Description
GABATARWA
Abin da idanuwan mu suke nuna mana da wanda kunnuwanmu suke jiye mana game da fushi; abu ne mai tayar da hankali.
A kusan kullum ba a rasa labarin kisan kai, ko raunanta jiki, ko kashe aure, ko bijirewa zumunci, ko yanke hulɗa da kasuwanci ko ta siyasa, da makamantan waɗannan al’amura; kuma duk wannan katoɓara tana samun asali ne daga fushi da danginsa.