-
-60%
Hausa Da Hausawa A Duniyar Intanet
0Original price was: ₦5,000.00.₦2,000.00Current price is: ₦2,000.00.Gabatarwa
X.1 Matashiya
Wannan littafin ya ɗauki intanet a matsayin “duniya” mai zaman kanta. A ciki (duniyar) akan tarar da duk waɗansu al’amura na yau da kullum suna gudana tamkar yadda suke kasancewa a duniyar zahiri. A duniyar intanet akan sami ɗaiɗaikun mutane (akawun-akawun da kafafen intanet na ɗaiɗaikun mutane). Akan kuma sami unguwanni (zauruka da kafafen intanet na tarayya). Ana kuma samun garuruwa da ƙasashe. Al’amuran da suke gudana a kowane daga cikin ɓangarorin sun kasance tamkar a duniya ta daban wadda ta kai ta dogara da kanta. A duniyar intanet, akan:
a. samu cinikayya da kasuwanci suna gudana tamkar yadda ake yi a duniyar zahiri ta mutane (kasuwanni da shaguna da dillalai da makamantansu);
b. samu zamantakewa da rayuwa mai kama da mafarki. Misali, ana iya samun tarayya tsakanin al’ummomi daga ɓangarorin duniya waɗanda ba su taɓa kallon juna a zahiri ba;
c. samu makarantu da azuzuwa har da ɗakunan karatu’
d. samu gine-gine da wurare da sauran abubuwan amfani masu matsayi kwatankwacin abubuwan amfanin bil’adama ta rayuwar zahiri.
Wato dai, al’amuran suna kasancewa cikin siga da salo makamanciyar yadda suke a duniyar zahiri. Akan kuma samu cuɗanya tsakanin al’amuran da suke wanzuwa a duniyoyin guda biyu. Daga duniyar zahiri ne ake samun damar cuɗanya da duniyar intanet ta hanyar na’urori. Wasu lokutan akan kai ga dawo da gudanarwar cuɗanyar zuwa duniyar zahiri. Misali, soyayyar duniyar intanet ta Isa Suleiman Fanshekara (ɗan Kano a Nijeriya) da Ba’amurkiya Janine Sanchez ta zama gaskiya. Don ƙarin bayani a duba BBC, (2020 para. 1)2 ko Abubakar, (2020 para. 1).
Babban al’amari kuma shi ne, akan rayu kuma a mutu a duniyar intanet. A rahoton da BBC ta fitar bayan bincike kan Fesbuk a shekarar 2016, ta bayyana kafar Fesbuk a matsayin wata babbar maƙabarta. Rahoton yana da taken: “Yadda Facebook ya zama makekiyar maƙabarta.” An tabbatar da cewa, shekaru takwas (8) kacal bayan buɗe Fesbuk, an samu masu amfani da kafar da suka mutu kimanin miliyan talatin (30,000,000). A bisa wannan, ana iya hasashen cewa ya zuwa yau adadin ya ninninka sau tarin yawa. Tun a shekarar 2012, adadin masu amfani da Fesbuk da suke mutuwa a kowace rana ya kai dubu takwas (8,000) (BBC, 2016 para. 1). Hakan yana nuni da cewa, adadin zai ci gaba da hauhawa yayin da ake samun ƙaruwar masu amfani da kafar.
Haƙiƙa akwai buƙatar a samu jakadu da wakilan Hausa da Hausawa a duniyar intanet, tamkar yadda ake da su a duniyar zahiri. Wannan littafi sharar fage ne da zai buɗe hanyar samar da wakilcin al’adun Hausa a duniyar ta intanet.
X.2 Madogaran Littafin
Wannan littafi ya taƙaita ne a kan al’adun Hausawa da intanet. Kadadarsa ba ta wuce duniyar intanet ba. Ko a duniyar intanet ɗin ba ko’ina aka duba ba. Littafin ya taƙaita a kafafen intanet na Hausa kawai. Dangane da sauran kafafen intanet, an yi ƙoƙarin duba al’adun Hausawa ne kawai daga cikinsu tare da nazartar irin tasirin da suka yi a kan al’adun Bahaushe. Ma’ana ke nan, an bibiyi kafafen domin ganin abin da suke faɗa ko suke nunawa dangane da al’adun Hausawa. An cim ma nasarar hakan ta hanyar:
i. nazartar rubuce-rubucen;
ii. nazartar hotuna;
iii. nazartar bidiyoyi; da
iv. nazartar alamomi.
Ba a iyakance adadin kafafen intanet da aka dubo waɗannan ba. Dalili kuwa shi ne, ya zuwa yau (2020), akwai kafafen intanet a duniya da adadinsu ya haura biliyan ɗaya da miliyan ɗari bakwai da hamsin da ɗaya da dubu talatin da ɗaya da ɗari huɗu da arba’in da bakwai (1,751,031,447) (Internet Live Stats, 2020 para. 2). Zaɓen wasu tsiraru daga cikin kafafen intanet ɗin na iya sa a tsallake wasu muhimman abubuwa da suka dace a yi magana a kansu. Hakan zai faru idan fitilar nazari ba ta haska kafafen intanet da suke ɗauke da waɗannan bayanai ba. A ɓangaren tasiri kuwa, za a yi ƙoƙarin gano irin gurbin kafafen na intanet ga rayuwar Bahaushe, musamman al’adunsa.
Dangane da waɗannan kafafen intanet na Hausa, an mayar da hankali ne a kan abin da ya shafi al’adu kawai. A cikin kafafen, za a yi ƙoƙarin zaƙulo al’adun Hausawa da suka shafi:
i. nazarin inda aka fito dangane da adanawa da yayata al’adun Hausawa a duniyar intanet;
ii. nazarin matsayin da al’adun Hausawa suka tsinci kansu a yau cikin waɗannan kafafen intanet na Hausa;
iii. nazarin matsaloli ko barazanar da al’adun Hausa suke fuskanta a duniyar intanet; da
iv. nazarin hanyoyi ko matakai da za a iya inganta kafafen.
X.3 Babukan Littafin
Wannan littafin yana ƙunshe da babuka guda biyar. Babi na ɗaya ya kasance shimfiɗa ne. A ciki an waiwaici samuwa da bunƙasar intanet. Bugu da ƙari, babin ya yi bitar kalmar ‘al’ada’ domin yin matashiya ga littafin. Bayan haka, babin ya dubi irin tasirin da intanet yake da shi a kan al’ummomi a duniya.
An gina babi na biyu a kan bunƙasar al’adun Hausawa a duniyar intanet. Babin ya duba manyan kafafen intanet a duniya da suka karɓi harshen Hausa. Daga cikinsu har da Fesbuk. Bugu da ƙari, babin ya kalli ire-iren tasirin da intanet yake da shi ga Hausa da kuma Hausawa.
Babi na uku ya mayar da hankali a kan nazarin yaɗuwar al’adun Hausawa a kan intanet. A ciki an duba yadda al’adun Hausawa daban-daban suka yaɗu a kan intanet. Sukan bayyana yayin da aka tura neman da yake da alaƙa da su a cikin injunan nema na kan intanet.
A cikin babi na huɗu, an nazarci amfani da aibun intanet ga Hausa da Hausawa. Ya tabbata cewa, intanet ya zo da alfanu masu tarin yawa waɗanda Hausa da Hausawa za su iya cin gajiyarsu musamman yayin da suka bi hanyoyin da suka kamata. Daga cikin amfaninsa akwai ba da damar sada zumunta da haɓaka Hausa da yayata ta. Yana kuma taimakawa wajen adana al’adun Hausawan. Aibin kafafen intanet ga al’ummar Hausawa sun haɗa da ɓata tarbiyya da ɓata lokaci da samar da kafar damfara da makamantansu. A ɓangare ɗaya kuwa, intanet ya zo da ƙalubale daban-daban waɗanda dole sai an bi kyawawan matakai domin kauce musu.
Babi na biyar ya tattauna nasarorin da kafafen intanet na Hausa suka samu a yau. Wannan ya haɗa da ƙaruwar ƙarfin tasirinsu a duniya da fannonin rayuwa da suka mamaye, ciki har da kasuwanci da ilimi. A ɓangare ɗaya kuwa, babin ya kawo wasu ƙalubale da kafafen suke fuskanta. Sun haɗa da ƙarancin tallafi da goyon baya daga masana da mahukunta da kuma wasu matsaloli da suka shafi yanayi da zamantakewar ƙasar Hausa. -
-20%
Hukuncin Dogara Da Hoto Da Vidieo A Murya A Kotun Sharia
0Original price was: ₦500.00.₦400.00Current price is: ₦400.00.Bayan haka, Allah Maɗaukakin Sarki ya sanya wannan addini ya dace da rayuwa
da juyawar halaye na ɗan Adam. Komai yana da hukuncinsa da matsayinsa a cikin
Shari’ar wannan addini. Saboda Allah Maɗaukaki shi ne ya halicci ɗan Adam kuma
shi ya saukar da Shari’ar (Al-A’raf:54; Al-Mulk:14). -
Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu
1₦400.00“A jikin ɗan Adam akwai gaɓoɓi ɗari uku da sittin (360) wajibi ya yi sadaka akan kowace gaba” sai suke ce wane ne zai iya wannan ya Manzon Allah? Sai ya ce: Binne Majina a Masallaci (Wato in ka ga wani ya yi kaki ya kwamɓala ta a masallaci ka binne ta) ko ka kawar da abu mai cutarwa daga hanya, in ba ka sami iko ba, raka’a biyu ta walaha ta wadatar”. (Abu Dawud 2/524).
-
-20%
Jagoran Noman Farin Wake a Najeriya
0Original price was: ₦500.00.₦400.00Current price is: ₦400.00.Wake muhimmin abinci ne wanda yake da matukar amfani a jikin mutane da
dabbobi, akwai manyan kasuwanni da ake saida wake kuma manoma suna sarrafa
harawar wake don sayarwa alokacin rani don samun kudin shiga da kimanin kashi
ashirin da biyar cikin dari (25%). -
-20%
Jagoran Noman Masara a Najeriya
0Original price was: ₦500.00.₦400.00Current price is: ₦400.00.Masara tana daya daga cikin amfanin gonar da akafi nomawa a Najeriya. Itace tafi
sauran amfanin gona yawan fadin kasa da ake nomata. Noman masara yana kara
bunkasa a Najeria sakamakon karuwar fasaha da dabarun noma. Masara itace abinci
mafi muhimmanci ga jama’a, dabbobi da masana’antu a Najeriya. -
-20%
Jagoran Noman Riɗi a Najeriya
0Original price was: ₦500.00.₦400.00Current price is: ₦400.00.Ridi yana daya daga cikin amfanin da ake nomawa domin samar da man girki a
duniya. Ya shigo Najeriya ne bayan yakin duniya na biyu. Sannan kuma ridi, ya
kasance amfani mai kawo kudi, sakamakon karuwar bukatan sa daga kasashen
waje. Ridi shine amfani mafi muhimmanci bayan gyada a cikin amfani gona masu
samar da mai a Najeriya. -
-20%
Jagoran Noman Shinkafa a Najeriya
0Original price was: ₦500.00.₦400.00Current price is: ₦400.00.Don samun kyakykyawar yabannya. Shinkafa na bukatar yanayi na zafi mai kimanin
ma’auni digri 20-400C .
Da rana shinkafa na bukatar yanayin zafi kimanin ma’aunin digri 30°C -
-20%
Jagoran Noman Waken Soya a Najeriya
0Original price was: ₦500.00.₦400.00Current price is: ₦400.00.Waken soya yana daga cikin amfanin gonar da aka dauka a matsayin abinci, wanda
ake shukawa kuma ake sarrafawa a kowace lahiya. -
-20%
Jagoran Noman Albasa A Najeriya
0Original price was: ₦500.00.₦400.00Current price is: ₦400.00.Albasa wata nau,in amfanin gona ne daga dangin kayan lambu, wacce ake nomawa
akusan ko ina a duniya. Tana girma mafi akasari a cikin kwanso wacce ake amfani da
ita a kusan ko wanne gida, a ko-da yaushe. -
-33%
JAKAR MAGORI
0Original price was: ₦600.00.₦400.00Current price is: ₦400.00.Wakar Dogaro ga Allah
Amshin ta:
Ina da Allah ba ni da raki
Komai gare Shi na ke maida shi
1.Bismillahi ya Rahmanu
Na fara da kiran sunan Shi
2.Na yi salati gun Manzon Shi
Shi ne ɗaha abin ƙaunar Shi
3.Don Ya ninkan salati goma
Ga-ni-ga-shi cikin fadar Shi -
-29%
KIMIYYA DA AL’AJABAN AL-QUR’ANI
0Original price was: ₦1,400.00.₦1,000.00Current price is: ₦1,000.00.Na rubuta wannan littafi Mai suna: “KIMIYYA DA AL’AJABAN AL-QUR’ANI” don na fitowa da masu karatu tarin abubuwan al’ajabai da suke tattare da al-ƙur’ani mai girma.
-
-20%
Ƙaidoji 16 Da Za Su Sa Unguwarku Ta Fi Sauran Unguwanni
0Original price was: ₦500.00.₦400.00Current price is: ₦400.00.Da sunan Allah Mai Rahama MaiJin kai. Tsira da aminci su tabbata ga Annabi
Muhammad (S.A.W) da alayensa da sahabbansa.