Tag: abin girki

  • Yadda Ake Haɗin Kayan Ƙamshi

    Yadda Ake Haɗin Kayan Ƙamshi

    Assalam alaykum.

    Barkan mu da sake kasancewa cikin sabon shirinmu na girka-girken WikiHausa Wanda muke koyar da Ƙayatattun abinci namu na gida NIjeriya da na ketare. Tare da bayani a kan lafiyarsu a jikin ɗan Adam cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat shettimah.

    A yau za mu kawo muku yadda ake haɗin kayan ƙamshi na musamman, ku biyo ni domin mu koya tare.

    Ko kun san saka kayan ƙamshi cikin nama na hana ƙarni, kuma ya sa nama ya yi ƙamshi na musamman.

    Abubuwan da ake buƙata:

    Gyaɗar miya (Nutmeg)
    Citta (ginger)
    Cadarmom (hab’al)
    Cumin
    Coriander leaf
    Masoro (black pepper)
    Kaninfari (cloves)
    Kirfa (cinnamon)
    Tafarnuwa (garlic)
    Busasshiyar Albasa (dried onions)

    Yadda ake haɗawa:

    1. Za a gyara wannan kayan ƙamshin, a cire datti, sannan a daka ko a niƙa da blender.
    2. A tankaɗe shi, sai a sami leda a juye a ciki, sannan a saka a roba mai murfi.

    Hakan na sa ƙamshin ba zai fita ba na tsahon lokaci.

    Domin karanta bayani akan Dabarun Yadda Ake Girki Mai Ɗanɗano danna nan

  • Dabarun Yadda Ake Girki Mai Ɗanɗano

    Dabarun Yadda Ake Girki Mai Ɗanɗano

    Shin ko an san mene ne dalilan da suke sa girke-girken iyayenmu na da ya fi namu daɗi da lafiya?

    Ko an san dalilan da yasa girke-girkenmu ke da ƙamshi, amman ba ɗanɗano?

    Ko mun yi namu ba ya yin garɗi, kamar na iyayenmu mata da suka manyanta?

    Bari a ji sirrin nasu:

    1. Yayin da ake girki a yanzu, muna amfani da tukwanen ƙarfe, muna rufe su da murfayensu na ƙarfe, maimakon mu yi amfani da FAIFAI na kaba.
    2. Muna amfani da gas ko risho a maimakon MURHU na gargajiya.
    3. Muna amfani da dukkan abubuwan da suke da alaƙa da Turawa; mun guji na gargajiya kwata-kwata, muna amfani da colender maimakon MADAMBACI (GITTERE)
    4. Wajen niƙa kayan girki; blender maimakon DUTSEN NIƘA, mixer maimakon TURMI
    5. Yanzu za ku ga gidaje da yawa ba sa amfani da turmi, wai ya yi ƙauyanci kuma da jijjiga jiki; gaskiya yana da kyau mu gyara.

    Domin sanin Yadda Ake Ɗan Sululu danna nan