Description
Ridi yana daya daga cikin amfanin da ake nomawa domin samar da man girki a
duniya. Ya shigo Najeriya ne bayan yakin duniya na biyu. Sannan kuma ridi, ya
kasance amfani mai kawo kudi, sakamakon karuwar bukatan sa daga kasashen
waje. Ridi shine amfani mafi muhimmanci bayan gyada a cikin amfani gona masu
samar da mai a Najeriya.
Noman ridi ya mamaye yankunan Arewa da tsakiyan Najeriya. Ada ridi karamin
amfani ne wajan samar da kudi ga manoma, amma a shekara ta 1974, lokacin ya
zamo amfani mai samar da kudin shiga ga juhohin arewa masu yawa, kamar su
Benue, Gombe, Kogi, Jigawa, Kano, Nasarawa, Katsina, Plateau da jihar Yobe
harma da Babban birnin taraiya Abuja
Reviews
There are no reviews yet.