-
-8%
TUMBUƊIN ZINARIYA
0Original price was: ₦650.00.₦600.00Current price is: ₦600.00.Littafi ne na yabon fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW
-
-17%
UWAR MIJI UWA CE
0Original price was: ₦600.00.₦500.00Current price is: ₦500.00.Shawarwari ga mace musulma akan yadda ya dace ta dauki mahaifiyar mijinta bisa koyarwar Addinnin Musulunci
-
-17%
Waiwaye Kan Harshen Makaɗi A Zubin Waƙar Baka
0Original price was: ₦600.00.₦500.00Current price is: ₦500.00.Baiwa ta naƙaltar harshe da iya samarwa da sarrafa kalmomi a tsari da ɗabi’ar al’umma
hanya ce wadda take ba da dama a shirya waƙoƙi kuma a rera wa jama’a. -
-60%
-
Wanene Bahaushe?
0₦400.00Littafi ne da ya ƙunshi tarihin Bahaushe tun asali, da yanayin yanda yake gudanar da rayuwarsa da zamantakewarsa kafin zuwan addini da kuma bayan zuwan addini.
-
-60%
Wasanni A Ƙasar Hausa
0Original price was: ₦5,000.00.₦2,000.00Current price is: ₦2,000.00.Wannan Littafi ya yi nasarar tattaro nau’ukan wasannin gargajiya har guda ɗari biyu da goma sha huɗu (214). An raba aikin zuwa babuka har guda tara. Babi na farko ya kasance shimfiɗa ga aikin. A ciki ne kuma aka kawo amfanin wasannin gargajiya. Daga ciki akwai: horo da gyaran hali, da koyar da jarumta, da koyar da hikima da dabara, da motsa jiki da dai makamantansu.
Babi na biyu ya waiwaici tsarin rayuwar Hausawa a jiya da kuma yau. Wannan ya haɗa da addininsu da kuma tsarin zamantakewa da auratayya. Hakan ya kasance ƙarin haske game da al’ummar da aka yi rubutun kansu. Wato dai tamkar fitila ce ta haska al’ummun da ake magana kansu domin a ji daɗin ɗaukar hoton zuci yayin da ake bayanin ire-iren wasanninsu.
A cikin babi na uku, an yi ƙoƙarin kawo nau’ukan wasannin gargajiyan Bahaushe. An yi hakan ne ta hanyar la’akari da alƙalumma daban-daban wurin raba wasannin. Waɗannan matakai sun haɗa da yanayin gudanar da wasannin, da lokacin gudanar da su, da masu gudanar da su da dai makamantansu. A ƙarƙashin kowane rukuni an kawo taƙaitaccen bayani mai gamsarwa tare da misalai domin ƙarin haske.Kamar dai yadda aka nuna a baya, zamani ya yi tasiri sannan yana ci gaba da yin tasiri kan wasannin gargajiya. Babi na huɗu ya waiwaici irin tasirin da zamanin ya yi kan wasannin. A cikin babin an nazarci dalilan da suka haifar da dusashewar wasannin gargajiyar Bahaushe. Sun haɗa da samuwar ilimin addini da na boko da samuwar yanar gizo da kafafen sadarwa na yanar gizo da dai sauransu. Sannan babin ya dubi irin sauye-sauye da aka samu ga wasu wasannin gargajiyar ta fuskar yadda ake gudanar da su. Daga ƙarshe kuma sai babin ya nazarci wasu sabbin wasannin gargajiya da Bahaushe ya tsinta a sakamakon Tasirin zamani a kan al’adunsa.
Daga babi na biyar kuwa, har zuwa na takwas, an kawo jerin wasanni ne tare da bayanin yadda ake gudanar da su. Babi na biyar na ɗauke da wasannin yara maza guda sittin da biyar (65) tare da bayanin kowanne. Babi na shida kuwa wasannin yara mata ya ƙunsa, guda ɗari da uku (103). Babi na bakwai kuwa ya ƙunshi wasanni ne na tarayya tsakanin yara maza da mata. Adadinsu ya kai talatin da shida (36). Sai kuma babi na takwas da ya ƙunshi wasannin manya, waɗanda adadinsu ya kasance bakwai (7) kacal.
Babi na ƙarshe kuwa, wato na tara, yana ƙunshe ne da jawaban kammalawa. Bayan an kawo jerin manazarta, sai kuma aka biyo baya da ratayen waɗannan wasannin Gargajiya guda ɗari biyu da goma sha huɗu (214) cikin tsararran jadawali. An yi hakan ne domin samar da haske ga mai karatu ko bincike, yadda zai samu bayanai masu muhimmanci kan kowane wasa kai tsaye. Ga kowane wasa, an bayyana abubuwa da suka haɗa da:
i. Sunan wasa
ii. Masu wasa
iii. Rukunin wasa
iv. Kayan aiki
v. Amfanin wasa
vi. Sakamakon wasa (Sakamako mai kyau yayin da aka yi abin ƙwarai, ko kuma mummunan sakamako yayin da aka ci karo da ƙa’idojin wasa) -
-60%
Wasannin Kwaikwayo Na Hausawa
0Original price was: ₦5,000.00.₦2,000.00Current price is: ₦2,000.00.Wannan littafi yana ɗauke da bayanai tare da misalan wasannin kwaikwayo na Hausawa. Yana ɗaya daga cikin littattafan da WAEC suka karɓa domin sakawa a makarantun sakandare.
-
-38%
ZATON WUTA A MAƘERA
2Original price was: ₦650.00.₦400.00Current price is: ₦400.00.Muna nan tsaye cirko-cirko da rana tsaka cikin jiran tsammani, idandunanmu bubbuɗe. Rana na ƙara zafi amma busawar iska da tsananin ɗoki ya sa ba mu ƙosa da tsaiwa cikin garjin ranar ba. Shitu ya haɗiye yawun da ke bakinsa a lokacin da ya ga ma’aikaciyar jinya ta tunkaro mu tana neman mai gidan Saratu.
-
-38%
ZOBEN ALƘAWARI
0Original price was: ₦650.00.₦400.00Current price is: ₦400.00.Wasu shekaru masu yawa a can baya da suka shuɗe.
Matsanancin gudu take ci iya ƙarfinta ko waiwayen baya ba ta yi, dafe da turtsetsen cikinta kamar an kifa ƙwarya, da ya hana ta samun damar yin gudun sosai.