Description
Wasu shekaru masu yawa a can baya da suka shuɗe.
Matsanancin gudu take ci iya ƙarfinta ko waiwayen baya ba ta yi, dafe da turtsetsen cikinta kamar an kifa ƙwarya, da ya hana ta samun damar yin gudun sosai. Iya gajiya ta gaji amma ba ta tsaya ba har sai da ta yi nisa cikin dajin sannan ta ji ƙafarta ta fara cijewa, kafin kuma ta riƙe ƙam ta hana ta cigaba da gudun. Dole ta ja ta tsaya, tana nishi kafin ta durƙushe a gurin tana cigaba da sauke numfashin gajiya a wahalce. Gumi ne ya soma karyo mata ta ko’ina, ya yin da ta ji mararta ta murɗa sosai, bayanta ya riƙe, ƙafa ma ta riƙe.
Reviews
There are no reviews yet.