Yadda Halaccin Ado Da Kwaliya Yake A Musulunci:

0
265

Mafi yawan mutane a wannan zamani, sun afu da sha’anin ado da kwalliya, musamman mata, waɗanda a kullum ake ƙirƙiro musu kayan ado da sanyawa iri-iri, har ta kai wasu kayan kwalliyar na iya kawo tangarɗa ga lafiya da tattalin arziƙi da sauransu.

Ga alama wannan ce ta sanya Malamai suka tashi tsaye, wajen karantuwa da wayar da kai a kan illolin wasu daga kayan ƙawa (ado) na mata, domin kare su daga matsalolinsu.

Amma kuma yawaita yin suka, da bayyana hatsarin mummunar shiga da mata su ke yi, sai ya sanya wasu mutane suke ganin kamar malamai ba su damu da ado da kwalliya da tsafta ba, kamar sun fi so mata su kasance cikin shiga marar tsari da ƙayatarwa, wasu ma gani  suke yi kamar koyarwa Musulunci ɗungurungum ba ta damu da kwalliya da ado da tsafta, da tsari ba!

Amma abin ba haka yake ba, Malamai sun san muhammancin tsafta da ado ga Musulmi baki ɗaya, maza da mata, manya da yara, sai dai ganin yadda wasu mata musulmi suke kwaikwayon Turawan Yamma a  fannin shiga marar tsari, kuma ko’ina ba tare da tsare dokakin Allah ba, shi ne ya sanya malaman suka fi yin bayani a kan abin da zai nesantar da musulmi daga irin waɗancan miyagun halaye.

Tabbas shari’ar Musulunci tana la’akari da muhimmanci ado da ƙayatarwa a ɗabi’ar ɗan’Adam, domin haka ne, Allah bai haramta wa bayinsa ado da kwalliya da kayan daɗi na halaliya ba.

A gaskiya, da wuya a sami koyarwa da ta fi ta Musulunci nuna muhimmancin kwalliya da ƙayatarwa ba. Saboda har a cikin Alƙur’ani ayoyin da Allah yake bayanin buwayarsa cikin wasu halittunsa, domin ɗan’Adam ya gujjan ta samuwar Ubangiji, kuma ya kaɗaita shi,

kana ya godewa ni’imarsa, dake cikin waɗancan halittu daban-daban, duk da haka sai mu ga Allah na nuna mana ɓangaren ado da ƙayatarwa dake cikin halittun nan nasa, misali:

  • Halittar Sama:

Allah Ta’ala Yana cewa: “Haƙiƙa mun ƙawatar da halittar sama ta duniya, da adon taurari”. (Suratul Annamli :14)

To, a nan za mu ga ashe taurari bayan sauran ayyuka da manufofin samar da su, kuma su zamo ado ne da ƙaye ga samaniya.

  • Halittar Ƙasa:
  • Allah Ta’ala Yana cewa: “Kuma da abin da (Allah ) Ya halitta muka a cikin ƙasa (na abubuwa) masu launi iri-iri, haƙiƙa cikin wannan akwai abu lura ga mutane masu tunatuwa”.

Wannan  yana nusar da mu ya zuwa halittun Allah na ƙasa masu kyan gani da ban sha’awa, kamar su barewa da doki da jakin dawa da raƙumin dawa, a cikin dabbobi, kamar kuma ɗawisu da Zabo da Baini, a cikin tsuntsaye, kamar kuma Malam-Buɗa-Mana-Littafi da Wutar-Yola, a cikin ƙwari, da dai sauransu.

Haka kuma, a cikin  halittun Ubangiji masu ƙaye dake cikin ƙasa, aƙwai furanni da huda da ganyaye masu launi mai armashi, da ban sha’awa, kuma wasu bayan launi da suke da shi har da ƙanshi mai tausasa zuciya, duka wannan baiwa ce ta Allah ga bayinsa.

 

  Halittar Ruwa:

Haka kuma Allah Ta’ala ya bayyana ni’imominsa ga ɗan’Adam waɗanda ya sanya a tekuna da koguna dake bayan ƙasa, inda yake cewa:

“Kuma Allah shi ne wanda Ya hore muku kogi domin ku sami nama lafiyayye daga cikinsa, kuma ku fito da kayan ado wanda za ku dinga sanyawa”.(Sura Annahl, Aya ta 14).

  A wannan ayar, Allah ya nuna muhimmancin dangin abinci mai gina jiki wanda ake samu a kogi kamar kifaye da sauransu. Amma saboda nuna muhimmancin kayan ado a Musulunci sai ga shi an yi  ishara ya zuwa kayan ƙawa, Allah ya halitta a ruwa, kamar su jauhari da murjanai da gwala-gwalai da sauransu.

 

. Tufafi (Suttura):

Duk da yake babbar manufar tufafi ita ce suturta jiki, amma wata aya dake bayani a kan ni’imar sutura, sai da ta faɗi ɓangaren ado da kwalliya, a matsayin cikamakin  baiwar da Allah Ya yi wa bayaninsa ta hanyar hore musu tufafi. Allah Ta’ala Yana cewa:

 “Ya ku ‘yan Adam, haƙiƙa mun saukar muku da tufafi masu rufe muku tsiraicinku, da gashi (don ado da kwalliya) da kuma tufafin tsoron Allah, wannan (Kuma) shi ne mafi alheri”. Al- A’araf:( (24).

 Tabbancin Halaccin Ado da Kwalliya:

Wata aya ta tabbatar da cewa ado na Allah ne, don haka babu wanda zai  haramtawa bayinsa kayan da ya fitar don amfaninsu. kuma shi ado da kayan daɗin duniya na halak, duk an fitar da su domin Musulmi su more su a duniya, haka kuma a lahira su kaɗai ne za su sha daɗin waɗannan ni’imomi. Ayar tana cewa:

“Ka ce wane ne ya haramta kayan Ubangiji na ado da kayan daɗi na halal wanda ya fitar da su ne don amfanin bayinsa, ka ce wannan (duk) na musulmi ne duniya, kuma a lahira su kaɗai ne za su more su”.Al-A’raf:32.

  A nan za mu ga cewa Allah Ta’ala ya yi tsawa ga wanda ke ƙoƙari haramata wa Musulmi more kayan ado da na halal, kuma ya jingina ado ya zuwa ga zatinsa, saboda ya ce (ado Ubangiji), sannan kuma Allah ya tabbatar da cewa Musulmi tun a duniya, ya halatta su more waɗannan ni’imomi, bugu da ƙari, a lahira su kaɗai ne ma za su amfana da su.

 

Allah Ta’ala mai Kyau ne, kuma yana son abu mai kyau.

Magana a kan matsayin ado da ƙaye a addinin Musulunci ba za ta cika ba, har  sai an kawo Hadisin Manzo Allah (S. A.W) da ya ke cewa:

“Haƙiƙa Allah (Ta’ala) mai kyau ne kuma yana son abu mai kyau”. (Hadisi ne ingantancce).

Saboda haka duk abin da za a faɗa na yi ne don a hana su kyautata jikinsu da ƙawata kansu ba ne, sai dai a faɗakar da su a kan abin da zai iya zame masu illa, idan sun saɓawa ladubban ado da kwalliyar tasu a Musulunci.

Tabbas, a irin yadda kwalliya mata ta zamani take, tana buƙatar mata Musulmi su yi mata gyare-gyare, akwai nau’o’i da yawa na kayan sawa da na kwalliya, waɗanɗa suna iya zama matsala a gare su, a kan haka, bai kamata garin kwalliya a jawo wa jiki illa ba, ko kuma a jawo wa aljihu, ko jaka naƙasu ba! Ko Hausawa ma suna cewa:  “kada garin gyaran gira a tsone ido’!

domin samun karanta cikkaken littafin danna koren rubutu

 

 

 

labarin da ya wuceYadda Illolin Wasu Daga Kayan Ado Da Na Kwalliya Suke
Labarin na GabaYadda Musulmi Zai Ribaci Lokutansa Na Rayuwa