Mai Kula Da Kuma Dangogin Waƙafi

0
94

Sharuddan da aka tanada wanda ake so mai kula da waƙafi ya mallaka da kuma bangarori da dama na daga cikin dangogin waƙafin.

An Sharɗanta Mai Kula Da Waƙafi Ya Zama:
  1. Musulmi
  2. Baligi wanda ya halatta ya yi tasarrufi a shari’ance
  3. Mai adalci
  4. Yana da ilmi ko ƙarfi da zai ba shi damar tsayuwa tsayin daka wajen kula da shi.

Dangogin Waƙafi

Dangogin Wakafi Sun Haɗa Da Bangarori Kamar Haka:

  1. Ɓangarorin yaɗa addini da ilmantarwa:

-Gina da samar da abubuwan jin daɗin masallata a cikinsu, waɗanda suka haɗa da rijiyoyi don samun ruwan alwala da sauransu. Ba shakka musulmai magabata sun yi ƙoƙari matuƙa ta yadda suka samar da masallatai daban-daban tare da ƙawata su da fitilu da cika su da Alkur’anai da shimfiɗu, tare da ɗaukar nauyin ɗawainiyar kulawa da su da biyan albashin masu yi musu hidima ta hanyar karantarwa da ilmantarwa da kiran sallah da sauransu.

Kaɗan daga cikin misalan waɗannan sun haɗa da abin da masana tarihin Musulunci suka bayyana a litattafansu cewa yawan masallatan da suke birnin Kurɗubah ta ƙasar Andalus a ƙarni na  uku bayan hijira (ƙarni na goma a shekarar miladiyya) sun kai kimanin ɗari shida. Kowannensu an samar masa duk wani abu da ake buƙata don jin dadin masu amfani da shi.

Kamar yadda, kuma sanannen abu ne cewa har zuwa wannan zamani namu, akwai ragowar irin masallatai daɗaɗɗu irinsu masallacin Azhar da ke birnin Alkahira da Masjid Al-Amawiy dake birnin Dimashk da masallacin Kairawan da a halin yanzu yake  Tunisiya da sauran ire- irensu a sauran wurare daban-daban a fadin duniya.

labarin da ya wuceCIKAKKEN BAYANIN ABUBUWAN DA SAI DA SU AURE YAKE ZAMA KARƁAƁƁE
Labarin na GabaKasuwanci Da Fatauci A Ƙasar Hausa
Suna na Isa Uba Chamo masanin na'ura mai kwakwalwa da ilimin addini da harshen Hausa da kuma ilimin halaiyar dan adam, kuma nine wanda ya samar da wannan manhajar wikiHausa tare da abokaina domin taimaka hausawa wajen samon ilimin cikin harshen Hausa a sauƙaƙe