Description
A lokacin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wani sahabinsa ya yi sabon aure ya nemi izininsa don zuwa gida wajen iyalinsa, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce da shi: “Ɗauki makaminka ka tafi da shi don ina jiye maka tsoron cin karo da Yahudawa bani Ƙuraiza”.
Sai wannan sahabi ya ɗauki makaminsa ya tafi da shi, ko da ya isa ƙofar gidansa sai ya tarar da matarsa tsaye a ƙofar gida, nan take sai kishi ya kama shi inda ya nufi matarsa da mashinsa zai caka mata. Sai ta ce masa kar ka jefe ni da mashi, shiga gidan ka ga abin da ya fito da ni.
Sai ya shiga, da shigarsa sai ya ga wani shirgegen maciji nannade a kan shimfiɗa. sai ya yi kan macijin ya jefe shi da mashin, sannan ya kafe mashin a tsakar gidan ya fito. Can sai macijin ya motsa ya yiwo kansa, inda a sakamakon hakan ba a san wanda ya riga mutuwa ba a tsakaninsu”. Muslim ne ya rawaito shi. Hadisi Mai lamba (2236).
Rumasa’u Muhammad Kallamu –
All contents in this book have been posted.