Description
Wannan littafi shi ne Diwanin Waƙoƙin Baka, Juzu’i Na Biyar: Matanonin Wasu Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Makaɗan Baka. Wannan Diwani na biyar ya ƙunshi wasu adadin matanoni na waƙoƙin baka daban-daban. An kasa wannan Diwani zuwa manyan sassa guda biyu. Akwai rukuni na farko wanda yake tattare da wasu waƙoƙi na makaɗa fada da kuma wasu waƙoƙi na makaɗa game-gari.
Shi kuma rukuni na biyu yana ɗauke ne da jerin wasu matanoni na wasu waƙoƙin baka waɗanda makaɗa mabambanta suka yi wa Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau.