YARJEJENIYAR WIKIHAUSA LTD DATA  MAI SIYARWA/MARUBUCI

Wannan yarjejeniya ce da aka kulla tsakanin marubuci/mai siyarwa da kuma wikihausa ltd. La akari da shigowar ka/ki  cikin dandalin wikihausa ltd a matsayin marubuci/mai siyarwa, marubuci/mai siyarwa, ya/ta yarda da sharuda da dokoki kamar haka:

DAURA RUBUTU/AIKIN DA AKA YI 

Marubuci/mai siyarwa zai/zata yarda ya/ta bawa dandalin wikihausa ltd aikin da suka yi na ainihi (wato orijinal) domin siyarwa a dandalin. Wannan ya kunshi littattafai, Makalu, lacca-lacca, bidiyo da sauransu

CINIKI DA BIYAN KUDI

(dandalin (wikihausa  ltd) shi zai kayyade farashin abin da marubuci/mai siyarwa ya daura, shi kuma marubuci /mai siyarwa zai/zata karba kaso na kudin da aka siyar kamar yadda aka fayyace a kebantarciyar yarjejeniya.

HAKKIN MALLAKA

Marubuci/mai siyarwa ke da hakkin iko da mallaka akan aikin da suka bayar.  Dama ce da marubuci/mai siyarwa suka bawa dandalin wikihausa ltd da ya siyar da abin da marubuci/mai siyarwa suka daura a dandalin ta bisa sharuda da dokokin ta. 

 

 

NAGARTA/INGANCIN AIKI

mai siyarwa ya/ta yarda da su kula da ka idojin aikin da suka yi wanda dandalin wikihausa ya tanadar don tabbatar da aikin da suka mikawa dandalin yayi daidai da tsarin doka da kuma tafarkin al ada.

 YAKE HULDA

kowane bangare yana da damar yanke wannan yarjejeniya bayan gabatar da sanarwa. Yanke hulda anan baya shafar hakkoki da nauyika da suke gudana kafin wa adin yanke hulda.

TSARE DA KIYAYE SIRRI.

dukkanin bangarorin sun yarda da tsare/kiyaye sirri dake cikin muhimman bayanai da aka samar yayin wannan yarjejeniya.

 MADOGARAR DOKA

wannan yarjejeniya zata kasance tana dogara karkashin gudanarwar dokokin Nijeriya. Idan aka cike wannan akwati dake kasa, to mai siyarwa/marubuci ya nuna gamsuwa da karbar wandanan dokoki da sharuda da aka zayyana a cikin wannan yarjejeniya.

Na fahimta kuma na Amince