Description
An juyar da wannan darasi (lecture) ya koma rubutun littafi, domin ya taimaka wa
‘yan uwa ɗalibai da ma al’ummar musulmi, domin su san su wane ne sahabban nan
goma(10)da aka yiwa bushara da gidan Aljanna. Ya taƙaitaccen tarihinsu da
matsayinsu da kuma dangantakar da suka haɗa da (Shugaban halitta عليه هللا صلى
وسلم) da kuma surukantakar dake tsakanin ahlul baiti da sahabbai. Sannan kuma
a cikin sa za ku ji sunayen matan (Shugaban halitta وسلم عليه هللا صلى) da yawan
hadisan da kowacce ta rawaito.
Asalin wannan littafin an ɗauko rubutunsa ne daga darasi (lecture) wanda Sheikh
Lawan Bello ya yi wa al’umma na tsahon makonni shida (6) a makarantar Gemston
(Gemstone College) dake Karamar Hukumar Tarauni daura da asibitin Standard a
Jihar Kano, (opposite Standard hospital). Muna roƙon Allah ya saka wa Malam da
mafificin alkairi ya biya masa dukkan buƙatunsa na alkairi.
Sai kuma mu da muka ga cewa ya kamata al’umma su amfana da wannan darasi
(lecture) da Malam ya gabatar,ta hanyar ba mu wannan darasin yana faɗa mana, mu
kuma muna rubutawa. Shi ne muka ga dacewarˋ rubuta ƙaramin littafi a shafin
yanar gizo a bisa shawarar malam Lawan Bello, domin taimaka wa al’ummar
musulmi, suma su amfana da wannan littafin mai ɗumbin fa’ida.
MU DA MUKA RUBUTA. Muna cikin ɗaliban da muka halarci wannan darasi
mai tarin amfani da albarka. Kuma an rubuta shi ne da izinin Malam Lawan Bello.
Bayan mun kai masa ya duba, ya yi duk gyare-gyaren da zai yi, kafin a ɗora shi a
shafin yanar gizo.
Reviews
There are no reviews yet.