Description
Wannan littafi mai suna Ajiyar Zuciya da Mallam Aminu Isma’il Sagagi ya rubuta, ya ƙunshi waƙoƙi guda Arba’in a kan al’amura daban-daban. Abubuwan da suka sosa zuciyar marubucin da waɗanda suka ƙayatar da shi a kimanin shekaru Ashirin da suka wuce ne suka kai shi ga rubuta su, domin ya bayyana wa duniya irin ɗanɗanon da zuciyarsa ta samu daga waɗannan al’amura, a cikin wannan bayani da aka yi ta sigar waƙa. Marubucin ya isar da saƙonni da darussa masu kyau ga duk wanda ya karanta littafin. A bisa misali, waƙar “Shari’ar Musulinci Kaɗai ce Magani”, da ta “Shiriyarmu Tana Alkur’ani” cike suke da saƙonni masu ma’ana.
Reviews
There are no reviews yet.