Availability: In Stock

Ɗan Adam Kamar Yadda Allah Ke Son Shi

400.00

Wannan ɗan littafi “Ɗan Adam kamar yadda Allah yake sonsa” na fara buga shi ne tun a shekarar 1997, wato yanzu (2007) shekaru goma ke nan. Kuma a wancan lokaci na fara rubuta shi bayan na gama jami’a da shekara ɗaya, wato akwai ragowar tasirin rayuwar jami’a da ruhinta ke nan. 

Already sold: 0/1000

Description

Babban abin da aka san dabbobi da shi; shi ne rashin hankali irin na mutane, kuma da rashin iya sarrafa al’amura bisa cikakken zaɓi na turanci da ilimi, duk da yake ana samun wasu dabbobi masu baiwa ta hazaƙa a wasu fannonin rayuwa iri iri, amma duk da haka matsayinsu ƙasa ya ke da na mutane saboda cikakken hankali da Allah ya ba su tare da wahayi ta hanyar Manzanni, abin da ka iya jagorantarsu su bi tafarkin shiriya tsantsa. 

Dabbobi ba su da wata manufa ta musamman da suke iya zaɓawa kansu a rayuwa, mafi muhimmancin abin da ke gabansu shi ne ci da sha da Barbara. 

Lallai ne mutum ya ɗinga faɗaka daga al’amuransa na yau da gobe, domin ya tabbata yana tafiyar da su akan tafarkin Imani da kuma aiki da hankali, domin idan ya sake ya zama shima ba shi da manufa sai dai ci da sha da sauransu. To sai ya fi dabbobi lalacewa.

1 review for Ɗan Adam Kamar Yadda Allah Ke Son Shi

  1. Rumasa’u Muhammad Kallamu

    All contents in this book have been posted.

Add a review

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Vendor Information

  • Store Name: Sagagi
  • Vendor: Sagagi
  • Address: Sagagi
    Kano
    Kano
  • No ratings found yet!