Yadda Ake Kunun Gyaɗa

0
3441

Kunun gyaɗa na ɗaya daga cikin abin sha mai daɗi da amfani a jikin ɗan Adam.

Abubuwan da ake buƙata;

Farar shinkafa

Ɗanyar gyaɗa 

Sugar daidai misali

Yadda ake haɗawa

A gyara farar shinkafa sai a wanke ta, a tsane tsaf. Bayan haka, a soya gyaɗa sama-sama a murje, bayan an bushe, sai a markaɗa, bayan an markaɗa a tace.

Sai a zuba tataccen ruwan gyaɗar a tukunya, in ya tafasa, sai a ɗauko wanna shinkafar da aka wanke aka tsane, sai a zuba ta a ciki, su yi ta dahuwa har sai ta dahu sosai.

Don gudun kada ya tsinke, za ki iya zuba ruwan lemon tsami kaɗan. Idan kuma an ga bai yi kauri ba, sai ki ɗan ɗibi gasarar koko a dama da ruwan sanyi sai a zuba a juya sosai zai yi kauri.

Domin sanin Yadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa danna koren rubutun nan.

labarin da ya wuceYadda Ake Yam Ball (Ƙwallon Doya)
Labarin na GabaIna Cikin Sallah Sai Na Tuna Akwai Najasa A Zanina. Yaya Zan yi?
Khadija Yusha'u (Amira) Babbar ɗalibar Addini ce, wacce ta karanci abin ci da lafiyar sa (Food and Nutrition) da kuma ƙwararriyar mai haɗa abin ci da kuma koyar da aikin hannu.