Description
Babban burin kowane miji da mata bayan an yi aure shi ne samun ‘ya’ya managarta; waɗanda za su zama farin ciki ga Iyaylinsu da duniya da lahira.
Amma fa ya wajaba a sani cewa sai fa an yi tarbiyya Sannan ake samun ‘ya’ya na gari wato dai yanzu nauyi ya ƙaru a kan ango da amarya yanzu kun zama umma da baba. A kan haka na rubuta wannan taƙaitacciyar maƙalar domin sanin makamar aikin tarbiyya.
Da farko ya kamata uwa da uba su sani cewa aikin tarbiyya wajibi ne kamar yadda salla da azumi da sauran ibadu suke wajibi.
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Kowane ɗaya daga cikinku mai kiwo ne kuma za a tambaye shi kan abinda aka ba shi kiwo. Za a tambayi shugaba a kan talakawansa, za a tambayi maigida a kan iyalinsa; za a tambayı uwárgida a kan mutan gidanta.
(Bukhari da Muslim).