Description
Wanda aka matse a sahu, ya kasa ruku’u, har liman ya ɗago daga ruku’un, ya tafi sujjada; tom, idan mamu zai iya riskar liman a sujjada ta biyu (2), to sai ya yi ruku’un, ya yi ƙoƙarin ya riske shi a sujjada ta biyu. Idan kuma mamu ba zai iya samun liman a sujjada ta biyu ba, sai ya jefar da raka’ar, ya rama ta bayan liman ya sallame, kuma babu sujjada a kansa.
Idan kuma a sujjada ne aka matse mamu, sai ya yi ƙoƙarin yin sujjadar da bai yi da liman ba kafin liman ya ƙulla wata raka’ar (ma’ana a yi ruku’u). Idan har liman ya kai ga yin ruku’u na wata raka’ar, nan ma mamu zai jefar da raka’ar, ya rama raka’ar bayan liman ya sallame sallah, shi ma babu sujjada a kansa.
Rumasa’u Muhammad Kallamu –
All contents in this book have been posted.