Wannan shi ne kumburi tareda ƙaiƙayin da fata ta wani ɓangare ko duka jiki keyi lokacin da jiki ya sako wani sanadari(histamine) dama sauran sinadarai waƴenda zasu saka ƙananan jijiyoyi su fidda ruwa wuri ya kumbura sanadiyar samuwan wasu abubuwa da jikin bai yarda dasu ba,bincike ya tabbatar cewa duk cikin mutum biyar sai an samu ɗaya aƙalla da zaiyi ko yattaɓayin samiha a wani lokaci na rayuwar shi/ta.
Tana iya zuwa ta wuce da kanta a tsawon lokacin da baifi wata ɗaya da sati biyu ba(Acute) wadda ita tafi yawa,tana kuma iyafin tsawon wannan lokacin tana(Chronic).
Abubuwan Dake Kawota
Ya danganta da jikin mutum,abubuwan da bincike ya tabbatar sun ha’da da
- Shan wasu rukunnan magunguna kamar wasu antibiotics,dana rage ra’dadi da Kuma na hawan jini.
- Baƙin kifi, Madarar shanu, chocolate,gya’da da sauran su.
- Zafi ko sanyi
- Matsatsun tufafi ko pressure tama fata yawa.
- Hasken rana ga wasu,carpet idan data ta taɓashi,cizon wasu ƙwari,idan Kuma fata ta taɓa wasu ganyuka( plants).
Duk waƴenan bincike ya tabbatar suna saka acute urticaria innan,akwai kuma wasu cutuka kamar hepatitis,cancer,filariasis dake saka Chronic urticaria.
Domin karanta Yadda Za Ki San Kanki Kafin Ki Yi Aure Danna nan
Magance matsalar (Treatment)?
Mafiya yawanci samiha tana zuwa ne takuma wuce da kanta ko ba’a sha komai ba,amma saboda ƙaikayi mai tsanani da kumburin da jiki keyi, akan iya bada magani ko alluran da zata kawar da ƙaikayin takuma saukar da kumburin,amma abinda yafi komai anan,shi ne agano miye ya haddasa wannan samihar(Allergen) sai ayi avoiding inshi. Kamar misali idan matsatsun tufafi suka saka samihar sai a ciresu, sai abar saka matsatsun tufafin, a saka masu yalwa,shikenan an kawar da matsalar,amma koda ansha magani domin rage ƙaikayin matuƙar za’a koma saka tufafin akwai yuyuwar ta dawo.
Domin karanta bayani akan Larurar Sarƙiwar Numfashi Da Ake Kira (Asthma) Danna nan