-
A KULA DA LAFIYA
2Haƙiƙa sanin cutar da take tare da mara lafiya da kuma tantance wata cuta daga wata, itace ƙwaƙƙwarar makamar shawo kan cuta da gano sahihin maganinta. Don haka farkon abin da ya kamaci mai bayar da magani shi ne, ya yi ƙoƙarin gano cutar da take tare da mara lafiyar da zai ba wa magani, sannan kuma sai ya bayar da maganin da ya dace da ita cutar da ya gano.
-
-37%
BAKANDAMIYAR SARKINFADA
0AMSHIN WAƘOƘI
(Bakandamiya, Mala’ikun Ubangji, Littattafan Ubangiji, Manzannin Ubangiji,
Kaddarar Ubangiji, Ni’imomin Ubangiji, Sharrin Zuciya, Nasiha da Kammalawa) -
DAMAKWARAƊIYYA
0Wajibi ne mu sani cewa, abin da ake nufi da addini shi ne, tsarin rayuwa wanda Allah Mahalicci ya shimfiɗa wa bayinsa domin su tafiyar da rayuwarsu a kai. Ba kamar yadda mafi yawanmu muke dunƙule shi a cikin Salla Azumi zuwa Hajji, karatun Al-Ƙur’ani da zikiri ba. Dalilina a nan shi ne, yayin da Allah ya kammala saukar da al-Kur’ani, cewa ya yi ya kammala mana addininmu a gare mu.
-
Duhun Kai Gaba Da Kishiya
1Wannan littafi ya yi bayani game da kishi da asalinsa da yadda ake yin sa a musulunci, tare da kawo misalai daga ayoyi da hadisan manzon Allah S.A.W. Haka kuma ya koyar da yanda ya kamata ya kamata mata su kasance suna gudanar da kishin a tsakaninsu.
-
GASKIYAR MAGANA A KAN ASHURA
1Babu wani abu da Manzon Allah (S.A.W) ya yi umarni a yi, ko ya yi, aka yi, bai ce komai ba a ranar Ashura sai azumi ya yi, ya yi umarni a yi, ya faɗi falalarsa, ya yi nuni ga falalar yin azumin ranar tara ga watan wato Tasu’a. Wannan shi ne kaɗai abin da ya inganta daga gare shi da sahabbansa da tabi’ai cikin su har da Imaman Ahlulbaiti.
-
-29%
KIMIYYA DA AL’AJABAN AL-QUR’ANI
0Na rubuta wannan littafi Mai suna: “KIMIYYA DA AL’AJABAN AL-QUR’ANI” don na fitowa da masu karatu tarin abubuwan al’ajabai da suke tattare da al-ƙur’ani mai girma.
-
-38%
-
SAHIHIN SIRRIN IZA JA’A
1Iza ja’a (Suratun Nasri), ita ce sura ta (110) a jerin surorin Alƙur’ani mai girma guda ɗari da sha huɗu (114), kuma tana ɗaya daga cikin surorin da aka saukar a Madina, sannan kuma ayoyinta uku ne. Ga su kamar haka:
-
SAHIHIN SIRRIN ƘULHUWALLAHU AHAD
0Suratul Ikhlas ita ce sura ta (112) a jerin surorin alƙur’ani mai girma. A wasu lokutan ana kiran ta da Ƙulhuwallahu Ahad, wato ana ambaton ta da ayar farko da ta fara da ita.
-
-
Wanene Bahaushe?
0Littafi ne da ya ƙunshi tarihin Bahaushe tun asali, da yanayin yanda yake gudanar da rayuwarsa da zamantakewarsa kafin zuwan addini da kuma bayan zuwan addini.