GAME DA WIKIHAUSA

Manufar wikiHausa ita ce yaɗa ilimin yadda ake yin komai cikin harshen Hausa a sauƙaƙe ta hanyar rubuce-rubuce da hotuna da bidiyoyi da kuma sautuka domin Hausawa da dukkanin masu sha’awar harshen Hausa.

Kafar ta mayar da hankali kan harshe da adabi da al’adun Hausawa, har ma da ilimin zamani. Bayan haka, shafin ya ba da damar aika tambaya kai tsaye. Ma’aikatanmu za su nazarci waɗannan tambayoyi tare da ba da amsoshinsu cikin lokaci.

WikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama’a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a sauƙaƙe, cikin harshen Hausa.