ta ƙarƙashin su. Akwai wani shi ma William Bossman shi ma ya rubuta littafi mai su na New and accurate description of the coast of Guinea aka buga shi a Landon a shekarar 1805.

    Inda yake faɗar yadda ake yi wa Bayin nan cewa a ƙirjin su ake yi musu lamba, kuma mata ba su fi kwata ko kashi ashirin tsadar namji ba yadda ake sayar da su, idan kuma aka shiga da su ruwan ma duk kwashe musu kayan su ake yi a tafi da su tsirara, kuma jirgin ya kan ɗauki mutum 600 zuwa 700. 

    Micheal Crowder ya yi lissafin irin mutanen da aka ɗiba daga nan Yammacin Afrika (West Afrika) da Angola ya ce, a ƙarni na 16 an ɗebi mutum miliyan 1, a ƙarni na 17 an ɗebi mutum miliyan 3, a ƙarni na 18 an ɗebi mutum miliyan 7. To yana maganar cewa a duk shekara a kan ɗauki mutum dubu ashirin da biyu daga ƙasar Najeriya, duk da yake cewa a ƙarni na 19 ma an hana cinikin Bayin, amma an ɗebi a ƙalla mutum miliyan 4. 

    A cikin irin bayanin da wani mai suna Rossel Warren Horray ya rubuta,  ya ba da labarin yadda ake cinikin Bayi da yadda cewa mutum ɗaya daga cikin mutum bakwai ko wane zai iya zama Bawa a cikin ‘yan Afrika saboda bala’i, kuma namiji ɗaya daga cikin ko wanne maza biyar zai iya zama, mace ɗaya daga cikin kowacce goma za ta iya zama Baiwa, saboda wannan masifar da aka yi ta cinikin Bayin nan.

    To cinikin Bayi ya kawo wa mutane rashin kwanciyar hankali da zaman lafiya, mutane ko yaushe su na cikin tashin hankali na cewa za a iya zuwa a kame ka a tafi da kai, wannan abu ya daɗe ya shiga ƙwaƙwalwar mutane an ragargaje su, gaba ɗaya aka rusa tunanin al’umma saboda harkar Bayin nan.

    Wani abu da ya faru a shekara ta 1835 inda wasu daga cikin Bayin da aka kai su Brazil suka yi tawaye, saboda sun samu wasu daga cikin su sun kasance mutanen da suka san Shehu Ɗanfodiyo ne da kuma Jihadin da ya yi, saboda haka wannan ya ba su ƙwarin gwiwa suka yi tawaye.

    Don haka mutanen Brazil suka koro su suka dawo da su Lagos, wasu daga cikin su musulmi suka zo suka kafa sansanin su na musulmi, wasu ma da ba musulmin ba suka biyo su da suka ga abin da musulmi suka yi. Wannan ya kawo canji a Lagos da samun abubuwa na ci gaba inda har suka yi Unguwar ‘yan Brazil (Brazillian quarters) a Lagos, har yanzu za ka ga cewa wasu daga cikin mutanen Lagos ɗin za ka ji sunayen su irin su Codoso, Perrara su Sanchez duk wannan sun same su ne a dangantaka da irin mutanen Brazil da suka zauna a can. 

    Haka kuma suka zo Lagos suka samu ɗaukaka suka shiga harkokin rayuwa da kasuwanci da harkokin ilimi har suka yi babban masallaci a Lagos, duk wannan su na daga cikin ɓurɓushin waɗanda suka taho daga Brazil da kuma samun wani abu na ci gaba a wannan lokaci. 

    Don karanta tarihin Afrika danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Biyu

    Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Biyu

    Yahudawan da wannan Sarkin King Jour II ya kawo a shekarar 1485 su ne suka zauna a wannan wuri na Afrika, a shekarar 1506  guda 600 suka rayu a nan.  Waɗannan Yahudawa yara ne ya tilasta musu suka zama Kirista ya sa aka dinga ɗebo masu mata daga Benin domin su hayayyafa, a ƙarshen ƙarni ma 15 (century).

    Waɗannan mutanen Poturgal suna da cikakken bayanin yadda ƙasar Benin take, irin su Pokados a Kudancin Najeriya, sun yi zane sun rubuta duk abubuwan da yadda za a iya shiga wannan ƙasar, wani wai shi Perar shi ya yi wannan rubutun ya gaya wa mutanen su irin yadda ƙasar take da inda za su shiga, har ma ƙasashen Yarabawa irin su Ijebu da yadda za su shiga. Ya zana mu su hanyoyin da za su bi su je, da wurare da za su kiyaye inda suke da haɗari ka da su yi nisa daga bakin wannan ƙasar da suke. 

    To labarin dai da aka fara samu na jirgin ruwan da ya fara ɗiban Bayi shi ne a shekarar 1522, kuma abin da shi wannan Sarkin Portugal ya tsara shi ne, bai yadda cewa ba wai daga can yake ɗebo mutane ba, saboda waɗannan yaran da ya fara kawo su suka hayayyafa, su ya fara ba wa kwangila cewa su ɗebo musu mutane daga nan ƙasashe da tsari, idan suka yi cinikin su suka kai su waɗannan ƙasashe shi ba ruwan sa duk shekara sai su biya shi su biya masu treasury na ƙasar Portugal. 

    To irin wannan aiki ya dinga yi har aka samu bayani (record) cewa ga shi a shekarar 2 ga watan Mayun 1522 jirgi ya taso daga Satomi  ya iso Pokados 1 ga Afrilun 1522, da irin wannan bayani (record) aka samu cewa ga irin halin da mutanen Portugal suka fara ɗiban mutane, suna kai su suna sayar da su, kuma su Portugees ɗin nan su suka fara kawo wannan wuri Najeriya domin su yi ciniki da shi.

    Kuma shi wannan Sarkin Portugal shi ya ba da wannan kwangilar ya ba da lasisi cewa  a ringa kawo wurin nan daga India, ana ciniki da shi a matsayin cinikin da yake tsakanin ƙasashen su Benin ɗin nan da wannan ƙasar ta su ta Satomi, kuma ya kasafta bayin nan kashi-kashi.

    Akwai yara waɗanda suke ƙasa da shekara 18 da maza da mata da kuma waɗanda suke tsakanin 18 da 30 duk kowanne da farashin sa, yaro ana sayar da shi kimanin wuri 3500, mace kuma ta kan kai ƙasa haka da haka wuri 80, wani lokacin shi kansa cinikin ma ana yin sa kamar na ban gishiri in ba ka manda. 

    Misali tsakanin kayayyaki da mutanen a na ba su kaya su kuma su bayar da Bayin. Sai ka ga ma wani an ba shi yadiddika da ba su fi ƙwaya 3 ba ko 4 ko 5 a karɓi Baiwa saboda bala’i, wani lokacin za ka sami jirgin ma ya ɗauki kamar bayi 137 jirgi guda, kuma su kansu masu tafiyar da jirgin ba wai kuɗi ake ba su ba ana ba su bayin ne su ma haka dai ake tafiyar da mutane kawai.

    Wani mai kula da bayin wanda yake tuƙa jirgin, za a ba shi kamar Bayi guda 3, ya danganta wani shugaban jirgin a ba shi bayi guda 6, mai kula da Bayin kuma a ba shi guda 4, wani ma kuma wanda suke aiki a ba shi 2 ko 1 ya dai danganta da yawan Bayin da kuma cinikin da aka zo da shi. 

    Wani lokacin za su yi tafiya 3 ko 2 a shekara, su kansu Bayin a cikin bala’i suke yawanci za ka ga waɗanda suke yara su sun iya tafiyar da rayuwar su ba su da matsala, amma manyan su na shan wahala, su kuma mata dama sun zama sai yadda aka yi da su.

    Wani lokacin ma su kansu Bayin wasu daga cikin su sukan yi faɗa saboda tashin hankali har ta kai a kashe su, da ƙyar wasu suke kai wa. Wani lokacin ma za ka ga an samu wani Bawan ya gudu har ma za ka ga suna ajiye bayanin (recording), Bawa kaza ya gudu a cikin wannan rahoto da aka samu a shekarar 1522. 

    Saboda haka akwai tabbataccen tsari na labarin yadda suka tafiyar da Bayi a wannan lokaci, kuma cinikin Bayin nan an shekara 450 ana yin san tun lokacin da su waɗannan Portugees suka fara, shekara 450 ana ɗiban mutane daga kowanne sassa na Afrika ta Yamma.

    Cinikin Bayi ya kankama a ƙarni na 16 kuma an samu labarai ma daga su kansu mutanen Portugal da wannan jirgin da ake kira Santamariya da Comansee, amma dai shekaru da suka biyo bayan wannan an fi cinikin, a wannan ƙarni na 16 an ɗebi Bayi sun kai miliyan 1.

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Ɗaya

    Cinikin Bayi A Tarihin Afrika Kashi Na Ɗaya

    Babban abin da ya fara ragargaza Afrika kamar yadda muka faɗa shi ne cinikin bayi. An yi rubuce-rubuce da yawa a kan cinikin bayi da yadda abin ya canja da yanayinsa, da su waye suka yi. Wane irin tsarin cinikin aka yi kafin Turawa su zo su kawo nasu tsarin, saɓanin abin da mutanen Afrika suka saba da shi. 

    A tarihin Afrika kamar na sauran nahiyoyi akwai bayi a tsarin zamantakewa. Bayi ana amfanin da su a harkokin gida a matsayin ma’aikata. Kafin zuwan baƙin Larabawa da Turawa, ba a ɗiban bayi ana cinikinsu zuwa ƙasashen wata nahiyar.

    Turawa su ne suka mai da Afrika nahiyar ɗiban bayi kamar dabbobi ko kayan gona. Abin da Turawa suka yi shi ne, sun mayar da cinikin bayi babbar sana’ar samun kuɗi a rayuwar mutanen Afrika.

    Bayi a ƙasashen Afrika da na Musulmi suna haɗewa da sauran mutanen ƙasar ko garin da ake so, ta hanyar ‘yantar da kansu idan suka yi na misali tsahon shekaru. Kuma ‘ya’yansu mata ana mayar da su ƙwara-ƙwarai har su haifi ‘ya’ya wanda za su zama ‘ya’ya ba bayi ba.

    Wasu daga cikinsu su zama manya mutane a masarautu. Wasu ƙasashen Afrika su na da irin wannan tsarin, yadda an rawaito cewa a Ife akwai wani Oni da yake Bawa ne a da, saboda haka wannan babu shi a tsarin bautar da Turawa suka kawo. 

    Turawan Portugal yadda suka zo da bautar su, kawai ɗiban mutane ake yi a je a bautar da su kamar dabbobi su yi aiki. Wannan shi ne tsarin da su Portugal suka kawo wa Afrika. Wannan sabon abu ne babu shi, ba a san shi ba, su Portugal su suka fara yin wannan. Sun samu ci gaba na yanayin gane duniya da su Vasko da Gama suka fara tafiye-tafiye.

    A dalilin haka suka fahimci cewa akwai damar ɗiban bayi a kai su wata ƙasar su yi aiki don ɗiban dukiya ko yin noma. Turawan Portugal sun yi tsari irin na Rumawa, na kafa ƙasashe (wato colonies da turanci). A wannan tsari ana ɗiban mutane a kai su ƙasar su zauna din-din-din suna aikin noma da na haƙo ma’adanai. Sun kafa ƙasar Brazil da irin wannan tsari, suna ɗiban bayi daga Afrika suna kai wa can. Wannan ƙasar ta Brazil ta fi kowacce a nahiyar Amerika ta kudu.

    Turawan da aka tabbatar sun fara yin cinikin bayi a matsayin sana’ar samun kuɗi  su ne Turawan Portugal, an yi shekaru 450 ana wannan mummunan ciniki. Turawan Portugal sun ajiye bayanai akan yadda suka yi wannan cinikayya a ma’aikatun (archives) tarihin su. Wannan bayanan na tun farkon zuwansu Afrika ne a shekarar 1472.

    Samun wannan ya sa masani Dr. A.F.C. Ryder ya yi rubutu masu mahimanci. Ryder (1959: 294-321) ya fassara bayani daga harshen Portguese zuwa Turanci na tafiyar wani jirgin ruwa a shekarar 1522 wanda ya ɗauko bayi daga kogin Forcados a Niger Delta. 

    Ryder ya rubuta littafi,  a ciki ya duba matsayin abubuwan da aka ajiye a ƙasar Portugal daga shekara 1522. Wannan ya ba da damar cewa a yi dogon bincike a ga yadda irin tsarin bautar su yake, kuma kamar yadda muka sani, bautar su ta bambanta da irin tsarin bautar da ake yi a Afrika.

    Su Turawa daban ne, sun shigo da wani tsari daban, kuma ba yadda za a yi a ce su bayin nan an mayar da su mutane a cikin wannan al’ummomi, saɓanin yadda yake a ƙasashen Afrika da ƙasashen musulmi, abin da ake nufi waɗannan ƙasashen Afrika da ƙasashen musulmi, ta yadda idan mutum bawa ne yana da damar da zai daina bautar nan ya shiga har ya zama wani abu, kamar yadda aka gani cewa, mata idan mutum yana da baiwa zai iya aurenta kamar yadda aka gani a shari’a zai iya mayar da ita ƙwarƙwara kuma. 

    Sun ɗebi mutanen ƙasarsu sun kai, a Afrika nan kusa da Najeriya, ya zo ya samu wani waje ana ce masa Satomi D’Principle, nan ma ya dinga ɗiban mutane yana kawo su, har ma ya yi wani abin da ba a taɓa yi ba a tarihin ɗan Adam shi ne ya fara yin sa. Ya ɗebo mutane waɗanda suke sun yi laifuffuka ya zo ya ajiye su.

    Ya ɗebo Yahudawa waɗanda aka fara yin rigima da su a can aka fara kakkashe su, sai ya ɗebo wajen dubu biyu ya kawo su Satomi, yake ɗebo mata daga wurin da ya zama Najeriya ta yanzu wato Kudancin Najeriya, sai a haɗa su da waɗannan fararen fata Yahudawa sun hayayyafa.

    Wasu Yahudawan da yawa sun mutu, amma ɗari shida sun kai labari, to haka ya kafa wannan ƙasa, shi wannan Sarki na Portugal na wannan lokaci ya yi wannan ne domin ya samu mutanen da za su ci gaba da yi masa cinikayya ta bayi a nan Afrika, saboda idan waɗannan mutane suka zo suka haɗu da mutanen Najeriya waɗanda suke da asalin su ‘yan ƙasa ne to rashin lafiyar su zai ragu. 

    Wannan sabuwar dabara ce shi wannan King Jour II ya kawo ta wanda ya yi zamani a 1515, ya ɗebi waɗannan mutane ya kawo su. An samu wannan cikakken labari da wani mutuminsu ya rubuta shi, shi kuma wannan Sarkin dai ya yi amfani da wannan mutane duk ga bayanin su (record) ɗin. Wannan abin da ya fara shi ne ya ba su damar su kafa wannan ƙasa ta Satomi N’Principle a wannan wurin da suke can a tekun Atlantic.

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu