Wannan littafi mai suna Ajiyar Zuciya da Mallam Aminu Isma’il Sagagi ya rubuta, ya ƙunshi waƙoƙi guda Arba’in a kan al’amura daban-daban. Abubuwan da suka sosa zuciyar marubucin da waɗanda suka ƙayatar da shi a kimanin shekaru Ashirin da suka wuce ne suka kai shi ga rubuta su, domin ya bayyana wa duniya irin ɗanɗanon da zuciyarsa ta samu daga waɗannan al’amura, a cikin wannan bayani da aka yi ta sigar waƙa.