Description
Cutar Korona (Corona Virus, Covid-19, Novel Corona) cuta ce mai sarke numfashi wacce Duniya ta fara saninta a watan karshe na shekarar 2019 (1440H); Ta zama annoba (pandemic) saboda ta yadu a kusan dukkannin Kasashen Duniya cikin kankanin lokaci; ta samo asali daga Kasar Sin (China); Tana yaduwa ta hanyar mu’amala da wanda yake dauke da cutar, musamman hada jiki, ko shakar nunfashi a yayin da mai dauke da ita ya yi atishawa ko tari;