-
-38%
ZATON WUTA A MAƘERA
2Muna nan tsaye cirko-cirko da rana tsaka cikin jiran tsammani, idandunanmu bubbuɗe. Rana na ƙara zafi amma busawar iska da tsananin ɗoki ya sa ba mu ƙosa da tsaiwa cikin garjin ranar ba. Shitu ya haɗiye yawun da ke bakinsa a lokacin da ya ga ma’aikaciyar jinya ta tunkaro mu tana neman mai gidan Saratu.