• A KULA DA LAFIYA

    A KULA DA LAFIYA

    2

    Haƙiƙa sanin cutar da take tare da mara lafiya da kuma tantance wata cuta daga wata, itace ƙwaƙƙwarar makamar shawo kan cuta da gano sahihin maganinta. Don haka farkon abin da ya kamaci mai bayar da magani shi ne, ya yi ƙoƙarin gano cutar da take tare da mara lafiyar da zai ba wa magani, sannan kuma sai ya bayar da maganin da ya dace da ita cutar da ya gano.

    400.00
    Add to cart
  • -38% BINCIKE

    BINCIKE

    0

    Da sannu a hankali cikin nutsuwa da ƙasaita, wata kyakkyawar sutaleliyar  budurwa mai matsakaicin tsaho siririya fara ƙal, fuskarta ta yalwatu da gashin  gira baƙin ƙirin da kuma gashin ido dogaye baƙaƙe kamar sala-salan yankan  lemo

    Original price was: ₦650.00.Current price is: ₦400.00.
    Add to cart
  • -60% Damfara A Duniyar Intanet

    Damfara A Duniyar Intanet

    0

    Gabatarwa
    Damfara hanya ce ta amfani da dabarun yaudara don kwaɗaitar da wani samun wani abin alfanu dangin kuɗi ko wani abu mai daraja, domin karɓar wani abu daga gare shi na dindindin. A ɓangare guda kuwa, intanet fasaha ce ta zamani wadda ta ƙunshi haɗakar tsauraran al’amura da suka haɗa da yaruka da na’urori da sabis waɗanda haɗuwarsu take samar da al’amari ko bagire da yake tattare da hadahada da fannoni tamkar waɗanda suke duniyar yau-da-kullum, ciki har da abubuwan da suka shafi sadarwa da makarantu da bankuna da kasuwanni da shaguna tare da sauran halittu kamar mutane da dabbobi da waninsu.
    Samuwa da bunƙasar intanet a duniya ya buɗe sabon babin damfara, wato damfara a duniyar intanet. Damfarar kan intanet ta fi shafar waɗanda suke hawa intanet ta hanyar kafafen intanet ko na sada zumunta ko kuma manhajoji. A yau, akan dama da Hausawa da dama a duniyar intanet dangane da kasuwanci da sada zumunta da sauran abubuwan da suka shafi tura bayanai ko amfani da su a kan intanet. Hakan ya sa Hausawan suka shiga cikin jerin waɗanda suke fuskantar ƙalubalen damfara a kan intanet. Wannan ya sa ya zama dole a gudanar da binciken da zai faɗakar da Hausawa game da matakan kare kai daga faɗawa tarkon ‘yan damfarar kan intanet.
    Littafin yana ɗauke da babuka guda shida (6). Babi na farko ya fara da bayani dangane da ma’anar damfara. Daga nan ya kawo tsokaci game da ma’ana tare da taƙaitaccen tarihin samuwa da bunƙasar intanet. Babi na biyu kuwa ya mayar da hankali ne a kan tattauna batutuwan da suka shafi “neman kuɗi a kan intanet.” An fi mayar da hankali a kan nau’o’in kasuwanci da ƙwadagon kan intanet waɗanda suka shafi Hausawa. Babin ya bayyana cewa, masu gudanar da harkokin neman kuɗi a kan intanet sun fi fuskantar ƙalubalen damfara.
    Babi na uku kuwa ya tattauna nau’o’in damfara ta kan intanet daban-daban. Fahimtar ciki da wajen waɗannan nau’o’in damfarar kan intanet wani muhimmin mataki ne na kare kai daga faɗawa tarkon ‘yan damfara. A babi na huɗu, an tattauna wasu misalan manyan damfarar kan intanet da aka yi wa Hausawa, waɗanda aka gudanar da su a cikin sigar kasuwanci. Hausawa masu yawa sun faɗa wannan tarkon damfara inda aka yaudare su da sunan kasuwanci. Nazartar wannan babi zai taimaka wa masu karatu, musamman Hausawa, wajen naƙaltar matakan tantance kasuwancin kan intanet na gaskiya da na bogi
    Babi na biyar ya tattauna wasu fitattun misalan damfarar kan intanet da suka ritsa da Hausawa ta sigar kasuwancin kuɗin intanet (kirifto). An yaudari Hausawa masu yawa da wasu nau’o’in kirifto na damfara. Sun haɗa da Insknation da Telegram P2P da AI Mining da sauran makamantansu. Bayanan da suke cikin wannan babin za su taimaka wa makaranta musamman Hausawa wajen bambance aya da tsakuwa, tsakanin harkokin kirifto na gaskiya da na damfara.
    Babi na shida ya kawo wasu muhamman dabarun kare kai daga faɗawa cikin tarkon ‘yan damfara a kan intanet. Dabarun sun haɗa da bayanai game da yadda ake gane saƙonnin damfara da kafafen intanet na bogi. Haka kuma, sun shafi bayani game da muhimman matakai da ya kamata mutum ya ɗauka domin kare akawun ɗinsa daga barazanar ‘yan damfara. Akawun ɗin yana iya kasancewa na kafafen intanet (websites da blogs) da manhajoji (applications) da kuma kafafen sada zumunta (social media).
    Muna da yaƙinin cewa, wannan littafin zai yi matuƙar taimakawa wajen fahimtar damfarar kan intanet da nau’o’inta da ma matakan kare kai daga wannan annoba ta damfara a kan intanet.

    Original price was: ₦5,000.00.Current price is: ₦2,000.00.
    Add to cart
  • -60% Hausa Da Hausawa A Duniyar Intanet

    Hausa Da Hausawa A Duniyar Intanet

    0

    Gabatarwa
    X.1 Matashiya
    Wannan littafin ya ɗauki intanet a matsayin “duniya” mai zaman kanta. A ciki (duniyar) akan tarar da duk waɗansu al’amura na yau da kullum suna gudana tamkar yadda suke kasancewa a duniyar zahiri. A duniyar intanet akan sami ɗaiɗaikun mutane (akawun-akawun da kafafen intanet na ɗaiɗaikun mutane). Akan kuma sami unguwanni (zauruka da kafafen intanet na tarayya). Ana kuma samun garuruwa da ƙasashe. Al’amuran da suke gudana a kowane daga cikin ɓangarorin sun kasance tamkar a duniya ta daban wadda ta kai ta dogara da kanta. A duniyar intanet, akan:
    a. samu cinikayya da kasuwanci suna gudana tamkar yadda ake yi a duniyar zahiri ta mutane (kasuwanni da shaguna da dillalai da makamantansu);
    b. samu zamantakewa da rayuwa mai kama da mafarki. Misali, ana iya samun tarayya tsakanin al’ummomi daga ɓangarorin duniya waɗanda ba su taɓa kallon juna a zahiri ba;
    c. samu makarantu da azuzuwa har da ɗakunan karatu’
    d. samu gine-gine da wurare da sauran abubuwan amfani masu matsayi kwatankwacin abubuwan amfanin bil’adama ta rayuwar zahiri.
    Wato dai, al’amuran suna kasancewa cikin siga da salo makamanciyar yadda suke a duniyar zahiri. Akan kuma samu cuɗanya tsakanin al’amuran da suke wanzuwa a duniyoyin guda biyu. Daga duniyar zahiri ne ake samun damar cuɗanya da duniyar intanet ta hanyar na’urori. Wasu lokutan akan kai ga dawo da gudanarwar cuɗanyar zuwa duniyar zahiri. Misali, soyayyar duniyar intanet ta Isa Suleiman Fanshekara (ɗan Kano a Nijeriya) da Ba’amurkiya Janine Sanchez ta zama gaskiya. Don ƙarin bayani a duba BBC, (2020 para. 1)2 ko Abubakar, (2020 para. 1).
    Babban al’amari kuma shi ne, akan rayu kuma a mutu a duniyar intanet. A rahoton da BBC ta fitar bayan bincike kan Fesbuk a shekarar 2016, ta bayyana kafar Fesbuk a matsayin wata babbar maƙabarta. Rahoton yana da taken: “Yadda Facebook ya zama makekiyar maƙabarta.” An tabbatar da cewa, shekaru takwas (8) kacal bayan buɗe Fesbuk, an samu masu amfani da kafar da suka mutu kimanin miliyan talatin (30,000,000). A bisa wannan, ana iya hasashen cewa ya zuwa yau adadin ya ninninka sau tarin yawa. Tun a shekarar 2012, adadin masu amfani da Fesbuk da suke mutuwa a kowace rana ya kai dubu takwas (8,000) (BBC, 2016 para. 1). Hakan yana nuni da cewa, adadin zai ci gaba da hauhawa yayin da ake samun ƙaruwar masu amfani da kafar.
    Haƙiƙa akwai buƙatar a samu jakadu da wakilan Hausa da Hausawa a duniyar intanet, tamkar yadda ake da su a duniyar zahiri. Wannan littafi sharar fage ne da zai buɗe hanyar samar da wakilcin al’adun Hausa a duniyar ta intanet.
    X.2 Madogaran Littafin
    Wannan littafi ya taƙaita ne a kan al’adun Hausawa da intanet. Kadadarsa ba ta wuce duniyar intanet ba. Ko a duniyar intanet ɗin ba ko’ina aka duba ba. Littafin ya taƙaita a kafafen intanet na Hausa kawai. Dangane da sauran kafafen intanet, an yi ƙoƙarin duba al’adun Hausawa ne kawai daga cikinsu tare da nazartar irin tasirin da suka yi a kan al’adun Bahaushe. Ma’ana ke nan, an bibiyi kafafen domin ganin abin da suke faɗa ko suke nunawa dangane da al’adun Hausawa. An cim ma nasarar hakan ta hanyar:
    i. nazartar rubuce-rubucen;
    ii. nazartar hotuna;
    iii. nazartar bidiyoyi; da
    iv. nazartar alamomi.
    Ba a iyakance adadin kafafen intanet da aka dubo waɗannan ba. Dalili kuwa shi ne, ya zuwa yau (2020), akwai kafafen intanet a duniya da adadinsu ya haura biliyan ɗaya da miliyan ɗari bakwai da hamsin da ɗaya da dubu talatin da ɗaya da ɗari huɗu da arba’in da bakwai (1,751,031,447) (Internet Live Stats, 2020 para. 2). Zaɓen wasu tsiraru daga cikin kafafen intanet ɗin na iya sa a tsallake wasu muhimman abubuwa da suka dace a yi magana a kansu. Hakan zai faru idan fitilar nazari ba ta haska kafafen intanet da suke ɗauke da waɗannan bayanai ba. A ɓangaren tasiri kuwa, za a yi ƙoƙarin gano irin gurbin kafafen na intanet ga rayuwar Bahaushe, musamman al’adunsa.
    Dangane da waɗannan kafafen intanet na Hausa, an mayar da hankali ne a kan abin da ya shafi al’adu kawai. A cikin kafafen, za a yi ƙoƙarin zaƙulo al’adun Hausawa da suka shafi:
    i. nazarin inda aka fito dangane da adanawa da yayata al’adun Hausawa a duniyar intanet;
    ii. nazarin matsayin da al’adun Hausawa suka tsinci kansu a yau cikin waɗannan kafafen intanet na Hausa;
    iii. nazarin matsaloli ko barazanar da al’adun Hausa suke fuskanta a duniyar intanet; da
    iv. nazarin hanyoyi ko matakai da za a iya inganta kafafen.
    X.3 Babukan Littafin
    Wannan littafin yana ƙunshe da babuka guda biyar. Babi na ɗaya ya kasance shimfiɗa ne. A ciki an waiwaici samuwa da bunƙasar intanet. Bugu da ƙari, babin ya yi bitar kalmar ‘al’ada’ domin yin matashiya ga littafin. Bayan haka, babin ya dubi irin tasirin da intanet yake da shi a kan al’ummomi a duniya.
    An gina babi na biyu a kan bunƙasar al’adun Hausawa a duniyar intanet. Babin ya duba manyan kafafen intanet a duniya da suka karɓi harshen Hausa. Daga cikinsu har da Fesbuk. Bugu da ƙari, babin ya kalli ire-iren tasirin da intanet yake da shi ga Hausa da kuma Hausawa.
    Babi na uku ya mayar da hankali a kan nazarin yaɗuwar al’adun Hausawa a kan intanet. A ciki an duba yadda al’adun Hausawa daban-daban suka yaɗu a kan intanet. Sukan bayyana yayin da aka tura neman da yake da alaƙa da su a cikin injunan nema na kan intanet.
    A cikin babi na huɗu, an nazarci amfani da aibun intanet ga Hausa da Hausawa. Ya tabbata cewa, intanet ya zo da alfanu masu tarin yawa waɗanda Hausa da Hausawa za su iya cin gajiyarsu musamman yayin da suka bi hanyoyin da suka kamata. Daga cikin amfaninsa akwai ba da damar sada zumunta da haɓaka Hausa da yayata ta. Yana kuma taimakawa wajen adana al’adun Hausawan. Aibin kafafen intanet ga al’ummar Hausawa sun haɗa da ɓata tarbiyya da ɓata lokaci da samar da kafar damfara da makamantansu. A ɓangare ɗaya kuwa, intanet ya zo da ƙalubale daban-daban waɗanda dole sai an bi kyawawan matakai domin kauce musu.
    Babi na biyar ya tattauna nasarorin da kafafen intanet na Hausa suka samu a yau. Wannan ya haɗa da ƙaruwar ƙarfin tasirinsu a duniya da fannonin rayuwa da suka mamaye, ciki har da kasuwanci da ilimi. A ɓangare ɗaya kuwa, babin ya kawo wasu ƙalubale da kafafen suke fuskanta. Sun haɗa da ƙarancin tallafi da goyon baya daga masana da mahukunta da kuma wasu matsaloli da suka shafi yanayi da zamantakewar ƙasar Hausa.

    Original price was: ₦5,000.00.Current price is: ₦2,000.00.
    Add to cart
  • -29% KIMIYYA DA AL'AJABAN AL-QUR'ANI

    KIMIYYA DA AL’AJABAN AL-QUR’ANI

    0

    Na rubuta wannan littafi Mai suna: “KIMIYYA DA AL’AJABAN AL-QUR’ANI” don na fitowa da masu karatu tarin abubuwan al’ajabai da suke tattare da al-ƙur’ani mai girma.

    Original price was: ₦1,400.00.Current price is: ₦1,000.00.
    Add to cart