Yadda Sirrin Nagartacciyar Unguwa Yake

0
58

 Idan aka ce tsare-tsaren unguwa, to, ya kamata  mu tsaya mu kula da yadda za mu yi mu’amala da maƙwabtanmu dama sauran al’ummar Musulmi baki ɗaya.

 

A Cikin Wannan Ne Masu Tsere, Ke Tsere wa Juna

1.Murmushi da sakin fuska kan gina abin da miliyoyin Nairori ba su iyawa: Tabbata yawan murmushinka da sakin fuskarka ya ƙaru da kaso 30 cikin 100. Wannan tamkar kaso 30 cikin 100 na lada ya ƙaru cikin asusun lahirarka ne.

2.Taimako komai ƙankantarsa kan gina alaƙar shekaru masu yawa. Taimakawa mai neman taimako bakin iyawarka.

3.Gudunmawar biki ko suna kan ƙulla alaƙa har jikoki. Kar ka ya yarda a yi wata hidima face ka miƙa gudunmawa komai ƙanƙantarta.

  1. Manya su ji ƙan ƙanana, su kuma ƙananan su girmama na gaba da su. Wannan zai sa unguwa ta zama a bar kwatance.

5.Daure ka yi sallama ga duk waɗanda ka samu yara ko manya za ka ga kimanin adadi 20 cikin 100 na ayyukanka na lada ya ƙaru. Kar ka ƙosa da yin sallama koda kuwa gida ka shiga ka fito. Hadisi ya ce koda bishiya ce ta shiga tsakaninku to ka sake yi wa juna sallama.

6.Idan za ka zartar da hukunci, zartar da mafi sauƙi.

7.Tabbata akwai kason almajiri cikin duk abin da za ka ci a gida, ofis ko kasuwa. Za ka ga kaso 10 Cikin 100 na ayyukan alherinka ya ƙaru.

8.Tabbata a motarka ko aljihunku akwai ƙananan canji N5, NI0, N20, N50 don miƙa wa mabuƙata mai bara ko wanda bai roƙa ba, amma yana cikin buƙata koda zuciyarka na raya maka ba gaskiya yake ko take faɗa ba.

9.Tabbata ka kai ziyara asibiti aƙalla sau ɗaya a kowane wata koda ba ka da wani abu da za kakai. Idan kuwa kana da iko haɗa da ɗan wani a buga masu buƙata.

10.Kar ka yarda ka wuce wani abu mai cutarwa ka hanya a unguwa ka wuce ba ka dauƙe ba. Wannan wata garaɓasa ce Ubangiji Maɗaukaki Ya ba ka, ya ga ko za ka more ta.

11.Komai saurin da kake tsaya ka raba faɗan yara, ka kuma sasanta tsakanin manya bakin iyawarka.

 domin samun karanta cikkakken littafin danna koren rubutun nan                             

 

labarin da ya wuceArewa A Yau
Labarin na GabaMulkin Soja Da Jamhuriyya Ta Uku (1983-1999)