-
DAMAKWARAƊIYYA
0₦400.00Wajibi ne mu sani cewa, abin da ake nufi da addini shi ne, tsarin rayuwa wanda Allah Mahalicci ya shimfiɗa wa bayinsa domin su tafiyar da rayuwarsu a kai. Ba kamar yadda mafi yawanmu muke dunƙule shi a cikin Salla Azumi zuwa Hajji, karatun Al-Ƙur’ani da zikiri ba. Dalilina a nan shi ne, yayin da Allah ya kammala saukar da al-Kur’ani, cewa ya yi ya kammala mana addininmu a gare mu.
-
-60%
Damfara A Duniyar Intanet
0Original price was: ₦5,000.00.₦2,000.00Current price is: ₦2,000.00.Gabatarwa
Damfara hanya ce ta amfani da dabarun yaudara don kwaɗaitar da wani samun wani abin alfanu dangin kuɗi ko wani abu mai daraja, domin karɓar wani abu daga gare shi na dindindin. A ɓangare guda kuwa, intanet fasaha ce ta zamani wadda ta ƙunshi haɗakar tsauraran al’amura da suka haɗa da yaruka da na’urori da sabis waɗanda haɗuwarsu take samar da al’amari ko bagire da yake tattare da hadahada da fannoni tamkar waɗanda suke duniyar yau-da-kullum, ciki har da abubuwan da suka shafi sadarwa da makarantu da bankuna da kasuwanni da shaguna tare da sauran halittu kamar mutane da dabbobi da waninsu.
Samuwa da bunƙasar intanet a duniya ya buɗe sabon babin damfara, wato damfara a duniyar intanet. Damfarar kan intanet ta fi shafar waɗanda suke hawa intanet ta hanyar kafafen intanet ko na sada zumunta ko kuma manhajoji. A yau, akan dama da Hausawa da dama a duniyar intanet dangane da kasuwanci da sada zumunta da sauran abubuwan da suka shafi tura bayanai ko amfani da su a kan intanet. Hakan ya sa Hausawan suka shiga cikin jerin waɗanda suke fuskantar ƙalubalen damfara a kan intanet. Wannan ya sa ya zama dole a gudanar da binciken da zai faɗakar da Hausawa game da matakan kare kai daga faɗawa tarkon ‘yan damfarar kan intanet.
Littafin yana ɗauke da babuka guda shida (6). Babi na farko ya fara da bayani dangane da ma’anar damfara. Daga nan ya kawo tsokaci game da ma’ana tare da taƙaitaccen tarihin samuwa da bunƙasar intanet. Babi na biyu kuwa ya mayar da hankali ne a kan tattauna batutuwan da suka shafi “neman kuɗi a kan intanet.” An fi mayar da hankali a kan nau’o’in kasuwanci da ƙwadagon kan intanet waɗanda suka shafi Hausawa. Babin ya bayyana cewa, masu gudanar da harkokin neman kuɗi a kan intanet sun fi fuskantar ƙalubalen damfara.
Babi na uku kuwa ya tattauna nau’o’in damfara ta kan intanet daban-daban. Fahimtar ciki da wajen waɗannan nau’o’in damfarar kan intanet wani muhimmin mataki ne na kare kai daga faɗawa tarkon ‘yan damfara. A babi na huɗu, an tattauna wasu misalan manyan damfarar kan intanet da aka yi wa Hausawa, waɗanda aka gudanar da su a cikin sigar kasuwanci. Hausawa masu yawa sun faɗa wannan tarkon damfara inda aka yaudare su da sunan kasuwanci. Nazartar wannan babi zai taimaka wa masu karatu, musamman Hausawa, wajen naƙaltar matakan tantance kasuwancin kan intanet na gaskiya da na bogi
Babi na biyar ya tattauna wasu fitattun misalan damfarar kan intanet da suka ritsa da Hausawa ta sigar kasuwancin kuɗin intanet (kirifto). An yaudari Hausawa masu yawa da wasu nau’o’in kirifto na damfara. Sun haɗa da Insknation da Telegram P2P da AI Mining da sauran makamantansu. Bayanan da suke cikin wannan babin za su taimaka wa makaranta musamman Hausawa wajen bambance aya da tsakuwa, tsakanin harkokin kirifto na gaskiya da na damfara.
Babi na shida ya kawo wasu muhamman dabarun kare kai daga faɗawa cikin tarkon ‘yan damfara a kan intanet. Dabarun sun haɗa da bayanai game da yadda ake gane saƙonnin damfara da kafafen intanet na bogi. Haka kuma, sun shafi bayani game da muhimman matakai da ya kamata mutum ya ɗauka domin kare akawun ɗinsa daga barazanar ‘yan damfara. Akawun ɗin yana iya kasancewa na kafafen intanet (websites da blogs) da manhajoji (applications) da kuma kafafen sada zumunta (social media).
Muna da yaƙinin cewa, wannan littafin zai yi matuƙar taimakawa wajen fahimtar damfarar kan intanet da nau’o’inta da ma matakan kare kai daga wannan annoba ta damfara a kan intanet. -
Duhun Kai Gaba Da Kishiya
1₦400.00Wannan littafi ya yi bayani game da kishi da asalinsa da yadda ake yin sa a musulunci, tare da kawo misalai daga ayoyi da hadisan manzon Allah S.A.W. Haka kuma ya koyar da yanda ya kamata ya kamata mata su kasance suna gudanar da kishin a tsakaninsu.
-
Ɗan Adam Kamar Yadda Allah Ke Son Shi
1₦400.00Wannan ɗan littafi “Ɗan Adam kamar yadda Allah yake sonsa” na fara buga shi ne tun a shekarar 1997, wato yanzu (2007) shekaru goma ke nan. Kuma a wancan lokaci na fara rubuta shi bayan na gama jami’a da shekara ɗaya, wato akwai ragowar tasirin rayuwar jami’a da ruhinta ke nan.
-
-67%
FASIHIYA BINTA LABARAN (Fati Nijar Da Waƙoƙinta)
0Original price was: ₦6,000.00.₦2,000.00Current price is: ₦2,000.00.“… contributes significantly to the field and will undoubtedly be a valuable resource for researchers, scholars, and students, particularly those focused on oral literature studies.” Dr. M. Grema (YSU)
“Babu shakka sun yi abin a yaba.” Dr. Adamu Rabi’u Bakura (FUGUS)
“… makes the book not only an educational resource but also a catalyst for broader discussions on gender and cultural diversity in the arts.” Dr. D.B. Bunza (UDUS)
“Su kuma ɗaliban adabi, sun samu abin karantawa.” Mal. I. Sheme (NOUN)
“Madallah da tunanin waɗanda duk ke da hannu a wannan kyakkyawan yunƙuri na wannan littafi da aka yi shi a bisa cancanta don amfani ga makaranta da ita kanta Zabiyar Bargu. ALAN Waƙa (Sarkin Ɗiyan Gobir)
-
GASKIYAR MAGANA A KAN ASHURA
1₦400.00Babu wani abu da Manzon Allah (S.A.W) ya yi umarni a yi, ko ya yi, aka yi, bai ce komai ba a ranar Ashura sai azumi ya yi, ya yi umarni a yi, ya faɗi falalarsa, ya yi nuni ga falalar yin azumin ranar tara ga watan wato Tasu’a. Wannan shi ne kaɗai abin da ya inganta daga gare shi da sahabbansa da tabi’ai cikin su har da Imaman Ahlulbaiti.
-
-37%
GOGAYYAR RAYUWA
0Original price was: ₦630.00.₦400.00Current price is: ₦400.00.Magidanta masu aiki ko kuma sana’a a nesa da inda iyalinsu suke rayuwa, mafi yawancinsu bayan sun yi ritayar aiki ko kuma wani dalili ya sa su dawowa cikin iyalinsu da rayuwa, to suna fuskantar matsalar rashin jituwa
-
Guziri Ga Mai Azumin Ramadana
1₦400.00Wannan Littafi gudummawa ce babba ga ƙoramar ilimi, domin Littafin ya dogara ne a kan littattafai, sharhohi da kuma bayanai daga malamai masu nagarta da jajircewa a kan koyarwar Alƙur’ani da Sunnah.
-
-8%
GUZIRI GA MAI AZUMIN WATAN RAMADAN
0Original price was: ₦650.00.₦600.00Current price is: ₦600.00.Littafi ne da ke magana a kan Azumi da hukunce-hukuncensa.
-
-
-13%
HADISAI 100 DOMIN HADDA
0Original price was: ₦400.00.₦350.00Current price is: ₦350.00.Wannan littafi ne ga masu sha`awar haddace ingantattun hadisan Manzon Allah (S.A.W).
-
Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali
1₦400.00A cikin wannan ɗan littafi an yi ƙoƙarin bayyana ma’anar zaman lafiya da kwanciyar hankali, ruɗanin mutane game da zaman lafiya da kwanciyar hankali, abubuwan da suke hana zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma abubuwa na gaskiya waɗanda suke kawo shi. Sannan an kawo ƙa’idojin zaman lafiya da dukkan nau’in mutane, da kuma waɗansu ƙa’idojin na zaman lafiya da iyali. Daga ƙarshe an kawo maganin farin jini da mallaka domin amfanin ƴan uwa.