Description
Wakar Dogaro ga Allah
Amshin ta:
Ina da Allah ba ni da raki
Komai gare Shi na ke maida shi
1.Bismillahi ya Rahmanu
Na fara da kiran sunan Shi
2.Na yi salati gun Manzon Shi
Shi ne ɗaha abin ƙaunar Shi
3.Don Ya ninkan salati goma
Ga-ni-ga-shi cikin fadar Shi
4.Tsira da Amincin Allah
Nan a gare shi da Alayen shi
5.Da Sahabbai da matayen shi
Da ma su bin su kan Shari’ar shi
Reviews
There are no reviews yet.