Description
Shugabanci a musulunci bai tsaya kan zaɓaɓɓun ko naɗaɗɗun masu muƙami ba, a’a kowa a iya huruminsa da sana’arsa shugaba ne kuma za a bincike shi a kan wannan shugabancin, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya faɗa.
Na yi ƙoƙarin kawo muhimman hadisai da suke magana akan shugabanci na yi musu take daban-daban na fassara su; kuma na yi musu sharhi gwargwadon fahimta ta. Na kawo hadisai tamanin da biyu sahihai da hasanai sai dai akwai tsirarun da’ifai waɗanda na faɗe su.