fbpx
₦0.00

No products in the cart.

Home addini Guziri Ga Mai Azumin Ramadana

Guziri Ga Mai Azumin Ramadana

0.00

Category: Tags: , , ,

Description

Gabatarwa
Wannan Littafi mai suna “Guziri Ga Mai Azumin Ramadana” wanda ɗan’uwa Mal. Ibrahim Garba Nayaya ya wallafa, ya ƙunshi muhimman bayanai dangane da watan Ramadan da kuma yadda rayuwar Musulmi yakamata ta kasance a cikinsa.
Haƙiƙa ɗan’uwa Mal. Ibrahim Garba Nayaya ya yi ƙoƙari matuƙa wajen taɓo abubuwa da ɗan’uwa musulmi ya kamata ya sani ya kuma aikata su a wannan wata mai albarka. Kama daga ma’anar azumi, wajibcinsa, falalarsa, tsayuwa cikinsa, buɗa-baki, sahur; abubuwan dake ɓata azumin da waɗanda ba sa ɓatawa, Tarawih, ittikafi, Zakkar fid-da-kai da azumin sittu Shauwal.
Wannan Littafi gudumawa ce babba ga ƙoramar ilimi, domin Littafin ya dogara ne a kan littattafai, sharhohi da kuma bayanai daga malamai masu nagarta da jajircewa a kan koyarwar Alƙur’ani da Sunnah.
A ƙarshe, ina kira ga ɗan’uwa musulmi ya sadaukar da wani ɓangare na lokacinsa, ya karanta wannan Littafi domin amfanuwa da darusan dake cikinsa.

Error decoding the Instagram API json
×

Maraba!

Yi magana da mu kai tsayi ta WhatApps ko a shiga group din mu.

×