Availability: In Stock

Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

400.00

A cikin wannan ɗan littafi an yi ƙoƙarin bayyana ma’anar zaman lafiya da kwanciyar hankali, ruɗanin mutane game da zaman lafiya da kwanciyar hankali, abubuwan da suke hana zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma abubuwa na gaskiya waɗanda suke kawo shi. Sannan an kawo ƙa’idojin zaman lafiya da dukkan nau’in mutane, da kuma waɗansu ƙa’idojin na zaman lafiya da iyali. Daga ƙarshe an kawo maganin farin jini da mallaka domin amfanin ƴan uwa. 

Description

Saɓo da mugunta su ne abubuwa masu daraja ta biyu da suke fatattakar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan abu a fili yake, saboda duk wani mai saɓon Allah cike yake da ɓacin rai, tsoro da rashin kwanciyar hankali. 

Misali mazinaci yana cike da tsoro da firgita don kada a gan shi, kuma yana gamawa sai wani irin mummunan ɓacin rai ya turniƙe shi. To ka auna halin da ɓarayi, ‘yan fashi, manema maza da sauran masu saɓo suke ciki. Su da kansu sun san babu zaman lafiya da kwanciyar hankali a tare da su. 

1 review for Hanyoyin Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali

  1. Rumasa’u Muhammad Kallamu

    All contents in this book have been posted.

Add a review

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Vendor Information

  • No ratings found yet!