Description
A ranar Ashura ta shekara ta sittin da ɗaya daga hijira, an yi mugun aiki mai tada hankali da tsananin ban tausayi, shi ne kashe Husaini (R.A) Jikan shugaban halitta, ɗan shugabar matan Aljanna, tsokar Manzon Allah (S.A.W) a Karbala da shi da iyalansa da wasu daga cikin mabiyansa. Wannan bala’i ne da babu abin da mai imani zai yi in ya tuna sai dai ya ce Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
Babu wani abu da Manzon Allah (S.A.W) ya yi umarni a yi, ko ya yi, aka yi, bai ce komai ba a ranar Ashura sai azumi ya yi, ya yi umarni a yi, ya faɗi falalarsa, ya yi nuni ga falalar yin azumin ranar tara ga watan wato Tasu’a. Wannan shi ne kaɗai abin da ya inganta daga gare shi da sahabbansa da tabi’ai cikin su har da Imaman Ahlulbaiti.
Rumasa’u Muhammad Kallamu –
All contents in this book have been posted.