Raya Daren Lailatul ƙadari

0
138

Daren Lailatul ƙadari, dare ne guda ɗaya da ake samunsa a watan Ramadan na kowacce shekara. Dare ne mai ɗimbin falala da daraja da babu wani dare da yake da irin waɗannan darajoji.

Allah Ta’ala ya saukar da sura guda a kan bayanin darajar wannan dare wato Suratul Kadari. A cikin surar Allah ya bayyana cewa wannan dare a cikinsa aka saukar da Alƙur’ani, kuma ya fi dare dubu wanda ya kama shekara tamanin da uku da wasu kwanaki ma’ana wanda ya dace da yin ibada a daren karɓaɓɓiya, za a ba shi ladan irin wannan ibadar na shekara 83.
Babu wanda ya san takamaiman daren nawa ga Ramadan ne daren Lailatul ƙadar. Amma ingantattun hadisai sun tabbatar da cewa ana samun daren Lailatul Kadari a dararen mara na goman ƙarshe na watan Ramadan, wato dararen 21, 23, 25, 27, da 29. Saboda haka, in goman karshe na Ramadan ya kama, sai a ƙara zage dantse a ƙara kan Ibadun da ake yi domin neman dacewa.
Babu wata alama da ake gani da za a ce in mutum bai ganta ba, to bai yi dace da Lailatul Kadari ba. Amma a washe garin daren, yanayi yakan kasance madaidaici.

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ciyar Da Mai Azumi danna nan.

Wannan bayani anciro shine daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya walfashi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceFalalar Ciyar Da Mai Azumi
Labarin na GabaFalalar Raya Daren Lailatul Ƙadari