Yadda Ake Faten Shinkafa

0
103

A yau za mu koyi yadda ake faten shinkafa

Abubuwan da ake buƙata

 • Kaza ko Nama
 • Shinkafa
 • Kayan ƙamshi
 • Mai, kayan ɗanɗano
 • Masara
 • Tafarnuwa
 • Citta
 • Albasa
 • Cinammon
 • Persley
 • kayan miya
 • Koren tattasai

Yadda ake haɗawa

 1. Za a sami nama ko kifi, idan nama ne, yana buƙatar a dafa shi kamar awa ɗaya, yadda zai yi laushi sosai
 2. Idan kifi ne za a wanke, a sa masa sinadarai da mai ɗanɗano, sai a saka shi a tukunya, a ba shi wuta kadan, don su shiga jikinsa, amman kar a sa ruwa.
 3. Sai a zuba markadaɗɗen kayan miya, amman ba da yawa ba.
 4. A kawo ɗan mai kaɗan, shi ma a zuba, a soya sama-sama kar ya soyu sosai.
 5. Sannan a kawo ruwa da ɗan dama a zuba, da sinadaran ƙamshi, amman ba masu yawa ba.
 6. A wanke shinkafa a zuba, idan ya tafasa, a zuba nama da ruwan naman, ana son aƙalla shinkafar ta yi awa ɗaya don ta samu ta farfashe, tun da romonta ake so. idan anga ta yi kauri, sai a kawo kayan mai ɗanɗano da cinnamon a zuba, a rage wuta, idan kuma da kifi ake yi, to sai a zuba.
 7. Sannan a yanka koren tattasai da parsley da albasa a zuba, a bar shi ya yi kamar minti 2 sai a sauke.

Domin sanin yadda ake pancake danna nan

labarin da ya wuceYadda Ake Kunun Goriba
Labarin na GabaYadda Ake Plaintai Chips
Suna na Isa Uba Chamo masanin na'ura mai kwakwalwa da ilimin addini da harshen Hausa da kuma ilimin halaiyar dan adam, kuma nine wanda ya samar da wannan manhajar wikiHausa tare da abokaina domin taimaka hausawa wajen samon ilimin cikin harshen Hausa a sauƙaƙe