Tag: Ƙagaggun Labarai

  • Yanayin Littattafan Ƙagaggun Labarai Da Suke Koyar Da Tarbiyya

    Yanayin Littattafan Ƙagaggun Labarai Da Suke Koyar Da Tarbiyya

    Akasari akan sami:

    a. Koyar da Darussa na Rayuwa

    Littattafan ƙagaggun labaran sukan koyar da ɗabi’u irin su gaskiya, haƙuri, da tsoron Allah. Galibi sukan nuna yadda mugunta ke kai mutum ga halaka, abin da ke zama darasi ga masu karatu.

    b. Ƙarfafa Tunani da Basira (Tarbiyya ta musulunci)

    Suna motsa tunanin matasa su zama masu hangen nesa da ƙirƙire-ƙirƙire wajen magance matsalolin rayuwa. Inda ake gane tarbiyya

    c. Ƙarfafa Soyayya da Haɗin Kai

    Labaran na nuna muhimmancin taimakon juna da zaman lafiya a cikin al’umma.

    d. Hana Mugunta da Laifi

    Ta hanyar nuna sakamakon laifuffuka kamar sata, ƙarya da cin hanci, matasa suna fahimtar illar yin haka.

    e. Ƙarfafa Sha’awar Ilimi

    Jarumai masu ilimi a cikin labarai sukan zama abin koyi ga matasa wajen neman ilimi.

    f. Adana Al’adu da Harshe

    Kagaggun labaran suna adana harshen Hausa da al’adunta ta hanyar karin magana da hikima.

    Bilkisu Ahmad Funtuwa

    Bilkisu Ahmad Funtuwa tana daga cikin fitattun marubatan Hausa mata da suka taka rawar gani wajen gina tunani da tarbiyya ta hanyar adabi. Rubuce-rubucenta suna ɗauke da darussa na addini, zamantakewa, aure, da rayuwar mata. Ta yi amfani da labarai domin koyar da ɗabi’a, adalci, da darajar mace a cikin al’umma.

    Takaitaccen Tarihin Bilkisu Ahmad Funtuwa

    An haifi Bilkisu Ahmad Funtuwa a Funtua, jihar Katsina, kuma ta shahara a fagen rubutun littattafan soyayya, zamantakewa da ilimi. Marubuciya ce mai kishin addini da al’adun Hausa, wacce ke amfani da rubuce-rubucenta wajen gyaran halayen matasa da mata.

    Daga cikin shahararrun littattafanta akwai:

    – Wa Ya San Gobe

    – Allura Cikin Ruwa

    – Wa Ya San Jiki

    – Rabon Juna

    Wanann bayanin an ciro shi ne daga muƙalar da aka gabatar a taron makon Hausa wanda ya gabata a Ranar 24 ga wata Oktoba 2025 a Jami’ar Ilimi ta tarayya da ke Bichi.

    Danna nan don karanta Adabin Kasuwa A Ƙasar Hausa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Fasalin Ƙagaggun Labaran Hausa A Zamanin Zuwan Turawa

    Fasalin Ƙagaggun Labaran Hausa A Zamanin Zuwan Turawa

    Turawa sun zo sun iske ƙasar Hausa cike da ilmin abin da ya shafi karatu da rubutu a cikin Hausar ajami, kenan ko da Bature ya zo ƙasar Hausa ya iske su da ilmin zamani. Masana da dama kamar su (Magaji, 1982 da Sa`idu, 1985 da Hafsat Tsiga, 1987 da Yahya, 1988 da Ampah, 1989 da da Dogara, 2008 da Sulaiman, 2008 da Gusau, 2008 da Malumfashi, 2009,) sun kawo bayanai gwargwado masu gamsarwa game da samuwar rubutun boko  da yadda ya yi tasiri a ƙasar Hausa.

    Abin da kurum za a ƙara a nan bai wuce cewa an fara samun ɓurɓishin labarin ƙasar Hausa a wurin Turawa ta hannun Al-Hassan Ibn Muhammad Al-Wizas Al-Fasi, wato Leo Africanus wanda aka tsare a kurkuku a ƙasar Italiya inda ya bayyana a cikin littafinsa Na Bakwai ziyarar da ya kai ƙasar Barno da wasu daulolin na Hausa a tsakanin 1513 zuwa 1515.  Samun wannan littafi shi ya ba mutanen ƙasar Turai haske kan yanayin ƙasa da rayuwa a wasu ƙasashe na Afirka ta Yamma.

    Wannan haske da ƙasashen Turai suka samu game da ƙasashen Afirka, shi ya sanya suka fara ƙoƙarin turo mutanensu domin su dubo musu abin da ke faruwa a wannan yanki na Afirka. An samar da ƙungiyoyi masu manufofi daban-daban, musamman waɗanda za su binciko ainihin yanayin ciki da wajen Afirka.

    (Yahaya, 1988:75) ya ruwaito Turawa masu yawon gano Afirka na farko hankalinsu ya fi karkata ne kan labaran ƙasar wuraren da suka ziyarta kamar kogunansu, tuddai, tsirrai, bishiyoyi, albarkatun ƙasa, sunayen garuruwa da fasalin mazaunansu, da tsarin mulkinsu, da cinike-cinikensu da sauransu. Saboda haka, su ba su ƙarfafa bincike kan harsunan waɗannan mutanen ba.

    Daga ƙarni na 18 zuwa na 19 ne aka fara turo masu bincike, musamman bincike kan al`adu da harsuna da addinan ƙasashen Afirka. Akwai ƙungiyar ‘yan mishan wadda ta zo Afirka a daidai wannan lokaci ƙarƙashin jagorancin J.F Schon, da C. H. Robinson, da Hans Vischer, da G.P Bargery da wasunsu da dama.

    Daga hannun waɗannan `yan mishan ɗin da `yan leƙen asiri labaran ƙasar Hausa da jama`arta suka isa ƙasashen Turai. Wasunsu kuwa kamar su Robinson, da Miller, da Richardson, da Ryder, da Burgin dama sun zauna a Tripoli sun koyi harshen Hausa, wannan ya sa ko da suka zo ƙasar Hausar ba su sha wata wahala ba, kuma wasu daga cikin su sun zagaya, kuma sun zauna a sassan ƙasar ta Hausa, daga baya suka koma gida suka bayyana abubuwan da suka gano, wasu kuma suka ci gaba da rayuwa a ƙasar suna ayyukan yaɗa addini. (Malumfashi, 2009).

    Zaman waɗannan mutane a ƙasar Hausa ya ba su damar fara samar da abubuwan karantawa daga abin da suka ji, wanda wannan ya taimaka ƙwarai da gaske wurin gina adabin Hausa da al`adun Hausawa. J.F Schon shi ne zaƙaƙuri, kuma fitacce wurin rubuce-rubuce cikin Hausa a Turai a cikin ƙarni na 19. Bayan shi akwai irin su G.P Bargery, da W.R. S. Miller, da Hans Vischer waɗanda duk ƙungiyar mishan ta C.M.S ta turo su.

    Wannan zuwan bakin Turawa ya zama tubali wajen juya adabin bakan Hausa ya koma a rubuce a karo na biyu. Za a iya cewa kusan tun daga wannan lokacin ne aka fara mai da labarai da tatsuniya da karin maganganu da maganganun azanci da kuma al`adun Hausawa  a rubuce cikin Hausar boko.

    Kusan daga ƙarshen wannan ƙarni na 19 zuwa farkon ƙarni na 20 ne aka samar da litattafai masu yawa da suke ɗauke da wannan fasalin, wasu daga cikinsu sun haɗa da ; Hausaland na C.H. Robinson (1893), da Spécimens of Hausa Literature na C. H. Robinson (1896), da Hausa Notes na W.R. Miller (1901), da Batu Na Abubuan Hausa na W.H. Brooks (1903), da Littafe Na Tatsunniyoyi Na Hausa na Frank Edgar (1911), da Hausa Superstitions and Customs na Tremearne (1913), da sauransu dai da dama. (Yahaya, 1988:81).

    Bayan `yan Mishan da suka mamaye ƙasar Hausa, sai kuma Turawa `yan mulkin mallaka suka diro wa ƙasar. A daidai 1900 ne gwamnatin Ingila ta miƙa wa Gwamna Lugga jan ragamar mulkin Nijeriya ta arewa. Daga kama aikin shi na Gwamna ya fara aiwatar da wasu canje-canje. Ya tumɓuke tutar Royal Niger Company a Lakwaja ya sanya ta mulkin Ingila.

    Ya tashi hedikwatar jihar arewa daga Lakwajar ya mai da ta Zungeru. Ya dinga aika wa sarakunan ƙasar Hausa da su ba da kai, wasu sun bi, wasu kuwa suka ƙi. Ya tura da sojoji garuruwan na ƙasar Hausa kamar Zariya da Yola da Daura da Bauci da Barno da Katsina sai Sakkwato, inda bayan hijirar sarkin musulmi Attahiru suka ƙulla yarjejeniya bayan an fafata (Yahaya, 1988:89).

    Bayan Turawan mulkin mallaka sun ci ƙasar Hausa, dama sun iske harsashin da ƙungiyoyin mishan suka assasa na koyon karatu da rubutun boko, ga kuma na ajami da Larabci da ya daɗe tare da al’ummar, sai suka gina makarantun boko bisa wannan harsashi, duk rubutu da karatu aka ci gaba da yin su cikin Hausar boko.

    Saboda haka, kusan daga wannan lokacin ne aka fi samar da ayyuka wajen adana labaran gargajiya na Hausa a rubuce. Daga wannan lokacin ne, wato a farkon ƙarni na ishirin lokacin da Turawan mulkin mallaka suka mamaye ƙasar Hausa ƙarƙashin jagorancin gwamna Lugga, sun yi iyakar bakin ƙoƙarinsu domin su tafi da hanyar rubutu ta Ajami da Larabci, don cimma burinsu na mulkin mallaka da ayyukan mishan, amma ba a je ko`ina ba suka kasa.

    Wasu daga cikinsu suka ba hukumomin mulkin mallakar shawarar lallai hukumar ta sake salo, domin kar a bar Hausawa wurin samun ayyukan gwamnati. Shi kan shi gwamna Lugga sai ya hango cewa dole ne ya sami ma’aikata `yan ƙasa waɗanda za su taimaka masa wajen gudanar da harkokin mulki a ofisoshin gwamnati a bisa tsari irin na Turai, kafin a samu yin haka kuwa, dole sai an kafa makarantun ilmin boko, haka kuma hukumomi sun lura ya kamata a ba al`ummar Hausa ilmin da mulkin mallaka ya zo da shi, wato karatu da rubutu irin na Ingilishi, maimakon wanda suke da shi na Larabci da Ajami. Wannan shi ne ya haifar da buɗe makarantun boko a arewacin Nijeriya daga Turawan Mulkin Mallaka.

    Bayan samuwa da bunƙasuwar makarantu da malamai a sassa da Lardunan Arewa, sai wata matsala ta kunno kai, wannan matsalar kuwa ita ce ta samar da litattafan koyarwa a waɗannan makarantun. Ganin wannan matsalar na neman kawo tsaiko ga makarantun nan, sai Gwamnatin jihar Arewa ta kafa hukumar fassara (Translations Bureau ) a shekarar 1929, An ɗora wa wannan hukuma ta fassara nauyin samar da litattafai ta hanyar fassara daga wasu harsuna musamman Larabci da Turanci zuwa  Hausa.

    Sannan kuma ta taimaka wurin wallafa litattafai cikin harshen Hausa, ta kuma shirya litattafai domin manya da ƙanana don karantarwa a makarantu, daga ƙarshe kuma ta taimaka wa `yan ƙasa su yi wallafar ƙagaggun labaran cikin Hausa. Wannan hukuma ta yi aiki ƙwarai da gaske wurin samar da litattafan da aka sa ta samar.

    Domin faɗaɗa aikin wannan hukuma ne ya sanya a shekarar 1933, aka canza wa wannan hukuma ta fassara suna zuwa hukumar Talifi (Literature Bureau) domin ta faɗaɗa daga aikin da hukumar fassara ke yi. Wannan hukuma ta Talifi ta yi ta ƙarfafa bayar da ilmin boko, ta kuma samu goyon baya daga `yan ƙasa, daga baya ta ga ya kamata a faɗaɗa wannan shirin ya haɗu da tarihin ƙasa da sauransu. Saboda haka sai aka samar da Jaridar mai suna ‘Jaridar Arewa’ wadda ake bugawa cikin harsunan Hausa da Larabci, da kuma Turanci, har zuwa shekarar 1939 da aka samar da Gaskiya ta fi Kwabo.

    Ayyukan wannan hukuma sun ci gaba har cikin 1945, amma fa duk wannan aikin da wannan hukumar ke yi, ba ta da injunan ɗab`i nata na kanta, sukan tsara aikinsu, su aika da su maɗaba’a ta Jos, ko Kaduna ko kuma Ikko, in kuma ta yi ƙamari sai a tura da shi Ingila. Domin a samu wurin buga litattafai da jarida da sauran talife-talifen da hanzari a hukumar, sai Gwamnan Nijeriya na wannan lokacin Sir Arthur Richards ya nemi Gwamnatin Ingila ta taimaka wa hukumar Talifi  da kuɗin sayen Injunan buga litattafai da kuma na gina kamfanin wallafa.

    Wannan ne ya sa aka kafa kamfanin Gaskiya wanda ake kira Gaskiya Corporation a Tudun Jukun cikin garin Zariya a shekarar 1945. Shi wannan kamfani na Gaskiya Corporation shi ne ya ci gaba da ɗaukar nauyin wallafa duk litattfai da jaridar da Hukumar Talifi ke samarwa. Ire-Iren waɗannan litattafn sun haɗa da ; Ka Koyi Karatu, da Ka Ƙara Karatu, da Ka Yi Ta Karatu, da Bala Da Babiya, da Yawo Duniya Haji Baba, da Mango Park Mabuɗin Kwara da sauransu da dama. (Yahaya, 1988:97).

    A shekarar 1953, Gwamnan jihar arewa na lokacin Sir Bryan Sherwood Smith (Mai Wandon Karfe) ya kafa wani kwamiti na yaƙi da jahilci, wannan kwamitin ya duba hanyoyin da suka kamata a bi domin samar da ilimin zamani. Sannan kuma suka ba da shawarar hanyar da za a bi domin a yi yaƙi da jahilci, ita ce a samar da litattafai cikin Hausa rubutun boko da na  ajami da kuma wallafa litattafai cikin harsunan arewa.

    Wannan ne ya sa aka samar da Hukumar Yaƙi Da Jahilci Ta Arewacin Nijeriya, Northern Region Literacy Agency, (NORLA) a shekarar 1954, aka naɗa mata shugaba wani Bature W.F. Jefferies, daga nan sai aka ɗauke nauyin buga Litattafai daga Gaskiya zuwa NORLA, kuma yawancin ma`aikatan Gaskiya ɗin suka koma NORLA ɗin. Hukumar NORLA ta yi matuƙar ƙoƙari wurin samar da litattafai, domin a iya cewa babu wata hukuma da ta yi aikin da hukumar NORLA ta yi.

    Baya ga litattfan yaƙi da jahilci da wannan hukuma ta samar, ta kuma wallafa litattfai don makarantu da sauran jama`a masu son abin karantawa don ƙaruwa da ilimi ko don nishaɗi.

    Haka kuma NORLA ta sake buga wasu litattafai da hukumomin baya suka samar, daga cikin litattafan da NORLA ta samar akwai na addini; Ibada Da Hukunci, da Jagorar Mai Sallah, da Tarbiyya ga mutum, da sauransu. Akwai na labaran hira ; Bayan Wuya sai Daɗi, da Sauna, da Nagari Na kowa, da Tauraruwar Hamada, da Da’u Fataken Dare da sauransu. Akwai kuma na tarihi kamar su ; Sarauniyar Zazzau, da Zuwan Turawa Nijeriya ta Arewa, da Wali Ɗanmarna da sauransu.

    Bayan litattafai da hukumar NORLA take tsarawa, ta kuma rinƙa buga jaridu na kusan kowane lardi, duk da cewar kuma jaridar Gaskiya wadda dama ita ta kowane lardi ne tana nan tana fitowa. Ita dai Hukumar NORLA duk da wannan jan aiki da ta yi, ta samu matsala, inda a 1959 ta durƙushe saboda hada-hadar siyasa da ta mamaye arewacin Nijeriya.

    `Yan kuɗaɗen da hukumar ke samu daga Gwamnatin Jihar Arewa suka tsaya, daga nan sai hukumar ta mutu. Ita dai wannna hukuma ta NORLA ta yi zamani ne daga 1954 zuwa 1959, amma sauran kayan aikin hukumar sai suka koma kamfanin Gaskiya inda aka ci gaba da kula da su, sannan kuma kamfanin na Gaskiya ya ci gaba da buga litattafan da hukumar NORLA take bugawa.

    Da tafiya ta yi tafiya ne Gwamnatin jihar Arewa ta lura ayyukan sun yi wa kamfanin Gaskiya yawa, wannna ne ya sanya aka ɗauke aikin buga jaridar Gaskiya ta fi kwabo daga kamfanin Gaskiya, domin a rage masa aiki, aka bar su da buga litattafai kurum. Da gwamnati ta ga aikin ya yi yawa, sai ta yi ƙoƙarin samun wani kamfani wanda zai ci gaba da wannan aikin. Wannan ne ya sanya aka nemo kamfanin Macmillan daga Ingila inda aka ƙulla yarjejeniya da shi aka samar da kamfanin wallafa na NNPC (Northern Nigeria Publishing Company) a watan Oktoba na 1966.

    An sakar wa kamfanin NNPC mara na ya zaɓi duk littafin da ya ga dama bugawa, shi kuma kamfanin Gaskiya sai aka bar shi kurum a matsayin kamfanin kasuwanci. Sannan kuma shi wannna kamfani na NNPC yana karɓar litattafai daga marubuta Hausa domin ya buga musu.

    Wannnan kamfani shi ma ya sake buga wasu daga cikin litattafan da hukumomin baya suka samar, wasu daga cikin litattafan da suka samar sun haɗa da ; Tauraruwa Mai Wutsiya na Umaru Dembo, da Uwar Gulma na A.M. Sanda, da Daren Sha Biyu na Ibrahim Yaro, da Iliya Ɗan Mai Ƙarfi na Ahmadu Ingawa, da Matar Mutum Ƙabarinsa na Bashir Roukbah, da dai sauransu da dama, wasu na addini ne, yayin da wasu waƙoƙi ne ko labarai ko kuma wasa kwaikwayo.

    Bayan wannan kamfani na NNPC da gwamnati ta samar, akwai wasu kamfanonin wallafa na raya al`adun Hausawa da samar da ƙagaggun litattafan Hausa. Akwai kamfanin litattafai na Oxford wanda ya koma Úniversity Press Limited’ (U.P.L), akwai kuma kamfanin Longman, shi ma na tallar litattafai ne, akwai kamfanin Thomas Nelson, akwai kamfanin Alhuda-huda Publishers, da Ilesanmi, da Truimph Publishers da dai sauransu da dama .

    A shekarar 1978 ne, kamfanin NNPC ya sanya gasar samar da ƙagaggun labaran Hausa da kuma wasan kwaikwayo. A tarihin ƙagaggun labaran Hausa, a iya cewa wannan gasa ita ce ta biyu, marubuta da yawa sun shiga wannan gasa, amma daga ƙarshe aka fitar da waɗanda suka lashe gasar kamar haka;

    • Mallakin Zuciyata  na Sulaiman Ibrahim Katsina
    • So Aljannar Duniya na Hafsat A. Abdulwaheed
    • Amadi Na Malam Amah   na Magaji Ɗanbatta

    Bayan wannan gasa da kamfanin NNPC ya samar, akwai wata gasa da za a iya kira ta uku a shekarar 1982, wadda ma’aikatar al’adun gargajiya ta tarayya ta shirya don bunƙasa manyan harsunan Nijeriya. Mutane wajen 30 sun shiga wannan gasar, amma dai an zaɓi guda bakwai waɗanda ake jin sun yi fice aka buga su, waɗanda aka zaɓa kuwa su ne;

    • Turmin Danya Na Sulaiman Ibrahim Katsina
    • Zaɓi Naka Na Munir Mohammed Katsina
    • Ƙarshen Alewa Ƙasa Na Bature Gagare
    • Tsumangiyar Kan Hanya Na Musa Muhammad Bello
    • Dausayin Soyayya Na Bello Sa`id
    • Soyayya Ta Fi Kuɗi Na Hadi Alƙanci
    • Wasa Ƙwaƙwalwa Na  Mohammed Yahuza

    Daga wannan lokaci ne abubuwan ɗab’i suka fara sauya fasali a arewacin Nijeriya, harkar samar da ƙagaggun labaran Hausa suka fara ɗaukar wani sabon salo, samar da litattafan sai suka tashi daga kamfanonin na hukuma ko waɗanda hukumar ta amince da su, sai marubuta suka fara samar da litattafansu, suna fiddo su, sannan kuma fasali da jigon litattafan duk suka sauya daga yadda aka san su, suka koma na wasu jigogi daban, wannan sabon fasali shi ne masana suka bayyana da Adabin Kasuwar Kano ko Labaran Soyayya, ko ƙagaggun Labaran Hausa da sauransu, kamar yadda za mu gani a babi na gaba.

    Naɗewa

    A wannan babin an kalli samuwar ƙagaggun labaran Hausa kama daga tatsunniya da tarihihi da labari da kuma ƙissa har zuwa lokacin da suka canza fasali suka tashi daga na ‘KA’ suka koma a rubuce wato bayan haɗuwar Hausawa da baƙi (Larabawa da Turawa).

    Sannan an ga yadda aka fara samar da karatu da rubutu a ƙasar Hausa da kuma yadda aka samar da ƙagaggun littattafan labaran Hausa daga gasa, wanda wannan ya kasance tamkar mabuɗin farko wajen samar da abin da ake kira Adabin Kasuwar Kano.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Don karanta Ƙagaggun Labaran Hausa Na Zamani danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

     

  • Ƙagaggun Labaran Hausa Na Zamani

    Ƙagaggun Labaran Hausa Na Zamani

    Da yake mun ga yadda ƙagaggun labaran Hausa na baka suka sauya fasali bayan haɗuwar Hausawa da baƙi, musamman Larabawa. A wannan ɓangaren kuma an kalli yadda waɗannan ƙagaggun labaran  na gargajiya suka sauya fasali, suka koma a rubuce, ta yadda maimakon a kai da ake riƙe su, sai yanzu suka koma a rubuce, a zamanin zuwan Larabawa da Turawa.

    Fasalin Ƙagaggun Labaran Hausa a Zamanin Larabawa

    Ƙagaggun labaran Hausa sun sauya fasali ta wata hanyar daban bayan da Hausawa suka haɗu da Larabawa, ta inda a wannan karon aka mai da wasu daga cikin waɗannan ƙagaggun labaran a rubuce a maimakon a ka da suke adane.  Daga binciken da aka yi an fahimci babu adabin gargajiyar Bahaushe da ake da shi a rubuce, sai lokacin da Hausawa suka haɗu da Larabawa, inda suka fara yin rubutun su cikin Ajami.

    Masana da dama (dubi Magaji, 1982, Dokaji, 1978, Yahya, 1988, Gusau, 2008 da kuma Malumfashi, 2009) duk sun yarda da Musulunci ya shigo ƙasar Hausa da daɗewa, tun wajen ƙarni na goma sha ɗaya zuwa na goma sha uku. Su kuwa Magaji, 1982, da Abdullahi, 1997 sun ruwaito cewa, ‘a wajen ƙarni na 12 zuwa na goma sha uku, wato lokacin da sarkin Kano Naguji Ɗan Ɗariƙu (1194-1247) wasu Larabawa ‘yan kasuwa suka fara kawo Musulunci Kano.

    Daga baya kuma zamanin sarkin Kano Aliyu Yaji (1349- 1385) wasu Wangarawa mutanen ƙasar Mali suka fara zuwa ƙasar Hausa don ƙarfafa addinin musulunci. Sun zo Kano tare da litattafan koyar da addinin Musulunci, kuma suka kafa makarantu da masallatai.

    Tarihi ya nuna kafin zuwan addinin Musulunci ƙasar Hausa, Hausawa ba su da wata hanya tasu ta karatu ko rubutu. Adabin Hausa a lokacin na baka ne, ana kuma watsa shi ta baka, a kuma adana shi da kai. Saboda haka zuwan waɗannan malamai shi ne matakin farko na koyon karatu da rubutu a ƙasar Hausa.

    To sai dai, duk da bayyanar waɗannan malaman da kuma samun cikakkiyar hanyar karatu da rubutu bayan watsuwar addinin Musulunci da kuma samar da sababbin masu ilmi cikin al`umma, wannan bai haifar da wani abun a-zo-a-gani ba game da samuwar adabin Hausa da ta shafi addinin Musulunci ba.

    A wannan lokacin, duk faɗi-tashin da malamai da almajirai suka yi ta yi, ta tsaya ne a kan yadda mutane za su fahimci addinin Musulunci, da kuma yadda za su yi aiki da shi cikin al`amurransu na yau da kullum. Wannan ya sanya adabin Hausa bai samu wani canji ba, yana na dai a adane cikin ƙwaƙwalwar mutane, duk lokacin da  ake buƙata sai a aiwatar da baki kuma a inda ya dace, kamar dai yadda Sulaiman, 2008 ya ruwaito daga Hisket (1975).

    Sai daga baya ne malaman addini da sarakuna suka yi amfani da rubutun Ajami ƙwarai da gaske wajen aikawa da saƙonni zuwa ga ‘yan uwansu sarakuna da malamai. Malamai sun yi wallafe-wallafe da dama cikin ajami don watsa addinin Musulunci, wasu a tsarin waƙoƙi, wasu kuma maganganun azanci ne suka rubuce, wasu kuma fassara suka yi.

    Wannan ya sanya yawa-yawan ayyukan adabin Hausawa, musamman waɗanda suka shafi ƙagaggun labarai na gargajiya da waɗanda aka tsinto daga Larabci suka shigo da sabuwar riga ta rubutun Ajami da Larabci ta yadda daga baya za ka ɗauka cewa tun can asali da wannan rigar aka haife su.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Domin karanta Gwamutsuwar Labaran Gargajiya Na Hausa Da Baƙin Al’adu danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Ƙagaggun Labaran Hausa Cikin Tarihi

    Ƙagaggun Labaran Hausa Cikin Tarihi

    Babi Na Biyu: 

    A cikin wannan babin an bi salsalar ko kuma an kawo taƙaitaccen tarihin samuwar ƙagaggun labaran Hausa ne. An dubi yadda aka fara samar da labaran Hausa na gargajiya kafin su koma a rubuce, da kuma yadda suka samu cuɗanya da baƙin al’adu.

    Ya’allah baƙin nan na kusa ne a cikin ƙasar Hausa ko kuma na nesa kamar Larabawa da kuma Turawa domin ganin yadda ƙagaggun Labaran Hausa suka samu canji da fasalce-fasalce daga garjiya zuwa zamani.

    Ma’anar Ƙagaggun Labaran Hausa

    Masana da dama sun kawo ma`anar ƙagaggen labari da cewa warwarar bayani ne bi-da-bi a kan aukuwar wasu abubuwa da yadda suke gudana, saboda haka ma’anar labari ta haɗa da jerin bayani, da ambaton dukkan muhimman al’amurra da iya siffanta su a lafazi mai kyau (Zarruƙ, 1990).

    Ke nan a iya cewa ƙagaggen labari ya ƙunshi waɗansu labarai masu ɗan tsawo, ana kuma yin su ne a lokacin hira kamar, labarai na jarumai ko `yan fashi ko na almara, irin su labaran hikima ko wasa ƙwaƙwalwa da kuma tatsuniyoyi irin na su gizo da ƙoƙi da hikayoyi na iskokai ko kuma aljannu.

    Haka kuma Magaji (1982:47) ya ce labarin zube (ƙagaggen labari) ya ƙunshi labarai masu ɗan tsawo kamar tatsuniya (Ga ta nan), da almara, da hikayoyi, da ƙissoshi da sauransu. Haka kuma akwai guntattakin maganganu na hikima kamar kirari, da karin magana, da kacici-kacici, da zaurance, da salon magana da dai sauransu.

    A taƙaice za a iya cewa labarai sun kasu gida biyu; na haƙiƙa ko kuma masu ƙamshin gaskiya, wanda aka fi sani da ƙissa ko tarihi ko tarihihi da kuma na ƙirƙira ko kuma ƙagaggen labari, wanda bai da asali ko tushe.

    Saboda haka ana iya bayyana ƙagaggen labari da wata hikima, ko basira ko tunani irin na ɗan Adam da ya ƙaga kan wani abu wanda bai ji ba, kuma bai gani ba, ya furta shi da fatar baki domin watsa wata manufa don koyarwa ko kuma hannunka-mai-sanda da jagora don nishaɗi.

    Akwai ire-iren waɗannan ƙagaggun labaran da yawan gaske a cikin adabin Hausa da suka haɗa da tatsunniya da almara da hikaya da zaurance da salon magana da kirari da take da zambo da sauransu da dama.

    Haka kuma ana iya kallon ƙagaggun labarai na baka da zance na hikima da ake shiryawa cikin azanci da yake zuwa a kara zube, kuma mai ɗan tsawo, mai kuma ban sha’awa da koyar da dabarun zaman duniya ta hanyoyi da matakai daban-daban.

    Samuwar Ƙagaggun Labaran Hausa

    Tun kafin haɗuwar Bahaushe da baƙi, yana da hanyoyi da dama da yake amfani da su domin ilimantar da kuma tarbiyantar da ‘ya’yansa ta yadda za su tashi cike da dabaru da kuma ilmin zamantakewa. Waɗannan hanyoyin kuwa su ne ire-iren ƙagaggun labaran da ya tanadar, sun kuwa haɗa da maganganunsa na azanci da sauransu.

    Tambayar da aka yi ita ce yaya aka yi waɗannan abubuwa suka samu? Daga waɗannan maganganun azanci ne aka samar da ƙagaggun labarai, waɗanda tushensu shi ne adabin bakan al’umma.

    Kuma kamar yadda masana suka nuna wannan ba sabon abu ba ne, domin kuwa ko a zamanin ci gaban Girkawa, ire-iren waɗannan sassan adabin aka fi ba muhimmanci wajen tarbiyantar da jama’a, domin labarai da maganganun azanci da suka yi tashe a wancan lokacin da baki ake aiwatar da su, daga wannan birni zuwa wancan (Malumfashi, 2004:6), sun kuma taimaka wajen ilmantar da al’ummar.

    A nahiyar Asiya kuma irin waɗannan al`adu na fasahohin baka  sun ginu, ta yadda a fadojin masu mulki da masu arziƙi, an samar da manyan masana labarai da maganganun azanci don su zama tamkar makaranta ta koya wa ‘ya’yan masu mulki da sauran masu arziƙi tarbiyya, su kuma nishaɗantar da al`ummar nahiyar. Labaran Sansikirti a Indiya da maƙwabtanta duk irin wannan fasalin suka ɗauka, kuma da yawa daga ire-iren waɗannan labaran sun kasance asalinsu ɗaya ne, wato tatsuniyoyi da almarorin jama’ar wannan yanki ne, (Malumfashi, 2004:6)

    Saboda haka, muna iya cewa a ƙasar Hausa ma irin wannan adabi ya yi tashe a lokacin maguzanci ko jahiliyya. Wato gargajiya ita ce jahiliyyar Bahaushe, lokacin da al’ummar Hausawa ba su waye ba ko kuma lokacin ba su haɗu da wasu baƙi ba, wannan zango ne tsakanin ƙarni na 10 zuwa na 11.

    A wannan lokacin ana neman matakai waɗanda za a fara rayuwa ta kan su, lokaci ne na neman wurin zama da abinci da gina shugabanci da yadda za a tsara shi, da kuma tsarin  sana`o`i daga wurin mutane. Don haka, ilahirin wannan lokaci ya ƙunshi fafutukar gina al`adu na gargajiya. Wannan shi ne zangon da ya samar da adabin baka da sassansa da lokacin da ake ganin ana da adabin ka na tsantsar Hausawa.

    A wannan lokacin ne aka samar da kirare-kirare na bauta da kirarin noma da na farauta da kuma waƙe-waƙen mata da labarun gargajiya da labarun tatsunniya da na jaruntaka da kuma na ban dariya (Muhammad, 2005:6).

    Saboda haka ko da irin wannan adabi na baka ya ginu, ya tashi ne kurum ya gan shi cikin al`ummar Hausawa, ta yadda Hausawan ke koyar da ‘ya’yansu dabarun zaman duniya ta yin amfani da sassan adabin baka na zube (ƙagaggun labarai) da suka haɗa da tatsuniyoyi da labarai da makamantan su. Bari mu dubi wasu daga cikin waɗannan sassan ƙagaggen labarin Hausa, mu ga yadda suke a taƙaice.

    Tatsuniya

    Tatsuniya tana daga cikin manyan rassa na adabin bakan Bahaushe, kuma ƙagaggen labari ne da Bahaushe kan ba ‘ya’yansa domin tarbiyya ta yadda za su tashi cikakku kuma kamilan mutane.

    Masana da dama sun daɗe suna kallon tatsuniya ta fuskoki daban-daban, Umar (1978: 25) yana cewa “tatsuniya wani ƙagaggen labari ne da magabata kan shirya, musamman don tarbiyya bisa ga tsarin gargajiya”. Amma shi kuma (Gusau, 2006:112) cewa yake “tatsunniya wani tsararren labari ne wanda magabata (musamman tsofaffin mata) suke shiryawa cikin hikima da nuna ƙwarewa da naƙaltar harshe da ya ƙunshi wata shiryarwa da nuni zuwa ga halaye da ilmin zaman duniya, sannan da saka nishaɗi da raha ga rayuwa da kuma cinye dare”.

    Duk da irin yadda tunani ya bambanta tsakanin masana game da ma’anar tatsuniya, sai dai masana da dama (Yahya, 1972 da Umar, 1978 da Alhassan da wasu, 1982 da Ɗangambo, 1984) duk sun yarda da cewa tsofaffi ne kan shirya tatsuniya, kuma ƙagaggen labari ne da akan shirya domin ilimantarwa ga yara.

    Daga nazarin da aka yi an fahimci cewa tun can farkon al`amari Hausawa suna da labaransu na tatsuniyoyi waɗanda su ne suka ƙirƙiro su da kansu don nishaɗi da koyarwa. Sun mallaki wannan hanya ta bayyana matsayinsu, musamman ga yara, tun jimawa, ba sai da suka cuɗanya da wata al`umma ta koya musu ba.

    Hasali ma dai ba za a iya bugun gaba a ce ga lokacin da aka fara yin ta ba. Tatsuniya gadon gado ce, ta ginu a sakamakon tasirin al`adar rayuwa ta Hausawa, har ta zama ruwan dare game duniya (Yahya da wasu 1992). Haka kuma, labari ne ƙagagge ake harhaɗawa a tayar da gangar jikin tatsuniya, har a kaɗa ta, ta bayar da wani amo da ake son sadarwa ga masu saurare.

    Saboda haka muhimmancin tatsuniya ya fi gaban a ambata, domin kuwa tatsuniya makaranta ce ta malam Bahaushe, ta nan yakan ilimantar da `ya`yansa dabarun zaman duniya tun kafin Bahaushe ya sadu da baƙi. Al`adun Hausawa ne suka haifar da tatsuniya kuma wajibi ne a yi la`akari da cewa tatsuniya ta samu tun kafin Bahaushe ya iya karatu da rubutu balle ya kafa makaranta.

    Tatsuniya ta wanzu cikin al’ummar Hausawa wadda tunaninta  da hikimominta da fannonin ilminta duk da baki ne akan baza su, daga wannan mutum zuwa wancan da kuma wannan zamani zuwa wancan. Koyo da koyarwa, ɗabi’ar ɗan Adam ce, saboda haka ya zama tilas ga Bahaushe ya ƙirƙiro wata hanya ta aikawa da hikimominsa da al’adunsa daga zamani zuwa zamani.Ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi ita ce tatsuniya. Ta amfani da tatsuniya Bahaushe kan kaifafa tunanin ‘ya’yansa.

    Labari

    Labari shi ne wani zance da yake abkuwa tsakanin mutane ko tsakanin mutum da mutum wanda ya wuce tsayawa a gaisa kurum. Kusan duk wani abu da ya danganci samar da wani abu game da wani abu mai tsawo ko gajere ana iya kiranshi labari.

    Shi dai labari zai iya kasance wa tsararre mai ma`ana sannan kuma yana da farko da kuma ƙarshe wanda kuma zai iya cusa tarbiyya ko kuma a koyi wani darasi daga cikin shi. Kazalika, labari na iya kasancewa a rubuce ko a magance.

    Labari na zuwa ta hanyoyi daban-daban, kamar Yanayin abinda labarin yake ɗauke da shi ta fuskar jigo ko siffa, wato dai a taƙaice abinda yake koyarwa. Kamar labarai na jaruntaka, da tarbiyya, da girmamawa, da zaman duniya da sauransu da dama.

    Ƙissa

    ƙissa kalma ce da aka samo daga harshen Larabci wadda ta shige tsundum a cikin adabin Hausa. Ita da wannan kalma tana ɗauke da ma’anoni biyu ne a cikin harshen Larabci. A ma’ana ta  lugga ƙissa na nufin bibiya ko ƙididdigewa, wato mutum ya bi diddigin wani abu har zuwa ƙarshensa.

    A ma’ana ta fannin ilimi kuwa, ƙissa na nufin ba da labarai dangane da mutanen da suka shuɗe, ko kuma ba da labari a kan waɗansu abubuwa da suka auku a da, ko kuma wani labari da ke kara zube da ya ƙunshi shiryarwa zuwa ga addini ko gaskiya ko neman tsira kan wani abu.

    A ra`ayin masana  (Gusau,1995:68) an fi danaganta ma’ana da manufar ƙissa a kan labarun da suka danganci addini kawai. Wato bayanai a kan rayuwar annabawa da sahabbai da waliyyai da sauransu. Duk da haka akwai wasu labarai na ƙayatarwa da jawo hankali da za a iya kiran su da ƙissa, kamar irin ƙissoshin da suka shafi soyayya. Don haka akan ce ƙissa wata hanya ce ta cusa wata manufa cikin zukatan masu saurare.

    Duk da irin wannan hasashe game da ƙissa an fahimci cewa ta shafi abin da ya biyo labaran Annabawa kamar yadda ya zo cikin Alƙur’ani mai girma, inda ake da surori da suke bayyana labaran annabawa da aka zayyana a cikin Alƙur`ani.

    Sai dai ita ƙissar da Bahaushe ke bayani ta shafi wadda aka gina bisa tunanin Bahaushe, wato ga yadda labarin yake a zahiri amma a ƙara masa wani abu ko dai don daɗin labarin ko kuma domin a ƙara ƙayatar da mai sauraro. Misali ƙissar Annabi Yusuf  ko ta Annabi Sulaiman ko kuma ta Annabi Nuhu za a same su da ɗan bambanci da wadda Alƙur’ani ya zo da ita.

    1. Ƙissar Cinye Dare: Wadda ta ƙunshi labarai da zuntuttukan da mutane suke yi don cinye ko ƙarasa dare.
    2. Ƙissar Addini: Wannan ta ƙunshi labarai ne da ake tsarawa a kan wani abu da ya auku na addini a lokacin annabawa da sahabbai da waliyyai da shehunnai da sauransu.

    A Hausance ke nan, ƙissa labari ne na gaskiya da aka bayar a kan rayuwar Annabawa da sahabbai ko waliyyai ko shehunnan malamai, ko wasu bayin Allah da sauransu waɗanda suka shafi addinin Musulunci, musamman waɗanda Alƙur’’ani da hadisai suka kawo bayanansu.

    Masana (Gusau, 1995: 69) sun raba ƙissa zuwa gida huɗu;

    1. ƙissar Annabawa wadda ta bayyana rayuwarsu ta haƙiƙa da irin gwagwarmayar da suka sha wajen isar da saƙon Ubangiji.
    2. ƙissar sahabbai da waliyyai da shehunnai wadda ke ƙunshe da rayuwarsu.
    3. ƙissar sauran bayin Allah wadda ke nuna rayuwar wasu bayin Allah nagartattu waɗanda suka miƙa wuyansu ɗungurungum zuwa ga addini Allah
    4. ƙissar kangararrun mutane waɗanda suka bijire wa addinin Allah.

     Tarihihi

    Asalin wannan kalma ta tarihihi an samo ta ne daga kalmar tarihi ta hanyar liƙa wa kalmar ɗafe-ƙeya na ‘hi’, sai ta koma ‘tarihihi’. Sai dai abin lura a nan shi ne tarihi dai yana nufin wani labari ne na haƙiƙa da ya taɓa faruwa a cikin al’umma.

    To amma shi tarihihi za a iya cewa  wani labari ne na wasu abubuwa da suka taɓa wakana na haƙiƙa a cikin al’umma, sai dai irin wannan labarin yana cakuɗe da wasu abubuwa da ba a tabbatar da faruwarsu ba. Don haka idan aka ce tarihihi, a taƙaice ana nufin gurɓataccen tarihi, wanda aka cakuɗe shi tsakanin gaskiya da ƙarya.

    Tarihihi labari ne na da ake riƙe da shi a kai, kuma kasancewar kai ba mariƙi ba ne, ballantana har ya yi ajiya, sai wajen ruwaito abubuwan da suka faru a rayuwa ake gwama su da waɗanda ba su faru ba. Wato dai yawancin tarihihi ya ƙunshi labarai ne na kunne-ya-girmi-kaka, waɗanda ba a iya tabbatar da abkuwarsu.

    Akwai tarihihi kala-kala a ƙasar Hausa, sai dai waɗanda suka yi tashe sun haɗa da na tarihihin zuwan Bayajidda ƙasar Hausa, da na sarkin Katsina Korau, da WaliƊanmarna, da WaliƊanmasani, ko naƊanwaire da sauran su.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga rubutaccen kundi mai taken: ADABIN KASUWAR KANO: Nazari da Sharhi Game da Ƙagaggun Labaran Hausa (1984-2008) wanda Bashir Abu Sabe 07/211111002 (M.A Hausa Studies) USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA ya wallafa.

    Domin karanta Al’adun Hausawa Na Jiya Da Na Yau danna nan

    Edita@rumasau-kallamu