Yadda ake katse mutane idan kuna maga cikin ladabi

0
970

Idan aka fara  tattaunawa da mutane da yawa, kowa kan so ya tofa albarkanci bakinsa. Amma, ta yaya za ka iya katse mutane idan kuna maga cikin ladabi ba tare da bata wa kowa ba?

Tattaunawar  da mutane da yawa a lokaci guda abu ne mai wuyar sha’ani, kama daga wanda za kaga hankalinsa baya wajan, zuwa ga wadanda su ka iso daga baya amma su ke tambayoyin da tuni an bada amsoshinsu.

Sai dai kuma, abinda yafi komai wuya a irin wannan tattaunawar shi ne, yadda za ka samu ka ce wani abu. Ga shi kuma mutane da yawa na son a ji ta-bakinsu.

Tambayar anan ita ce; yaya za ka iya yin magana ba tare da ka bata wa kowa ba?

Yin magana

Abdullahi uba chamo, dan kasar Najeriya ne bangaren da ke amfani da harshen Hausa, wanda ya ke aikin kulada mutane acikin jirgi yayin tafiya a sararin samaniya (Cabin Crew) a birnin Kano ta kasar Najeriya. Yace katse mutane ya zama dole; “Babu yadda ka iya, sai ka yi.”

Duk da haka, akwai dabarun da yake bi kafin ya katse mutane.

Na farko dai, ka tabbatar ka na da kwakkwaran dalilin da ya sa ka yi kutsen, in ji Richie Frieman, marubucin littafin kyakkyawar mu’amala a zamanance mai suna “REPLY ALL… And Other Ways to Tank Your Career”.

Dalilin na iya zama na kokarin iza mutane su yanke hukunci, tattara bayanin matsayar da aka cimma ko kuma ware wadansu bayanan da za’a tattauna akai nan gaba. Mataki na biyu shi ne ka saurari yadda sauran mutane ke katse wasu domin fahimtar hanyoyin da su ka karbu wurin mutanen da ka ke tattaunawar da su.

Kar ka bada kunya

Da zarar ka katse mai magana, to kowa zai mai da hankali gare ka, don haka kar ka yi abin kunya.

“Ka tabbatar maganar da zaka fada mai muhimmanci ce. Ba wai kawai ‘na amince da wane ba'”. Idan kutsen naka na da ma’ana, zai fi saurin samun karbuwa.

“Na kan ji haushi idan wani ya ce, ‘Ina ga ya isa haka’… Wannan wulakanta mai maganar ne,” in ji Abdullahi chamo. Duk lokacin da ka nuna gudunmawar wani ba ta da amfani, za a kalle ka a matsayin mara mutunci.

Domin kauce wa haka, akan katse mutane ne a hankali, tare da gode wa mai maganar bisa batutuwan da yake fada.

Daga nan ya karkata akalar hirar ta yadda wancan mai surutun ba zai ci gaba da zuba ba. Ya kan ce, “Wannan maganar taka na da muhimmanci, kuma zamu iya tattaunata nan gaba, kasancewar yanzu lokaci na neman kwace mana.”

Togaciya

Wani lokacin da yake da saukin cusa baki, shi ne idan mutane su ka fara magana a tare ba mai jin ta wani ko kuma lokacin da aka yi tsit. “Ba wanda zai ga laifinka don ka yi kokarin cewa wani abu a lokacin da kowa ya yi shiru.”

Ko kuma ka yidabarar yin togaciya tun kafin a fara tattaunawar. Bayyana musu cewa idan na ga maganar da ka kawo ta fita daga hurumin abinda muke tattaunawa zan iya ce maka ‘ba yanzu ba sai dai karo na gaba’. Wannan togaciyar, kan taimakawa mutane su amince da duk wani kutse da za ka yi musu a lokacin da ku ke tattaunawar.

Da cewa: “Togaciya, kan sa mutane su fi sakin jiki idan an katse su.”

BAR AMSA

Please enter your comment!
Please enter your name here