Description
A wannan takarda an nufi aniyar yin magana ne a kanaiwatarwa da kuma sadarwar waƙar baka ta Hausa. Za a duba aiwatarwa, sannan kuma a yi nazarin yadda ake yin sadarwa ta waƙoƙin baka na Hausa. Sadarwa nan wajiba ce; idan ba a sadar da waƙar baka ba, to, ba a yi waƙar baka ba. Ashe kenan bayan an yi tunani baɗini, sannan, waƙar baka za ta cika sai kuma a sadar da ita wato sai an rera ta, a kuma sadar da ita ga jama’a, daɗa waƙar bakan nan ta gargajiya4 ce ko ta zamani.
Domin karanta littafin Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa danna nan