Description
Baiwa ta naƙaltar harshe da iya samarwa da sarrafa kalmomi a tsari da ɗabi’ar al’umma
hanya ce wadda take ba da dama a shirya waƙoƙi kuma a rera wa jama’a.
Mutum yakan zama makaɗi a lokacin da ya mallaki baiwa ta shirya kalmomi cikin saɗaru, sannan ya
kasance yakan tsara waƙoƙi lokaci bayan lokaci har al’umma ta gane ya iya waƙa, a san shi
da yin waƙa, kuma ya zama mai adani da kiyaye alfarmar waƙa, tare da ba waƙar kulawa da
kima a matsayinta na adabi mai shirya al’umma.
Reviews
There are no reviews yet.