Yadda Ake Addu’ar Ƙunutin Wutiri

0
29

“Allaahummahdinii fiiman hadaita wa aafinii fiiman aafaita wa tawallanii fiiman tawallaita, wa baarik lii fiimaa a’aɗaita, wa ƙinii sharra maa ƙadhaita, fa’innaka taƙdhii wallaa yuƙdhaa alaika, innahu laa yazillu man waalaita, (walaa ya’izzu man aadaita), tabaarakta Rabbanaa wa ta’alaita”.
{Ya Allah! Ka shirye ni cikin waɗanda ka shiryar, ka amintar da ni daga mummuna cikin waɗanda ka yi wa aminci daga mummuna, ka jiɓanci lamarina cikin waɗanda ka jiɓanci lamarinsu, ka albarka ce ni cikin abin da ka ba (ni), ka kiyashe ni sharrin abin da ka ƙaddara, domin kai ne kake hukunci, babu wanda yake hukunci a kanka. Tabbas wanda ka jiɓance shi, ba zai wulaƙanta ba, wanda kuma ka ƙi shi, ba zai ɗaukaka ba. Alherinka ya yawaita, ya Ubangijinmu! Kuma ka ɗaukaka}.
“Allaahumma inni a’uzu bi ridhaaka min sakhaɗika, wabi mu’aafaatika min uƙuubatika, wa a’uzu bika minka, laa uhsii sanaa’an alaika, anta kamaa asnaita alaa nafsika”.
{Ya Allah! Ina neman tsari da Yardarka daga Fushinka, da kuma Rangwamanka daga Uƙubarka, kuma ina neman tsari da kai daga gare ka. Ban isa in tuƙe ga yabo mai cancanta gare ka ba; kai dai kamar yadda ka yabi kanka ne}.
“Allaahumma iyyaaka na’abudu, walaka nusallii wa nasjudu, wa ilaika nas’aa wa nahfidu, narjuu rahmataka, wa nakhshaa azabaka, inni azabaka bil kaafirina mulhiƙun. Allaahumma innaa nasta’iinuka, wa nastagfiruka, wa nusnii alaikal khaira, walaa nakfuruka, wa nu’uminu bika, wa nakhdha’u laka wa nakhla’u man yakfuruka”.
{Ya Allah! Kai kaɗai muke bautawa, kuma gare ka kaɗai muke sallah, muke sujada, kuma gare ka kaɗai muke ƙoƙari muke gaggawa wajen aiki muna ƙaunar rahamarka, kuma muna jin tsoron azabarka. Lalle azabarka mai riskar kafirai ce. Ya Allah! Muna neman taimakonka, kuma muna neman gafararka, kuma muna yabon alheri a gare ka; ba ma kafirce maka, kuma muna imani da kai, muna ƙasƙan da kai gare ka, kuma muna yarɓe wanda yake kafirce maka}.

Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Da Ake Yi Bayan An Yi Sallama Daga Wutiri danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceAddu’a Bayan Tahiyyar Ƙarshe Kafin Sallama
Labarin na GabaAddu’ar Tafiyar Da Ƙuncin Zuciya
Suna na Isa Uba Chamo masanin na'ura mai kwakwalwa da ilimin addini da harshen Hausa da kuma ilimin halaiyar dan adam, kuma nine wanda ya samar da wannan manhajar wikiHausa tare da abokaina domin taimaka hausawa wajen samon ilimin cikin harshen Hausa a sauƙaƙe