Availability: In Stock
Damfara A Duniyar Intanet
₦5,000.00 Original price was: ₦5,000.00.₦2,000.00Current price is: ₦2,000.00.
Gabatarwa
Damfara hanya ce ta amfani da dabarun yaudara don kwaɗaitar da wani samun wani abin alfanu dangin kuɗi ko wani abu mai daraja, domin karɓar wani abu daga gare shi na dindindin. A ɓangare guda kuwa, intanet fasaha ce ta zamani wadda ta ƙunshi haɗakar tsauraran al’amura da suka haɗa da yaruka da na’urori da sabis waɗanda haɗuwarsu take samar da al’amari ko bagire da yake tattare da hadahada da fannoni tamkar waɗanda suke duniyar yau-da-kullum, ciki har da abubuwan da suka shafi sadarwa da makarantu da bankuna da kasuwanni da shaguna tare da sauran halittu kamar mutane da dabbobi da waninsu.
Samuwa da bunƙasar intanet a duniya ya buɗe sabon babin damfara, wato damfara a duniyar intanet. Damfarar kan intanet ta fi shafar waɗanda suke hawa intanet ta hanyar kafafen intanet ko na sada zumunta ko kuma manhajoji. A yau, akan dama da Hausawa da dama a duniyar intanet dangane da kasuwanci da sada zumunta da sauran abubuwan da suka shafi tura bayanai ko amfani da su a kan intanet. Hakan ya sa Hausawan suka shiga cikin jerin waɗanda suke fuskantar ƙalubalen damfara a kan intanet. Wannan ya sa ya zama dole a gudanar da binciken da zai faɗakar da Hausawa game da matakan kare kai daga faɗawa tarkon ‘yan damfarar kan intanet.
Littafin yana ɗauke da babuka guda shida (6). Babi na farko ya fara da bayani dangane da ma’anar damfara. Daga nan ya kawo tsokaci game da ma’ana tare da taƙaitaccen tarihin samuwa da bunƙasar intanet. Babi na biyu kuwa ya mayar da hankali ne a kan tattauna batutuwan da suka shafi “neman kuɗi a kan intanet.” An fi mayar da hankali a kan nau’o’in kasuwanci da ƙwadagon kan intanet waɗanda suka shafi Hausawa. Babin ya bayyana cewa, masu gudanar da harkokin neman kuɗi a kan intanet sun fi fuskantar ƙalubalen damfara.
Babi na uku kuwa ya tattauna nau’o’in damfara ta kan intanet daban-daban. Fahimtar ciki da wajen waɗannan nau’o’in damfarar kan intanet wani muhimmin mataki ne na kare kai daga faɗawa tarkon ‘yan damfara. A babi na huɗu, an tattauna wasu misalan manyan damfarar kan intanet da aka yi wa Hausawa, waɗanda aka gudanar da su a cikin sigar kasuwanci. Hausawa masu yawa sun faɗa wannan tarkon damfara inda aka yaudare su da sunan kasuwanci. Nazartar wannan babi zai taimaka wa masu karatu, musamman Hausawa, wajen naƙaltar matakan tantance kasuwancin kan intanet na gaskiya da na bogi
Babi na biyar ya tattauna wasu fitattun misalan damfarar kan intanet da suka ritsa da Hausawa ta sigar kasuwancin kuɗin intanet (kirifto). An yaudari Hausawa masu yawa da wasu nau’o’in kirifto na damfara. Sun haɗa da Insknation da Telegram P2P da AI Mining da sauran makamantansu. Bayanan da suke cikin wannan babin za su taimaka wa makaranta musamman Hausawa wajen bambance aya da tsakuwa, tsakanin harkokin kirifto na gaskiya da na damfara.
Babi na shida ya kawo wasu muhamman dabarun kare kai daga faɗawa cikin tarkon ‘yan damfara a kan intanet. Dabarun sun haɗa da bayanai game da yadda ake gane saƙonnin damfara da kafafen intanet na bogi. Haka kuma, sun shafi bayani game da muhimman matakai da ya kamata mutum ya ɗauka domin kare akawun ɗinsa daga barazanar ‘yan damfara. Akawun ɗin yana iya kasancewa na kafafen intanet (websites da blogs) da manhajoji (applications) da kuma kafafen sada zumunta (social media).
Muna da yaƙinin cewa, wannan littafin zai yi matuƙar taimakawa wajen fahimtar damfarar kan intanet da nau’o’inta da ma matakan kare kai daga wannan annoba ta damfara a kan intanet.
Reviews
There are no reviews yet.