Description
Yadda za a haɗa;
A samu fulawa a tankaɗe ta, a zuba a mazubi mai tsafta, a juye margarine a guggutsira shi a cikin fulawa, sai a cakuɗa ta, a barbaɗa hoda da maggi a cikin fulawa ko ina ya ji.
A fasa ƙwai a zuba a cakuɗa gabaki ɗaya ta haɗu sannan a kawo ruwa a dinga zubawa da kaɗan da kaɗan har ta haɗe jikinta, sai a rufe ta, ta yi minti 30.
Sai a ɗauko niƙaƙƙen naman, a zuba mai a kasko madaidaici, ya ɗan yi zafi kaɗan kafin a sa naman, sai a kawo albasa da attaruhu da aka jajjaga a kawo maggi da kayan ƙamshi kaɗan, a dinga juya naman ,har sai ya soyu.
Rumasa’u Muhammad Kallamu –
All contents in this book have been posted.