Daga hadisan da suka gabata, za mu fahimci cewa ranar Ashura sananniya ce tun kafin bayyanar Manzon Allah (S.A.W) kuma azumin ranar shi ma an daɗe ana yin sa tun zamanin Yahudu da Nasara har zuwa lokacin Larabawan jahiliyya.
To amma akwai waɗansu masu da’awar son ahlul bait (R.A), da bin tafarkinsu, su ba sa yin wannan azumin, suna ganin ƙirƙirar sa aka yi kawai wai don nuna farin ciki da goyon baya, kan kashe Sayyidina Husaini (R.A) da aka yi a ranar Ashura shekara ta 61 hijiriyya.
Wannan yana nufin tun ɗaruruwan shekaru kafin a haifi Husainin aka fara murnar za a kashe shi, ɗan uwa ka yi tunani, a hankalce haka za ta yiwu?
To, amma mu duba mu gani, shin su Ahlul baiti (R.A) yaya suka ɗauki ranar Ashura da kuma azumin ranar? Ga amsa daga bakinsu:
I-Sayyidina Ali (R.A): An karɓo daga Al-Aswad IbnYazid ya ce: “Ban ganin wanda ya fi Sayyidina Ali da Abu Musa yawan umartar mutane da yin azumin Ashura ba. I- An karɓo daga Abu Abdullahi daga mahaifinsa (A.S) ya ce haƙiƙa Ali (A.S) ya ce “Ku yi azumin Ashura. da Tasu’a saboda yana kankare zunubin shekara guda”2
Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan
II- Daga Abul Hassan (AS) ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya yi azumi ranar Ashura”. 3 2) JA’AFARU SADIK (R.A)
III- An karɓo daga Assadik (R.A) ya ce, “Wanda zai iya azumtar watan Muharram gaba ɗayansa ya yi, zai tsare mai yin sa daga dukkan saɓo”.
IV- Daga Abu Ja’afar (A.S) ya ce: “Jirgin ruwan Annabi Nuhu (A.S) ya tsaya a jikin dutsen Judee ruwan ranar Ashura, sai ya umarce gaba ɗayan mutane da aljanu da suke taře da shi da su yi azumi a ranar.
Wannan kaɗan ne daga maganganun Ahlul baiti (R.A) kan falalar azumin Ashura, saboda wani babban malamin Shi’a mai suna Radiyuddin Abul Kasim Aliyu bin Musa Ibn Ja’afar Ibn Tawus ya ce: Hadisai da yawa sun zo kan bayanin zaburarwar kan azumin ranar Ashura”.”
Mai karatu ka ga yadda maganganun Ahlul baiti (A.S) suka da ce da maganganun kakansu (S.A.W) da na sauran musulmi kan azumin Ashura da falalarsa da tarihinsa tun zamanin Annabi, falalarsa da tarihinsa tun zamanin Annabi Nuhu (A.S).
Don karanta Ma’anar Aure danna koren rubutu
Sai dai kuma su Kulaini da Dusi da ire-iren su sun yi fatali da waɗannan maganganu na gaskiya da hadisai ta yadda suka rago waɗansu maganganun suka jingina su ga Ahlul baiti saɓanin waɗanda suka gabata.
A irin waɗanan maganganu suke cewa wai Abu Ja’afar da Abu Abdullahi sun hana yin azumin Ashura, kuma yin sa bidi’a ne, kuma wai iyalan Yazidu ne da Banu Umayya suka ƙirƙiro domin murnar kashe Husaini, kuma duk wanda ya yi, to zunubinsu ɗaya da waɗanda suka kashe Husaini, da sauran maganganu.
To abin tambaya a nan shi ne, shin su ma Imaman da ma Annabi Nuhu da Ahlul Kitabi har ma da shugaban halitta (S.A.W) Banu Umayya ne? kuma wannan wace irin tufka ce da warwara daga Imamai? Anya suna baki biyu? Ko kuwa dai akwai wata a ƙasa? Kuma su Dusi da Sadik da Hurrul Amili, da Nuri Attabrasj da Ibn Tawus da suka rawaito falalar azumin suna yaɗa sunnar Banu Umayya ke nan? Ɗan uwa ka yi tunani.
Daga ƙarshe ya kamata a sani cewa, ruwayoyin da suke tabbatar da falalar ranar Ashura da yin azumi a ranar ingantattu ne a wurin malaman Shi’a, amma waɗanda suke hani da sukar azumin raunana ne! Kamar yadda shaihunsu Alhaj Assayyid Muhammad Rida Alhusaini Alha’iri ya faɗa a littafinsa mai suna: “Najatul Umma fi lkamatil Aza’i Ala Husaini Wal A’imma shafuka na 145, da 147, bugun birnin Kum na Iran shekara 1413.
Domin Karanta Bayani akan Matakan Zaman Lafiyar Kishiyoyi, Haƙuri Da Junansu A Kan Kurakurai Danna nan
GASKIYAR MAGANA
Daga abubuwan da suka gabata za mu fahimci cewa gaskiyar magana game da ranar Sshura da azuminta ita ce:
1- Ranar Ashura rana ce mai daraja da ake yin azumi a cikinta tun kafin bayyanar Manzon Allah (S.A.W).
2- Dukkanin musulmai tun daga Annabawa har Ahlul baiti sun yarda da haka. . 3- Duk abin da ya saɓawa abin da ya gabata ƙarya ne.
Ya Allah ka ganar da mu gaskiya ka ba mu ikon bin ta.
Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan