# WikiHausa > Yadda akeyin komai cikin harshen Hausa ## Posts - [Tatsuniyar ’Yar Biyayya](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-yar-biyayya/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wata yarinya mai hankali da tsananin biyayya ga iyayenta; ba ta saɓa wa umarninsu. Wannan biyayya da take yi waiyayenta, ta sa ƙawayenta na kishi da jin haushinta. Ana nan, sun rasa yadda za su yi da ita, sai wata rana aka tura su saran itace dajin da ke bayan garinsu. Da ƙawayen nan suka ga suna cikin daji tare da ita, sai suka tali ɓawon kargo suka ɗaure ta da shi, suka tafi suka bar ta a ɗaure a daji. Can da almuru, sai ga Zaki zai wuce. Yarinyar nan da ta ga […] - [Tatsuniyar Ɗanbushiya Da Ɗankomayya](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-danbushiya-da-dankomayya/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wasu mata su biyu, Bushiya da Komayya. Suna da’ya’ya samari su biyu. Ɗaya sunansa Ɗanbushiya, ɗayan kuma Ɗankomayya. Yaran nan sun yi kama da juna sosai, kuma sun shaƙu da juna. Komai iri ɗaya ake yi musu, kamar tufafi da sauran abubuwa makamantansu. Kwanci tashi, rannan sai ciwo ya kama Bushiya. Jikinta kuma ya ba ta cewa ciwon nan na ajali ne. Saboda haka, sai tace da Komayya ta kula da Ɗanbushiya idan ta rasu. Sai Komayya tace da ita: “Haba, ai abin da aka yi kina nan, shi ne za a yi ko […] - [Tatsuniyar Maibaiwa Da Dodanniya](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-maibaiwa-da-dodanniya/): Ga ta nan, ga ta nanku. A can ƙasar Kwarkiya, an yi wani mutum mai shanu da yawa a garkensa. Yana da ɗansa ɗaya, mai suna Maibaiwa. Kullum idan zai fita kiwo sai su tafi tare da wasu karnukansa guda shida. Wata rana sun fita kiwo, sai aka goce da ruwan sama, kamar ana zubar da shi da bakin ƙwarya. Kuma saboda rashin sa’a ba wurin fakewa. Yana dube-dube, can sai ya hango wani gida guda ɗaya ƙwal a cikin dokar daji. Sai ya je, ya shiga. Ashe gidan wata Dodanniya ne. Da ya yi magana sai ya ji shiru. Da […] - [Tatsuniyar Sarki Mai Mata Ɗaya Da ’Ya Ɗaya](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-sarki-mai-mata-daya-da-ya-daya/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani sarki mai mata ɗaya da ’yarsu ɗaya mai suna Kulu. Kwanci-tashi, Allah ya yi wa matar sarkin nan rasuwa. Bayan ɗan wani lokaci, sai Sarkin nan ya auri wata bazawara. Ita kuma tana da ’yarta mai suna Zainab. Bayan amaryar Sarki ta tare, sai ta sa wa Kulu karan tsana. Kullum sai azabtar da ita take yi. Wannan mata ta yi ta tunanin yadda za ta yi ta gama da Kulu, amma ta rasa. Daga ƙarshe sai tace da ’yarta, watau Zainab agolar Sarki, idan sun je rijiya ɗauko ruwa, ta sa Kulu […] - [Hukuncin Rai Da Rai Shi Zai Kawo Ƙarshen Kashe-Kashe](https://wikihausa.com.ng/hukuncin-rai-da-rai-shi-zai-kawo-%c6%99arshen-kashe-kashe/): RAI DA RAI… SHI ZAI KAWO KARSHEN KASHE KASHE  Whatsapp: 08039290267  20th June, 2026  “A cikin qisasi(kashe wanda ya yi kisa da gangan) akwai rayuwa” Qur`ani 2:179 SHIMFIƊA:  Wannan hukunci na kashe duk wanda ya yi kisan kai, ba hukunci ne da addinin musulunci ya kaɗaita da shi ba, hukunci ne wanda duk sauran addininai da Allah SWT ya saukar daga sama suka yi umarni da shi. A aya ta arba’in da biyar cikin Suratul Ma’idah Allah SWT ya yi nuni da cewa, an wajabta a kan banu Isra`ila hukuncin kashe duk wanda ya yi kisan kai wato ƙisasi. Banu Isra`ila ba su ɗau wannan hukuncin da muhimmanci ba, shi yasa kashe kashe […] - [Tatsuniyar Auren Kaza Da Muzuru](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-auren-kaza-da-muzuru/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wata kaza da ta ce za ta yi aure, sai zakaru suka yi ta zuwa neman aurenta. Duk zakaran da ya zo, sai Kaza ta ce ba ta son sa. Wani tace ya yi gajarta; wani ta ce ba shi da gashi; wani ta ce bai iya cara ba. Wani kuma idan ta raina shi, sai ta ce ba shi da sirdi, ko kuma ya yi tsawo, ko ba shi da kyaun fuska. Haka dai ta rinƙa korar su. Sai wata rana Muzuru ya sami labarin halin Kaza, da kuma buƙatar iyayenta na su […] - [Tatsuniyar Naƙuda A Daji](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-na%c6%99uda-a-daji/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wata mata mai ciki. Sai wata rana ta shirya za ta yi balaguro. Tana tafiya a cikin daji, sai naƙuda ta kama ta. Sai ta raɓa a ɗan wani wuri ta haihu. Ta ɗauki jinjirin ta kama hanya tana tafiya, ko za ta tarar da wani gida ta huta. Sai ko ta tarar da wani gida a tsakar dokar daji ta shiga. Ashe gidan nan na Dodo ne. Sai ko mai jegon nan ta ga ruwa a gidan, ta ɗiba ta yi wanka da shi, ta wanke ɗanta, ta dafa abinci. Sai ta hau […] - [Tatsuniyar Kunkuru Da Matarsa](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-kunkuru-da-matarsa/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani Sarki Kunkuru, wanda matarsa ta haifi ɗa namiji. Sai ya tara Kunkurayen garin ya sanar da su cewa matarsa ta haifi ɗa. Ya bayyana cewa duk wanda ya san sunan yaron, zai ba shi ’yarsa aure. Sai wani Kunkurun ya je bakin rafi ya ɓuya. Lokacin da ’yar Sarki da ƙawayenta da kuyangi suka je ɗaukar ruwa, sai Kunkurun ya faɗa cikin tukunya ɗaya daga cikin kuyangin, ya ɓuya. Bayan ’yar Sarki da jama’arta sun koma gida, kuma wadda ya shiga tukunyarta ta ajiye ruwan, sai Kunkurun nan ya fito, ya ɓuya a […] - [Tatsuniyar Kare Da Kura](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-kar-da-kura/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani Kare da wata Kura a Dajin Saidawa. Suna ganin juna amma daga nesa, har dai yau da gobe suka saba, sai suka ƙulla abota. Kare yana da ’ya’ya bakwai, Kura kuma tana da ’ya’ya biyar. Sai wata rana suka ce za su je daji dakan wake. Sai suka shirya suka fita. Suka yi ta tafiya har suka isa wurin dakan wake, suka kama aiki. Can sai Kare ya ce wa Kura: “Gara ki jeki ɗora mana sanwar kalaci. Ina ganin wake da shinkafa ya kamata ki dafa.” Kura na jin haka ta ce: […] - [Tatsuniyar Juya Ta Sami Gagare](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-juya-ta-sami-gagare/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wata mata da mijinta, ba su taɓa haihuwa ba. Sai ’yan gaza gani a garinsu suka shiga cewa ita juya ce ba mai haihuwa ba. Irin waɗannan maganganu kuwa sukan dame ta. Wata rana tana dawowa daga gona, sai ta ga wani jariri a gindin gamji. Sai ta ɗauke shi, ta goya, ta tafi da shi gida. Da mijin ya shiga gida, sai ta gaya masa ta haihu a gona. Ya yi murna, amma fa da ’yar shakka. Bayan mako guda aka raɗa wa jariri suna Tabi. Daga nan sai ta shiga zaman jego […] - [Tatsuniiyar Ɗankucaka](https://wikihausa.com.ng/tatsuniiyar-dankucaka/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana Ɗankucaka ya fita kiwon ragonsa a bayan gari. Ya yi wa Rago talala don kada ya shiga gonakin mutane ya yi ɓarna. Bayan la’asar sai ya koma ya kunce Ragon, ya hau ya kama tafiya. Da ya isa kusa da gidan Kura, sai Rago ya yi kuka. Da Kura ta ji kukan Rago sai ta fito da gudu ta kira Ɗankucaka. Da ya je sai tace: “Yaya sunanka ne?” To da man kuwa Ɗankucaka wani hatsabibin yaro ne. Wasu ma kan yi masa ganin aljani. Sai ya ce da Kura: “Sunana Ɗankucaka.” Kura […] - [Tatsuniyar Furera Da Gungume](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-furera-da-gungume/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wata yarinya sunanta Furera. Wata rana ita da ƙawayenta suka je daji neman itace, sai ta ga wani gungume ta ce za ta ɗauka, amma suka hana ta. Ta kafe faufau ita sai ta ɗauka. Ta ɗauka, ta tafi da shi gidansu. Ya zamana a gidan suna da dabbobi da yawa, kamar shanu da tumaki da awaki da jakai, har ma da alfadari. Furera ta ajiye gungume a tsakar gida. Can sai gungume ya kama waƙa yana cewa: “Nama, Furera nama, in ci, Nama, Furera nama, in ci, Nama, Furera nama, in ci.” Wannan […] - [Tatsuniyar Dawi Mai Turmi](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-dawi-mai-turmi/): Ga ta nan, ga ta nanku. A can wata ’yar unguwa da ke dab da wani tsauni, an yi wasu ’yan biyu, Awa da Dawi. Tun suna yara mahaifiyarsu ta rasu, suka ci gaba da taimakon juna. To, amma shi Dawi hatsabibin yaro ne, kuma duk sanda ’yar’uwarsa Awa ta dafa abinci, sai ya cinye. Kullum ana haka har ta kai sai da ta tona rami domin ta riƙa ɓoye rabonta na abincin a ciki, amma sai ya tono ya cinye. Wata rana Dawi ya ce da Awa: “Ni fa na gaji da zaman garin nan. Ina so ki goya ni […] - [Tatsuniyar Zinari A Bakin Kwano](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-zinari-a-bakin-kwano/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wani mutum ne yana zaune da matarsa a cikin talauci a wani ɗan ƙauye, babu cin yau balle na gobe. Wata rana sai ya je gona ya ga wata busasshiyar bishiya, ya hau ya fara sara da gatarinsa domin neman abin zaman gari. To akwai wani dutse mai kogo kusa da gonar. Sai kwatsam, ga wasu mutane su goma sha biyu riƙe da kwari da baka sun fito daga ciki. Da fitowarsu sai suka zauna suka ci abinci, suka tafi. Amma kafin su bar wurin sai da suka faɗi wani abu kamar haka: “Kalja sum […] - [Tatsuniyar Jika Da Kaka](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-jika-da-kaka/): Ga ta nan, ga ta nanku. A can wani ɗan ƙauye da ke kusa da Gulbin Tattabaru, an yi wata yarinya da ke zaune tare da kakarta. Rannan yarinyar tana shara sai ta tsinci kurkunu ta bai wa kakarta ta ajiye mata. Da ta gama sharar sai ta je wurin kakar ta tambaye ta: “Kaka, ina kurkununa?” Kakar ta dubi jikarta ta mayar da jawabi: “Ai na cinye, jikalle.” Da jin wannan amsa sai yarinya ta fusata; ta ƙura wa kakar ido ta ce: “A gaskiya kaka ban yarda ba.” Daga nan ta ɗauki buta, ta cika ta da ruwa; ta […] - [Tatsuniyar ’Yan Matan Fangama](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-yan-matan-fangama/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana ’yan matan Fangama suka shirya za su biki a wani gari da ke kusa da su. Dabarar zuwan ita ce ko za su yi dace kowaccensu ta sami manemi, wata rana a yi nata bikin. Kowacce dai ta ci ado, abin gwanin ban sha’awa. Amma kafin su tafi sai da suka fita bayan gari domin kowacce ta tsinko wa mahaifiyarta goriba. Dukkanninsu sun samo goriba, in ban da ɗaya daga cikinsu. Ita ta nema, ta rasa. Shi ne bayan sun koma gida, sai mahaifiyarta ta ce lallai ta koma sai ta samo, in […] - [Tatsuniyar Garin Da Ba Maza Sai Mata](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-garin-da-ba-maza-sai-mata/): Ga ta nan, ga ta nanku. An yi wani gari da duk mazaunansa mata ne zalla, watau ba wani namiji ko ɗaya a cikinsu. Su matan a kullum sukan tafi rafi su yi wanka, su kuma ɗauko ruwa. Sai wani mutum daga wani gari mai nisa ya ji labarin wannan ƙauye. Ya ɗaura ɗamara, ya kama hanya da nufin sai ya je wannan gari mai ban mamaki. Ya yi tafiya mai nisa a cikin ƙungurmin daji kafin ya isa. Da zuwansa sai ya hangi wasu mata kyawawa suna wanka a rafi. Ya matsa har ya isa kusa da su, ya gama […] - [Tatsuniyar Kanta Da Mugayen Abokananta](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-kanta-da-mugayen-abokananta/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wasu ’yan mata su goma sha biyu ƙawaye. A cikinsu har da wata ’yar Sarki mai suna Kanta. Ita kaɗai ce a wurin mahaifiyarta. Ita ce kuma ta fi kyau a tsakanin duk ’yan matan garin. Kowane saurayi a garin yana so ya aure ta, amma ta ƙi. A cikin waɗanda suke son ta har da wani maciji wanda ke zaune a cikin kogin da ke kusa da ƙauyen. Sauran ’yan matan suna kishin Kanta saboda farin jininta da kyauta. Saboda haka suka haɗa baki cewa za su ja ta zuwa kogin nan domin […] - [Tatsuniyar Dila Da Zomo](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-dila-da-zomo/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana Dila ya haɗu da Akuya. Bayan sun gaisa sai Dila ya tambayi Akuya ko za ta ba shi ɗaya daga cikin ’ya’yanta su je bakin kogi shan ruwa? Akuya ta amince amma fa da sharaɗi. Sharaɗin shi ne tana so Dila ya lura da ’yarta sosai kar wani mugun abu ya same ta. Shi kuma Dila ya amince da haka. Da Dila da ’yar Akuya suka isa bakin rafi sai suka tarar wuta na ci a wani rami da ke kusa da kogin. Tun da ’yar Akuya ba ta da cikakken wayo, sai […] - [Tatsuniyar Gizo Da Kura](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-gizo-da-kura/): Ga ta nan, ga ta nanku. Gizo ne yana yawonsa sai ya tarar da tarin kashi a wani wuri. Bai tsaya ba, ya tsallake ya yi tafiyarsa. Jim kaɗan sai Kura ta bi ta wurin, ita ma ta ga kashin, sai ta kama da ci, kuma ta ji kashin yana da daɗi, sai ta ce: “Lallai duk wanda ya yi kashin nan, namansa zai zama maidadin gaske.” Nan fa ta yanke shawara a kan sai ta gano wanda ya yi kashin. Saboda haka ta hau wani kututture ta shiga jira. Ta daɗe amma ba ta ga kowa ba.Haka ta haƙura; a […] - [Tatsuniyar Tasalla Mai Kifi](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-tasalla-mai-kifi/): Ga ta nan, ga ta nanku. Tasalla mace ce wadda ke zaune a wani ƙauye mai suna Saladuna. Tana kiwon wani kifi babba. Ta daɗe da wannan kifin, har sun saba da juna. Tasalla tana ciyar da kifin a kullum gwargwadon ƙarfinta. Saboda sabon da suka yi da juna, har yakan riƙa yin tsalle cikin wasanni da ita. Wata rana Tasalla ta yi tafiya, sai mutanen ƙauyen suka kama kifin nan suka cinye. Kowa ya ji daɗin naman kifin. Da Tasalla ta dawo sai ta nemi kifinta ko sama ko ƙasa, ya ɓace. Ta yi ta tambaya da cigiya ko ta […] - [Tatsuniyar Kwaɗayi Mabuɗin Wahala](https://wikihausa.com.ng/tatsuniya-kwa%c9%97ayi-mabu%c9%97in-wahala/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana mutuwa ta je wani ƙauye da saniya da ta turke, tana neman wanda zai sayi wannan saniya a kauyen. Mutane suka tsorata baki ɗaya suka ƙi. Can Gizo ya dubi mutuwa ya ce shi yana so. Suka yi yarjejeniya a kan baɗi Mutuwa za ta dawo ta yanke kunnuwan Gizo. Wato kunnuwan sun zama kamar da su zai biya saniyar. Nan da nan sai Gizo ya yanka saniyar shi da matarsa Koƙi suka dafa, suka ci, suka ƙoshi. Da shekara ta kewayo sai ga Mutuwa ta zo fansar bashi. Ta fara cigiyar wanda […] - [Tatsuniyar Yelwa Da Tsohuwa Da Sarki](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-yelwa-da-tsohuwa-da-sarki/): Ga ta nan, ga ta nanku. An yi wata yarinya mai suna Yelwa. Tana da ƙawaye da yawa. Wata rana Sarkin garinsu ya umurci ‘yan matan garin su je rafi, su kamo kifi bisa sharaɗin cewa duk wadda ta kamo ta yi masa miya mafi daɗi, ita zai aura. Daman sauran ‘yan matan sun tsani Yelwa. Saboda haka bayan sun kamo kifi sai suka haɗa baki suka jefa ta a cikin kogin ta nutse. Da farko har ruwan zai tafi da ita, to amma ta yi sa’a, wata tsohuwa ta zo ta tsamo ta. Wannan tsohuwa kuwa tana da baiwa. Yelwa […] - [Tatsuniyar Tsohuwa Da 'Yan Mata Uku](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-tsohuwa-da-yan-mata-uku/): Ga ta nan, ga ta nanku. An yi wata tsohuwa mai ‘ya’ya uku mata. Sannu a hankali suka girma, har suka kai munzalin aure. Saboda haka ta ce da kowaccensu ta fid da mijin aure. Nan da nan Allah ya ba kowacce wanda za ta aura. Suka yi aurensu, kowacce ta tare a gidan mijinta a garuruwa daban-daban. Bayan ‘yan kwanaki kaɗan, sai tsohuwa ta ce ya kamata ta ziyarci kowacce a gidanta a garuruwan da suke. Ta fara da zuwa garin ‘yarta ta fari ta tarar kusan dukkan mutanen garin kowa maye ne. Ga shi kuma suna da jela da […] - [Tatsuniyar Ɓarayin Albagadadi](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-%c9%93arayin-albagadadi-2/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani attajiri a wani gari ana kiran sa Albagadadi. Ba abin da yake so kamar ya ji wani yana neman taimako, domin ya taimaka masa. Duk ranar Jumma’a mutane kan taru maƙil a ƙofar gidansa, suna karɓar sadaka. Ana nan, ana nan, wata rana sai wani saurayi ya je wajensa ya ce masa yana son masauki, ko ya sami aikin yi a garin. Sai Albagadadi ya sauke shi a gidansa. Sannu a hankali, sai yaron nan ya zama hadiminsa, watau ya riƙa yi masa aikace-aikacensa na gida. Yaron kuma makarancin Alkur’ani ne sosai. Kullum […] - [Tatsuniyar Ƙuda Mai Kwaɗayi](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-%c6%99uda-mai-kwa%c9%97ayi/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wata ƙuda da ’ya’yanta. Kullum sukan je mahauta a kasuwa neman abin da za su ci, idan sun ƙoshi su koma gida. Wata rana sai ƙudar ta ja ƙawarta suka je mahautar neman abinci tare. Bayan sun samo, sai suka kama hanyar gida domin ita mai ’ya’yan ta kai musu gida, ta yi wa ƙananan cikinsu koto. A kan hanyar komawa sai suka gamu da wani mai zuma. Sai ƙudar ta ba ƙawarta ƙunshin abincin da ta samo wa ’ya’yan ta kai musu, saboda za ta bi mai zuma ko ta kalato musu zumar. […] - [Tatsuniyar Auta Da Dodanniya](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-auta-da-dodanniya-2/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani gari wai shi Shadafi. Mutanen wannan garin koyaushe suna zaune cikin tsoro, saboda wata dodanniya da takan cinye duk wanda ya fita waje daga faɗuwar rana har gari ya waye. Ana nan, ana nan, sai dodanniyar nan ta lura takan zagaye garin baki ɗaya ba tare da ta sami wanda za ta cinye ba. Sai ta dinga yi waƙanta kirari tana cewa: “Wa zai iya da ni, Ni dodanniya, Wa zai ja da ni, Ni dodanniya.” Kowa ya yi shiru, ba wanda ya taɓa tanka mata, ko da sau ɗaya. Kwanci tashi, sai […] - [Tatsuniyar Samarin Ɓarayi Uku](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-samarin-barayi-uku-2/): Ga ta nan, ga ta nanku. A can wani gari wai shi Komayya da ke kusa da Dajin Dila na yamma da ƙoramar Kada, akwai wasu samari su uku. Ɗaya ana kiran sa Ba-ka-son Asara; na biyunsu kuma Ɓarna; na uku Wayo. Kullum ba su da aiki sai su shiga gonakin mutane su tono rogo, ko su yi ta karya dawa ko gero ko masara, su je wani gari su sayar. Yau da gobe, abu ya ishi mutanen gari, har aka bullo da dabarar yadda za a kama ɓarayin nan. Da suka san an kafa doka a garin, sai Wayo ya […] - [Tatsuniyar Abotar Biri Da Kifi](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-abotar-biri-da-kifi-2/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani Biri da kullum yakan je rafi wanka, bayan ya gama yawon cin ‘ya’yan itatuwa da tsalle-tsallensa ya gaji. Wata rana ya je wanka rafin da ya saba zuwa, sai ya haɗu da wani Kifi a cikin ruwa. Sai Kifin ya nemi su ƙulla abota da Birin. Biri ya amince, kuma suka yi wa juna alƙawari ba za su ci amanar junansu ba. Suna nan, abotarsu ta yi ƙarfi. Wata rana sai Biri ya ce zai je ganin gida, watau a can wani daji da danginsa suke. Da Kifi ya ji haka, sai ya […] - [Tatsuniyar Muwa Muwa](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-muwa-muwa-2/): Ga ta nan, ga ta nanku. A can wani daji an yi wata raƙumar dawa mai suna Muwa. Ba ta da da ko ɗaya. Kullum in ta dawo daga kiwo, sai ta yi ta kuka saboda rashin haihuwar nan. Cikin ikon Allah rannan sai ta haifi ‘ya’ya huɗu. Saboda murna ta raɗa wa babban cikinsu suna Muwa Muwa, mai bi masa kuma Caccikarimba, na ukunsu kuma Malaladumba. Amma sai ta ki raɗa wa na huɗun suna, don ya fito a rame, ba ta son sa. Saboda yawan son ‘ya’yanta nata uku, sai ta gina musu ɗaki, ta saka su don kada […] - [Yadda Kunya Take](https://wikihausa.com.ng/yadda-kunya-take/): “kunya yana kawo dukkan alheri” Manzon Allah SAW Kunya wata ɗabi`a ce da take hana mutum aikata rashin ɗa`a ga Allah ko ga mutane. Kunya ɗabi`a ce da Allah ya yi umarni da ita tun tale-tale ba a addinin musulunci kaɗai ba, duk addinai kunya abu ne da aka yi umarni da shi, kuma abu ne mai kyau. Wannan ya sa Manzon Allah SAW yace: “Yana daga cikin abinda mutane suka gada daga kalaman hikima na Annabawa magabata shi ne: Idan ba ka jin kunya, toh ka aikata abinda ka ga dama” Allah Ta`ala ya ba mu labarin wasu `yanmata da […] - [Tatsuniyar Dogarawa Uku](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-dogarawa-uku/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wasu dogarawa ne dai su uku masu suna Gi da Ɗa da kuma Ɗo. Aikinsu shi ne gadin gidan Sarki. To, akwai wani mutum kuma a garin sunansa Giɗaɗo. Shi ke nan, Sarki kuma yana da kaji da yawa a gidansa. Wadannan dogarai kuma su Gi da Ɗa da Ɗo kullum suna zuwa kamun fari. Idan sun zo da su sai su zuba wa kajin Sarki. In kajin sun ga farin, sai su zo suna ci. Su kuma dogaran sai su kama guda uku, kowa da tasa. Sai su je su gasa, su ci. To, […] - [Tatsuniyar Ɗantsintuwa](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-dan-tsintuwa/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wata mata da mijinta, suna zaune a wani ɗan kauye. Sun daɗe tare, to amma Allah bai ba su haihuwa ba. Wata rana matar nan ta je gona, sai ta tarar da jinjiri a kan dutse, sai ta ɗauko. Ashe wannan yaro ba mutum ba ne, ɗan aljani ne, ba ta sani ba. Sai ta kawo yaron gida. Da mijin ya ga yaro, sai ya tambaye ta inda ta samo shi. Sai ta ce, ai ɗan tsintuwa ne, sai mijin ya ce, anya wannan mutum ne kuwa? Sai matar ta ce ai da ma […] - [Tatsuniyar Ɓarayin Albagadadi](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-%c9%93arayin-albagadadi/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani attajiri a wani gari ana kiran sa Albagadadi. Ba abin da yake so kamar ya ji wani yana neman taimako, domin ya taimaka masa. Duk ranar Jumma’a mutane kan taru maƙil a ƙofar gidansa, suna karɓar sadaka. Ana nan, ana nan, wata rana sai wani saurayi ya je wajensa ya ce masa yana son masauki, ko ya sami aikin yi a garin. Sai Albagadadi ya sauke shi a gidansa. Sannu a hankali, sai yaron nan ya zama hadiminsa, watau ya riƙa yi masa aikace-aikacensa na gida. Yaron kuma makarancin Alkur’ani ne sosai. Kullum […] - [Tatsuniyar Ƙuda Mai Kwaɗayi](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-kuda-mai-kwa%c9%97ayi/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wata ƙuda da ’ya’yanta. Kullum sukan je mahauta a kasuwa neman abin da za su ci, idan sun ƙoshi su koma gida. Wata rana sai ƙudar ta ja ƙawarta suka je mahautar neman abinci tare. Bayan sun samo, sai suka kama hanyar gida domin ita mai ’ya’yan ta kai musu gida, ta yi wa ƙananan cikinsu ƙoto. A kan hanyar komawa sai suka gamu da wani mai zuma. Sai ƙudar ta ba ƙawarta ƙunshin abincin da ta samo wa ’ya’yan ta kai musu, saboda za ta bi mai zuma ko ta kalato musu zumar. […] - [Tatsuniyar Auta Da Dodanniya](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-auta-da-dodanniya/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani gari wai shi Shadafi. Mutanen wannan garin koyaushe suna zaune cikin tsoro, saboda wata dodanniya da takan cinye duk wanda ya fita waje daga faɗuwar rana har gari ya waye. Ana nan, ana nan, sai dodanniyar nan ta lura takan zagaye garin baki ɗaya ba tare da ta sami wanda za ta cinye ba. Sai ta dinga yi wa kanta kirari tana cewa: “Wa zai iya da ni, Ni dodanniya, Wa zai ja da ni, Ni dodanniya.” Kowa ya yi shiru, ba wanda ya taɓa tanka mata, ko da sau ɗaya. Kwanci tashi, […] - [Tatsuniyar Samarin Ɓarayi Uku](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-samarin-barayi-uku/): Ga ta nan, ga ta nanku. A can wani gari wai shi Komayya da ke kusa da Dajin Dila na yamma da ƙoramar Kada, akwai wasu samari su uku. Ɗaya ana kiran sa Ba-ka-son Asara; na biyunsu kuma Ɓarna; na uku Wayo. Kullum ba su da aiki sai su shiga gonakin mutane su tono rogo, ko su yi ta karya dawa ko gero ko masara, su je wani gari su sayar. Yau da gobe, abu ya ishi mutanen gari, har aka ɓullo da dabarar yadda za a kama ɓarayin nan. Da suka san an kafa doka a garin, sai Wayo ya […] - [Tatsuniyar Muwa Muwa](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-muwa-muwa/): Ga ta nan, ga ta nanku. A can wani daji an yi wata raƙumar dawa mai suna Muwa. Ba ta da ɗa ko ɗaya. Kullum in ta dawo daga kiwo, sai ta yi ta kuka saboda rashin haihuwar nan. Cikin ikon Allah rannan sai ta haifi ‘ya’ya huɗu. Saboda murna ta raɗa wa babban cikinsu suna Muwa Muwa, mai bi masa kuma Caccikarimba, na ukunsu kuma Malaladumba. Amma sai ta ƙi raɗa wa na huɗun suna, don ya fito a rame, ba ta son sa. Saboda yawan son ‘ya’yanta nata uku, sai ta gina musu ɗaki, ta saka su don kada […] - [Tatsuniyar Abotar Biri Da Kifi](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-abotar-biri-da-kifi/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani Biri da kullum yakan je rafi wanka, bayan ya gama yawon cin ‘ya’yan itatuwa da tsalle-tsallensa ya gaji. Wata rana ya je wanka rafin da ya saba zuwa, sai ya haɗu da wani Kifi a cikin ruwa. Sai Kifin ya nemi su ƙulla abota da Birin. Biri ya amince, kuma suka yi wa juna alƙawari ba za su ci amanar junansu ba. Suna nan, abotarsu ta yi ƙarfi. Wata rana sai Biri ya ce zai je ganin gida, watau a can wani daji da danginsa suke. Da Kifi ya ji haka, sai ya […] - [Tatsuniyar Cin Amanar Ɗan'uwa](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-cin-amanar-danuwa/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani mutum da ‘ya’yansa guda biyu. Suna nan, suna nan, sai wata rana babansu ya tura su neman furannin ƙawa. An ɗauka cewa duk wanda nasa ya fi kyau, to mahaifinsu zai fi nuna masa soyayya a gidan, kuma za a yi masa aure. Shi ke nan, sai suka je. Da suka je, sai ƙaramin ya tsinki fure mai kyau. Da yayansa ya gani, sai ya ƙwace, sannan kuma ya kashe shi. Sai ya kai furen nan gida. Sai babansa ya yi masa aure. Daga baya sai babansa ya tambaye shi inda ƙanensa yake, […] - [Tatsuniyar Ya Tsinci Dami A Kala](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-ya-tsinci-dami-a-kala/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wasu yara su uku abokan juna. Wata rana sun je farauta sai suka kama maciji, suka aiki ƙaramin cikinsu ya nemo wuta domin su babbaka macijin, su ci; ya ce da su ba zai iya ba. Suka ba shi riƙon macijin, suka tafi neman wutar da kansu. Kafin su dawo ya saki macijin. Da suka dawo suka ce ina macijin, ya ce maciji ya fi ƙarfinsa, wai sun yi kokawa ya ka da shi a cikin toka, kuma ya gudu. Sai suka ce ba su yarda ba, sai ya biya su. Baki ɗaya suka […] - [Tatsuniyar Ɗan Agwai Da Kura](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-dan-agwai-da-kura/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani Ɗan Agwai yana kiwon ɗan akuyarsa, har ya girma ya yi ƙiba. Sai wata rana ya kama shi ya kai shi kasuwa. Namun daji da yawa suka yi ta taya ɗan akuyar, to amma da zarar sun ji tarihinsa, sai su wuce, su ƙi saye. Ana nan, ana nan, har labari ya kai ga kunnuwan Kura, uwar son na banza. Sai ta shirya, ta je a yi cinikin ɗan akuya da ita. Kura ta ga ɗan akuya ya yi ƙiba, kuma tana so. Sai ta tambaya: “Nawa kuɗin ɗan akuyan nan?” Sai Ɗan […] - [Tatsunyar Ɗan Buwaila Da Ɓangorinsa](https://wikihausa.com.ng/tatsunyar-dan-buwaila-da-bangorinsa/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani ƙauye wai shi Wake-Wake, kusa da Dajin Aljanu, inda aka yi wata mata mai ’ya’ya biyu, mace da namiji. Wata rana sai mahara suka kai wa ƙauyen Wake-Wake hari. Maharan kuma suna da yawan gaske kuma sun fi zaratan Wake-Wake yawa da tarin makamai. Faɗa ya ƙaure, aka yi musu kaca-kaca, ko’ina sai gawarwakin mutanen Wake-Wake ake gani a yashe. Mata da tsofaffi da ƙananan yara suka ruɗe, hankalinsu ya tashi, gigita ta yawaita. Da uwar yaran nan ta ga maharan sun hallaka jama’ar garin masu yawa, sai ta suri ’yarta domin ta […] - [Tatsuniyar Darajar Neman Sani](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-darajar-neman-sani/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wani mutum mai suna Duna wanda yake zaune da matarsa Delu a wani ɗan ƙauye da ke kusa da garin su Koƙi matar Gizo, sun jima da yin aure ba tare da Delu ta yi ko da ɓatan wata ba. Mijin dai bai damu ba, ita kuma ta dangana komai ga Mai sama. Ana nan sai wata rana Delu ta yi ɓatan wata. Ita da mai gidanta Duna suka yi murna. Bayan wata tara kuma ta sauka lafiya, ta haifi ɗa namiji. Bayan sati guda aka raɗa masa suna Maishuni. Da ya ɗan data, sai […] - [Tatsuniyar Ladi Da Dodo](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-ladi-da-dodo/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wata yarinya kyakkyawa tana tare da iyayenta waɗanda suke maƙwabtaka da surukan Gizo a wani ƙauye wai shi Yana. Sunan yarinyar Ladi. Wata rana sai ƙawayenta suka biya mata domin su tafi bayan gari cin kaɗanya. Da yayyenta suka ji inda za su, sai suka ce kada ta je saboda akwai wani mugun Dodo da yake kashe mazauna Yana in sun fita bayan gari. Ladi ta ƙeƙasa ƙasa, ta kafe ita sai ta je. Sai ta sha ɗamara, ta ɗauki sanhon zuba kaɗanya, ta bi ƙawayenta, suka fita bayan gari. Ba su tsaya ba […] - [Tatsuniyar Talume](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-talume/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana wata yarinya wai ita Talume sun je daji cin ɓaure ita da kawayenta da sauran ’yan matan garinsu, tare kuma da yayyensu mata. Bayan sun gama shan ɓaure, sai yayyen yaran nan suka ce da su: “Kowacce ta share hannunta, ta goge bakinta, kuma kada a ce za a ɓoye a kai gida.” Ashe Talume ta ɓoye wani ɓauren domin ta kai wa mahaifiyarta, ga kuma danƙonsa da ta bari a hannunta ba ta share ba domin ta riƙa lasa a hanya. Suna cikin tafiya sai ta riƙa tanɗar hannunta, tana jin zaƙin […] - [Tatsuniyar Sarki, Gizo Da Kwarkwata](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-sarki-gizo-da-kwarkwata/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana a can kusa da garin da Gizo ke sarauta, wani tsoho yana cikin gonarsa yana kashe kwarkwata, sai ya ga wata ƙatuwar kwarkwata, har ya haɗa manyan yatsunsa zai murtsuke ta, sai ta ce da shi: “Kada ka kashe ni, zan yi maka tsaro a gonarka, kada ka kashe ni.” Sai ya tambaye ta: “Idan na bar ki, me za ki yi mini?” Sai Kwarkwata ta ce: “Kai dai ka sake ni a cikin gonarka ka gani.” Mamaki ya kamaTsoho, sai ya sake ta a cikin gonarsa. Ya yi kamar ya tafi gida, […] - [Tatsuniyar Kogi Mai Cinye Maƙaryata](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-kogi-mai-cinye-ma%c6%99aryata/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani mutum da ’ya’yansa su goma sha biyu. Wata rana sai ya samo ’ya’yan kaɗanya ya kai gidansa. Da ɗaya daga cikin ’ya’yansa ya ga kaɗanya nunanniya, sai ya ɗauka ya shanye. Mahaifinsu ya tambaye su wanda ya shanye masa kaɗanya, kowanne daga cikinsu ya ce ba shi ba ne. Ya sake tambayar su, kowa ya ce ba shi ba ne. Suka yi ta yin haka, shi kuma wanda ya shanye kaɗanya bai bayyana kansa ba. Can dai sai mahaifin nasu ya ce da su: “To, tun da kun kasa fitar da wanda ya […] - [Tatsuniyar Kurege Da Biri](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-kurege-da-biri/): Ga ta nan, ga ta nanku. Kurege da Biri suka ga wata yarinya, kowannensu ya nuna yana son ta da aure. Sai kowannensu ya aika a tambayo masa izinin nemanta da aure. Iyayen yarinya suka ce duk wanda yake son ‘yarsu da aure sai ya kawo musu fatun namun daji. Da Kurege ya ji haka, sai ya je wurin Kaza ya ce da ita: “Ina gayyatar ki aiki a gonata gobe.” Kaza na jin haka ta ce: “To, zan zo amma fa kada ka gaya wa Kyanwa.” Sai ya ce: “Haba me zai sa in gaya mata kuwa?” Daga gidan Kaza […] - [Tatsuniyar 'Yar 'auta Da Kogin Rantsuwa](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-yauta-da-kogin-rantsuwa/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani mutum mai mata ɗaya da ‘ya’yansu tara maza da mata, waɗanda yake ƙaunar su ƙwarai. Kullum idan ya je kasuwa, sai ya sayo kifaye tara saboda yaran nan. Suna nan haka cikin annashuwa, sai wata rana da ya kai kifayen nan tara, ‘yar autar gidan ta ɗauki ɗaya ta cinye ba tare da ta tambaya ba. Ta yi haka ne kuwa saboda wautar ƙuruciya. Da ya duba ya ga kifaye ba su cika ba, sai ya ce a tafi rafin Tantafane domin ‘yan ruwa su yi maganin wanda ya cinye kifin nan. Shi […] - [Tatsuniyar Gwaidayara](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-gwaidayara/): Ga ta nan, ga ta nanku. A can bakin Rafin Kada akwai wani mutum da yake zaune tare da matansa su huɗu; sai dukkaninsu suka sami ciki a lokaci ɗaya. Da watansu ya kama suka haifi ’ya’ya duka mata. Bayan mako guda na al’ada, ya raɗa wa uku daga cikin yaran nan sunaye. Ɗaya sunanta Halima, ɗaya Jummai, ta ukun kuma A’isha. Amma sai ya ƙi rada wa ’yar matarsa ɗaya suna. Sai mahaifiyar tata ta tambaye shi: “Me ya sa ni ba za ka sa wa ’yata suna ba?” Bai dai amsa ba, amma ya ce zai raɗa mata suna. […] - [Tatsuniyar ’Yan Mata Biyu](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-yan-mata-biyu/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wasu ’yan mata, ya da ƙanwa ne uwarsu ɗaya, ubansu ɗaya. Allah ya yi musu ƙira mai kyau, har ma wasu kan ce kyansu kamar na aljanu. Wata rana ƙaramar ta fita ƙofar gida tana rigar aya, sai wani mutum ya gifta ya gan ta ya yi mata sannu. Da ta amsa sai ya ce da ita: “Kin san kyan da kike da shi kuwa amma a ce wai ke ce kike rege aya?” Da ta ji haka sai mamaki ya kama ta, ta ce masa: “Ai da ka ga yayata da ba ka […] - [Tatsuniyar Nasiru Da Nisiru](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-nasiru-da-nisiru/): Ga ta nan, ga ta nanku. A can ƙasar Mazarƙwaila an yi wani yaro ɗan Sarkin Zaƙi, mai suna Nasiru. Yana da wani aboki wai shi Nisiru. Ana kiran baban Nasiru Sarkin Zaƙi ne, domin ya fi kowa yin kayan zaƙi a garinsu. Shi Nisiru yakan je ya sami Nasiru su tafi cin zuma, watau su ƙona itace hayaƙi ya kori ƙudan zuma, su kuma su kwaso saƙarta da ruwan. Haka suke yi kullum. Ana nan, ana nan, sai mahaifiyar Nasiru ta rasu. Rasuwarta ke da wuya sai kishiyarta ta shiga ba Nasiru wuya. To amma ɗan kishiyar uwar mai suna […] - [Tatsuniyar Marowata](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-marowata/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani mutum a wata ruga da ke gefen Dajin Ganji. Yana zaune tare da matarsa da ’ya’yansu biyu. Suna da matashin sa ɗaya. Wata rana mai gidan da matar suka yanke shawarar cewa ya kamata su yanka san nan su ci nama. To amma su marowata ne na ƙin ƙarawa. Sai suka shirya cewa za su je dawa su yanka san inda ko ƙuda ba za su bari ya taɓa naman ba. Da zuwansu dajin sai suka tsuguna, suka yi kashi. Nan da nan ƙudaje suka rufe kashin; sai suka bar wurin wannan kashi, […] - [Tatsuniyar Wani Mutum Da 'Yarsa](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-wani-mutum-da-yarsa/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana wani mutum da ke garin Yamutsawa ya je gidan Sarkin garin ya ce yana so zai ba Sarkin ‘yarsa ya aura. Shi kuwa Sarkin Yamutsawa ya daɗe da matansa biyu. Da Sarki ya ji haka sai ya sanar da shi cewa ba zai ƙara aure ba, idan ma ya auri mace ta uku, to kuwa zai gille mata kai. Sai mutumin ya ce: “Na ji, na yarda ka aure ta ko za ka gille mata kan.” Shi kuma mutumin daman malami ne ɗanbaiwa. Shi ke nan, Sarki ya aure ta. Kamar yadda Sarki […] - [Tatsuniyar Biri Da Kare](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-biri-da-kare/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana Kare yana yawo a cikin gari, sai ya haɗu da Biri. Sai Biri ya tambaye shi inda za shi, ya ce: “Ina yawo ne ko zan sami ɗan abin da zan ci.” Shi ma Kare ya tambayi Biri inda za shi, ya ce: “Ai ni kullum a daji nake wuni, in ci abinci in ƙoshi.” Biri ya ce da shi: “Ko za ka bi ni ne?” Kare ya ce: “Ni ban taɓa zuwa daji ba.” Daga nan Biri ya tambayi Kare: “Shin kai ma kana da wayo irin nawa?” Kare ya mayar da […] - [Tatsuniyar Arɗo Da Ndoffiwa](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-ar%c9%97o-da-ndoffiwa/): Ga ta nan, ga ta nanku. An yi wani makiyayi wai shi Arɗo a can kusa da wani baƙin daji da ake kira Dajin Gafiya. Yana zaune da matarsa ɗaya, wai ita Hodanego. Shi Arɗo kullum yakan yini a daji ne wurin kiwo, amma ita matarsa ta ha’ince shi, domin tana da kwarto mai suna Ndoffiwa. Kullum idan mijinta ya tafi kiwo, sai ta kama kaza daga cikin kajin gidan ta yanka wa kwartonta, ta shirya abinci mai daɗi su ci tare. Ana nan, wannan abu yana tafiya, har dai wata rana wata maƙwabciyar Arɗo ta kira shi ta ce da […] - [Tatsuniyar Marainiya Mai Turmi](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-marainiya-mai-turmi/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wata Marainiya a wani gari. Sanda iyayenta suka rasu ba su bar mata komai ba, sai wani turmi. Turmin kuwa wani shu’umi ne mai ƙwanƙwamai, to amma sauran mutanen gari ba su san haka ba. Sai turmin ya ce da ita: “To, tun da ba ki da uwa, ba ki da uba, ni ne zan tsaya miki a madadinsu.” Wannan magana ta faranta wa Marainiyar nan rai. Sai ta dafa wa turmi ta ce: “To, na gode. Yanzu watau duk abin da nake so za ka ba ni?” Turmi ya ce da ita: “Ba […] - [Tatsuniyar Janniya](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-janniya/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wata mata mai ɗa wai shi Janniya. Suna zaune ita da kishiyarta tare da mijinsu cikin lumana. Wannan mata kuma tana da garken shanu. Bijimin da ke cikin shanun kuma yakan yi magana kamar mutum. Ana nan, ana nan, wata rana uwar Janniya da kishiyarta suna zaune suna taɗi, sai ta ce da kishiyar: “Ina jin fa na kusa mutuwa. Idan na mutu ki kula da Janniya.” Da kishiyar ta ji haka sai ta ce: “Haba! Ai ko ba ki faɗa ba ma zan kula da shi, ai ɗana ne.” Sai uwar Janniya ta […] - [Tatsuniyar Maharbi Da Zaki](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-maharbi-da-zaki/): Ga ta nan, ga ta nan ku. An yi wani maharbi da ke gefen Dajin Shiddar, a can yamma da ƙasar Sarkin aljanu. Wata rana ya fita farauta a daji, sai ya ga wani rami, bai yi wata-wata ba sai ya kutsa kai ya shiga. Ashe ramin nan na Zaki ne. Zaki ko na ganin sa sai ya yo kansa. Mutumin nan ya fito ya kama gudu, har ya fita daga dajin ya shiga karkara. Zaki dai na bin sa, har ya tarar da wani manomi, ya ce da shi: “Mai gida ka taimake ni.” Manomin ya ce: “Me ya koro […] - [Tatsuniyar Kurege Da Kura](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-kurege-da-kura/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana Kurege da ƙawarsa Kura suka fita farauta. Suna cikin tafiya, sai suka tarar da inda hanya ta rabu biyu. Hanyar da ta yi dama, doguwa ce, wadda ta yi hagu kuma gajeriya. Sai Kurege ya ce da Kura: “Tun da ke ce babba, sai ki bi doguwar hanyar, watau ta dama, ni kuma ƙarami in bi gajeriyar, wadda ta yi hagun.” Kura ta ce: “A a, kai ƙarami ka bi babbar hanya, ni zan bi ƙaramar.” Sai ya ce: “To, shi ke nan mu tafi.” Kowa ya kama hanyarsa. Kura da ta bi […] - [Ɗan Kutungayya](https://wikihausa.com.ng/%c9%97an-kutungayya/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani mutum da ke zaune awani gari mai suna Raƙumawa tare da matarsa da ’ya’yansu su goma sha ɗaya. Rannan sai matar ta haifi ɗa namiji, ya zama na goma sha biyu. Da haihuwar yaro kuwa sai ya yi magana ya ce wa uwarsa: “Kada ma a yi wahalar raɗa mini suna, domin sunana Ɗankutungayya.” Ya ƙara da cewa, ragon sunansa ma kada a yanka, a bar masa ya rinƙa hawa. Iyayen suka yi haka, jama’ar gari suna ta mamakin wannan yaro da abubuwan da ya yi. Ana nan, ana nan, sai wata rana […] - [Tatsuniyar Musare Da Hodanego](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-musare-da-hodanego/): Ga ta nan, ga ta nanku. An yi wani mutum mai mata biyu, da ’ya’ya biyu. Uwargidan tana da ɗanta mai suna Musare; amaryar kuma tana da ’ya wai ita Hodanego. Ana nan har yara suka girma. To da ma shi mahaifinsu yana da dabbobi masu yawa, sai ya ba Musare Akuya guda, ita kuma Hodanego da take ƙarama, ya ba ta Kaza. Suna nan, duk sanda Musare ya nemo wa akuyarsa abinci ya zuba mata, sai Hodanego ta saki kazarta ta je ta watsar da abincin. Kullum haka, har dai rannan yunwa ta kashe akuyar Musare. Ya yi haƙuri bai […] - [Tatsuniyar Marayu Biyu](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-marayu-biyu/): Ga ta nan, ga ta nanku. An yi wani mutum shi da matarsa suna zaune cikin farin ciki a wata ’yar unguwa ta mafarauta da ke bakin wani daji. Suna nan sai matar ta sami juna biyu. Bayan’yan watanni ta haifi ɗa namiji. Uwar da mai gidanta suka yi murna ƙwarai, zaman daɗi ya karu a tsakaninsu. Bayan matar ta yaye wannan ɗa na fari, sai kuma ta sake samun ciki, amma kuma sai mai gidanta ya rasu kafin ta haihu. Haka dai ta ci gaba da renon yaron da abinda ke cikinta, har Allah ya sa ta haihu lafiya. A […] - [Tatsuniyar Wata Mata Da Aljani](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-wata-mata-da-aljani/): Ga ta nan, ga ta nanku. An yi wata mata a wani ɗan ƙauye, wadda ta jima tare da mijinta, amma ba su sami haihuwa ba. Sun nemi maganin samun haihuwa, amma ba su sami biyan buƙata ba, sai suka dangana. Ana nan, ana nan, wata rana matar ta je gona tana noma, sai ta ji kukan yaro a gindin wata bishiya. Da ta matsa kusa, sai ta ga wani jariri a cikin tsumma, sai ta ɗauke shi ta goya, ta kuma ɗauki fartanyarta, ta koma gida. Da mijinta ya dawo sai ta ɗauko jariri ta kawo masa, tace da shi: […] - [Tatsuniyar 'Yar Mowa Da 'Yar Bora](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-yar-mowa-da-yar-bora/): Ga ta nan, ga ta nanku. A wani gari an yi wani mutum mai mata biyu da ’ya’ya biyu, ’yan mata; ɗaya sunanta ’Yar Mowa, ɗayar kuma ’Yar Bora. Suna nan, ran nan sai mijinsu ya rasu. Bayan ɗan wani lokaci kuma sai uwar ’Yar Mowa ta rasu, ta bar uwar ’Yar Bora kaɗai. To da ma kafin ta rasu, ta kira kishiyarta tace mata: “Don Allah ga amanar ’yata nan; ki kula da ita.” Sai tace: “To.” Amma da ta rasu sai uwar ’Yar Bora ta fara ganawa ’Yar Mowa azaba. Kullum ita ke yin hidimar gida, ba ta da […] - [Tatsuniyar Mai Haƙan Ɓera](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-mai-ha%c6%99an-bera/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani mutum da ba ya aikin komai sai ya fita farauta, yana haƙar ramukan Ɓera. Idan ya kamo ɓeraye yakan yanka ya yi bandar naman ya kai kasuwa ya sayar. Wani lokaci yakan fita wannan farauta tare da wani maƙwabcinsa, har ma sun yi suna ƙwarai wajen wannan sana’a tasu. Wata rana shi da maƙwabcinsa sun fita farauta, sai suka ga wani babban rami. Da suka tsaya za su haƙa sai maƙwabcin ya ce: “Wannan fa ramin Kura ne bana Ɓera ba. Kada mu tono abin da zai cuce mu.” Sai ya ce da […] - [Tatsuniyar Makauniya Da Ɗanta](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-makauniya-da-danta/): Ga ta nan, ga ta nanku. A wani ɗan ƙauye da ke yamma da Dajin Kurege, akwai wani manomi da matarsa makauniya. Suna cikin zama irin na rufin asiri, sai Allah ya yi masa cikawa. A lokacin kuwa tana goyon jariri mai suna Zama. Uwar tasa kuwa ta sha wuya wajen renonsa. Kullum sai ta je ta yo bara kafin ta ciyar da kanta da ɗanta. Mijinta kuma bai bar dukiya ba sai shanu biyu kawai da Zama ya gada. Ita kuma mace ce mai tsinkaye da riƙon amana, sai ta kai shanun nan wani garke, a rugar wasu makiyaya da […] - [Tatsuniyar Sandar Arziƙi](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-sandar-arzi%c6%99i/): Ga ta nan, ga ta nanku. A can wani gari da ya yi iyaka da ƙasar Aljanu, akwai wani mutum mara sukuni da matarsa, da ɗansu ɗaya. Suna zaune a cikin wannan hali, sai ɗan ya isa aure. Iyayen nasa sai suka ce da shi: “Yanzu ga shi ka isa aure, amma ba mu da abin da za mu aura maka mata da shi.” Amma mahaifinsa yana da wata sanda; sai ya ba shi ita yace: “Ka kama hanyar duk garin da ka zaɓa a zuciyarka; sandar za ta zama sanadin yin aurenka.” To, da yake yaron mai biyayya ne, sai […] - [Tatsuniyar Sarkin Maƙera Da Dodo](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-sarkin-ma%c6%99era-da-dodo/): Ga ta nan, ga ta nanku. A wani ɗan ƙauye, an yi wata mata mai ’ya’ya biyu, mace da namiji. Sunan namijin Fugo shi ne wa; ita kuma macen sunanta Awa, ita ce ƙanwa. Shi Fugo maƙeri ne. Ana nan, sai wata rana wani mutum daga wani gari mai nisa ya zo ya ce yana son ya auri Awa, sai aka yarda, aka ba shi ita. Bayan an gama biki, sai ya ɗauki matarsa suka tafi garinsu, wanda ba a bin hanyar zuwansa da rani saboda akwai wani dodo da kan tsare hanyar, ya cinye matafiya duk lokacin rani. Amma kuma […] - [Tatsuniyar Umbagila Da Dodo](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-umbagila-da-dodo/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani ƙaramin ƙauye da yake kusa da wani daji ai cike da dodanni. Ɗaya daga cikin dodannin ya matsawa mutanen wannan ƙauyen, yana kama su ya bautar da su. Yakan fita ɗibar kayan miya duk ranar Asabar. Saboda haka mutanen ƙauyen suka daina fita ɗibar kayan miya a ranar da Dodon yake fita domin kada ya kama su ya mayar da su bayi. Mutanen da ya kama ne sukan dafa masa abinci da sauran wahalhalun gida na yau da kullum. Ana nan cikin haka shekara da shekaru, sai wata rana wata yarinya wai ita […] - [Tatsuniyar 'Yan Goma Sha Ɗaya](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-yan-goma-sha-daya/): Ga ta nan, ga ta nanku. A can kusa da dajin Ƙanzon Kurege, akwai wani mutum da ke zaune da matarsa. Mace ce mai haƙuri da son taimakon mijinta a hidimar da yake yi ta kula da gida. Suna nan, sai Allah ya ba matar ciki. Sannu a hankali, ciki ya girma, sai mijinta ya ce tunda cikinta ya girma, ta daina zuwa rafi ɗaukar ruwa, amma sai tace ai babu mai taimaka mata. Ta ci gaba da zuwa ɗaukar ruwan. Ana nan, wata rana matar nan ta je ɗaukar ruwa sai ta fara naƙuda a bakin rafi. Da sauran matan […] - [Tatsuniyar Wata Mata Da ’Ya’yanta](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-wata-mata-da-yayanta/): Ga ta nan, ga ta nanku. A can kudu da garin su Gizo da Koƙi akwai wata mace mai ’ya’ya mata su huɗu, waɗanda ubansu ɗaya. Suna nan zaune cikin jin daɗi, sai ciwo ya kama mijinta, watau uban yaran nan. Da ya ga kamar ba zai tashi ba, sai ya sa aka yi wa ’yan matan nan huɗu aure. Bayan kamar wata uku da aurar da su, sai ya cika. Ɗaya daga cikin ’ya’yan nan ta yi aure a garin da ba a barci; ta biyu ta yi aure a garin da ake tsinkar gauta da hanci da tsinkar kuɓewa […] - [Tatsuniyar 'Yan Bakwai Da Aljana](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-yan-bakwai-da-aljana/): Ga ta nan, ga ta nanku. A can kusa da dajin aljannu wanda aka ce ya yi iyaka da bangon duniya, akwai wata mata mai ’ya’ya maza su bakwai. Ana nan, ana nan sai yaran suka girma, har dai suka isa aure. Da gyatumarsu ta ga sun isa aure, sai ta tara su ta ce: “Ya kamata a ce yanzu kun yi aure, tunda ga shi Allah ya sa duk kun girma, kowa ya mallaki hankalinsa.” Da suka ji haka, sai babban cikinsu ya ce wa uwar: “Za mu yi aure, amma muna so a sama mana ’yan mata bakwai waɗanda […] - [Tatsuniyar Wata Mayya Da Danta](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-wata-mayya-da-danta/): Ga ta nan, ga ta nanku. An yi wata mayya a wani gari, tana zaune da mijinta, har ta sami rabo. Daga ƙarshe ta haifi ɗanta namiji aka sa masa suna Malgwi. To da man tun tana da cikinsa ubansa ya rasu, ya bar dokinsa, wanda yaron ya gada. Uwar ta kula da dokin har Malgwi ya girma, ya zama saurayi kyakkyawa. Wata rana sai wata ƙawar uwar Malgwi ta ziyarci gidansu. Sai ita da baƙuwa suka zauna a tsakar gida suna hira. Sai ƙawar tace da ita: “Ya kamata ki san yadda kika yi da ɗanki tun da ya girma […] - [Tatsuniyar Awa Da Dawi](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-awa-da-dawi/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana Awa da Dawi suna kiwo a daji, sai wani abu ya tsoratar da su. Kowa ya kama gabansa domin neman tsira. Suka ɓace wa juna. Da Dawi ya nemi ƙanwarsa bai gan ta ba, sai ya kama hanya ya tafi. Ita kuma ta nemi hanya ta rasa. Ta riga ta ɓata a dajin nan. Sai tafiya take ta yi, ba ta san inda za ta ba, har dare ya yi. Da ta gaji, kuma ga dare ya yi, sai ta sami gindin wata bishiya ta kwanta, har gari ya waye. Da sassafe tana […] - [Tatsuniyar Maye Da ’Ya’yansa](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-maye-da-yayansa/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani mutum a wani gari da ke gabas da garin nan. Yana da mace ɗaya da ’ya’ya biyu mata. Da suka isa aure Allah ya ba su masoya, aka yi musu aure aka kai kowacce ɗakinta. Bayan ’yan shekaru kowacce ta haifi ’ya’ya. Ana nan, sai aka aika musu uwarsu ta rasu; sai dai su ba su san cewa ubansu maye ne ba, kuma shi ne ma ya cinye uwar tasu. Shi ke nan yaran nan suka je gidan ubansu saboda zaman makoki, amma sai suka tarar uban nasu ya cinye gawar uwar tasu, […] - [Tatsuniyar Binta ’Yar Sarki](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-binta-yar-sarki/): Ga ta nan, ga ta nanku. An yi wani Sarki a wani gari mai mata biyu, kowacce tana da’ya. Yarinya ɗaya sunanta Binta, ɗayar kuma Falmata. Sarki yana ji da’ya’yan nan nasa, to amma fa ya fi son Binta don ita ce ƙarama, kuma ’yar amarya. Ana nan, rannan sai Sarki ya tafi wani gari mai nisa, kuma zai daɗe a can. Bayan ya tafi da ’yan kwanaki, sai ciwo mai zafi ya kama amaryarsa, watau mahaifiyar Binta. Da ta lura ciwon kamar ba wanda za ta tashi ba, sai ta kira kishiyarta ta gaya mata cewa tana jin ba za […] - [Tatsuniyar ’Ya’yan Sarki Da Ƙadangare](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-yayan-sarki-da-kadangare/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani Sarki da ’ya’yansa mata su biyu kyawawa. Amma tun suna ƙanana ya hana su fita waje domin tsaron lafiyarsu. Kullum suna gida har suka girma, suka isa aure. Ganin sun kai munzalin aure, sai ya bari suka ɗan fara fita waje. Ana nan, rannan dai Sarki ya ce zai aurar da su. Manema suka fito. Wannan ya zo, a ce a a, bai yi ba. Wancan ya zo, a hana shi. Wata rana dai sai Sarki ya ce a tara mutane, duk wanda ya kira sunan ɗaya daga cikinsu, to shi za a […] - [Tatsuniyar Tsurondi](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-tsurondi/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana wani Dodo ya rikiɗa ya zama mutum, ya shiga wani gari neman aure. Da ya je mazaunin wasu mutane sai ya gaishe su. Ya sanar da su cewa shi baƙo ne, amma neman aure ne ya kawo shi garin. Ya ƙara yi musu bayani cewa ya fi son kyakkyawar mace, wadda babu kamar ita a garin. Shi ke nan, sai mutanen nan suka yi masa kwatancen gidan wasu ’yan mata biyu, Awa da ƙanwarta Tsurondi. Da ya je gidan ya yi sallama, sai mai gidan ya fito suka gaisa. Daga nan baƙo ya […] - [Tatsuniyar Kurege Da Wayo](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-kurege-da-wayo/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani lokaci da aka yi yunwa, ba abinci. Wuya ta sa Kura da Maciji da Alade da Kurege suka haɗa kai, suka haɗu domin su haɗa gwiwa su yi noma tare. Sai suka zaɓi wani fili a dajin da suke, suka gyara, ya zama gonarsu. Ana nan, jim kaɗan kafin damina ta faɗi, sai Maciji ya ce shi ne zai yi sassabe, watau zai gyara gona, ya sare lallagowa ya kawar da yayi. Alade ya ce: “Ni zan yi mana huda.” Kura ta ce: “Ni zan nome mana gonar.” Kurege kuwa sai ya ce: […] - [Tatsuniyar ƊanAuta Da ’Yar Gwaggo](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-danauta-da-yar-gwaggo/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani mutum yana da ’ya’ya biyu mace da namiji. Macen ce babba, namijin ne ƙarami. Ita sunanta ’Yar Gwaggo, shi kuma sunansa Ɗan’auta. Da iyayensu za su rasu sai suka kira ’Yar Gwaggon suka ce: “Za mu bar miki ƙaninki Ɗan’auta. Kada ki ba shi wahala, duk abin da yake so ki ba shi; kuma duk abin da ya ce zai yi, kada ki hana shi; ki bar shi ya yi.” ’Yar Gwaggo ta ce: “To na ji.” Sai iyayen suka kwanta, suka rasu. To da ma iyayen sun bar musu dukiyar abinci da […] - [Tatsuniyar Gizo Da Sarki](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-gizo-da-sarki/): Ga ta nan, ga ta nanku. An yi wata tsohuwa a wani ɗan ƙauye; tana da ɗan maraƙinta kyakkyawan gaske; ga shi ƙosasshe. Ana nan wata rana Gizo ya je gidan wannan tsohuwa bara sai ya ga wannan maraƙi. Sai ya fasa bara ya fita daga gidan, ya sheƙa a guje sai gidan Sarki. Ya faɗi a gaban Sarki, ya ce: “Ko kunnuwan Sarki nawa ne?” Sarki ya ce: “Biyu.” Sai ya ce wa Sarki: “Ƙara biyu, a kan biyu ka sha labari.” Sarki ya ce: “Na ƙara.” Sai Gizo ya ce: “Akwai wani kyakkyawan sa a gidan wata tsohuwa, in […] - [Riya Da Tasirin Social Media](https://wikihausa.com.ng/riya-da-tasirin-social-media/): RIYA A MUSULUNCI: Duk wata ibada da musulmi zai yi don neman lada a wurin Allah, sharaɗi ne ya zama an yi shi ne saboda Allah Shi Shi kaɗai, ba tare da an haɗa Shi da wani mahaluki cikin wannan ibadar ba. Dole ne musulmi ya nufi Allah da kowace irin ibada da niyyar Allah ne Ya ba da umarnin a yi kuma Shi zai bada lada. Ya tabbata a hadisin Mahmud Bin Labid RA cewa Allah SWT zai faɗa wa waɗanda suka aikata wani aiki ba don Allah shi kaɗai ba, Allah zai ce musu ku je wurin waɗanda kuka […] - [Tatsuniyar Kura Da Kurege (Na Huɗu)](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-kura-da-kurege-na-hu%c9%97u/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana Kurege yana farauta a daji sai ya ga mushen Kurciya, sai ya ɗauka ya ajiye a kan itace. Ya ci gaba da tafiya sai kuma ya ga mushen Giwa, ya matsa kusa, ya dubi mushen da kyau, ya yi dariya. Daga nan sai ya kai wa Kura ziyara. Ya same ta tana saka zana sai yace: “Ki bari in kwanta a kan zanar nan taki.” Sai Kura ta ce: “To, kwanta mana.” Da Kurege ya kwanta sai ya lumshe idanunsa. Jim kaɗan kuma ya buɗe; sai ya ce da Kura: “Na yi mafarki […] - [Tatsuniyar 'Yar Sarkin Da Ta Saci Ɗinya](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-yar-sarkin-da-ta-saci-%c9%97inya/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wani Sarki yana da ‘ya’ya maza da mata da yawa. Wata rana an kawo masa ɗinya sai ya ajiye ta a dakinsa. Rannan sai tafiya ta kama shi. Sai ɗaya daga cikin ‘ya’yansa ta ɗauki dinyar ta cinye. Da Sarki ya dawo sai ya tarar an cinye masa ɗinya. Sai ya tara matansa da ‘ya’yansa ya tambaye su ko waye ya cinye masa ɗinya. Sai suka shiga yi masa rantsuwa cewa ba su suka ɗauka ba. Bayan an yi, an yi babu wanda ya amsa cewa shi ne ya ɗauka, sai Sarki ya ce […] - [Tatsuniyar Rimi Da 'Yar Amana](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-rimi-da-yar-amana/): Ga ta nan, ga ta nanku. An yi wani gari mai yawan jama’a da Sarkinsu mutumin kirki. Shi ke nan akwai wani mutum mazaunin wannan gari shi da matarsa da’yarsu ɗaya. Suna nan sai wata rana ciwon ajali ya kama matar wannan mutum. Kafin ta rasu sai ta kira shi ta ce: “Mai gida, ni fa ina jin ba zan tashi daga ciwon nan ba, amma ga amanar ‘yarmu nan ka kula da ita sosai. Kada ka bari wani mugun abu ya same ta.” Mijin ya amsa. Da matar ta rasu sai shi kuma uban yarinyar ya ci gaba da renon […] - [Tatsuniyar Gizo Da Damon Sarki](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-gizo-da-damon-sarki/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana Sarki ya kawo Damo babba. Sai ya kai shi gonarsa bayan gari. Bayan ‘yan kwanaki kaɗan ya sake kawo wasu don kiwo, kuma yasa aka yi shela a gari cewa kada a taɓa su, tare da bayanin cewa duk wanda ya yanka ya ci zai mutu. Ana nan, sai wata rana kwaɗayin nama ya kama Gizo, sai ya zagaya inda Damon Sarki suke. Ba tare da jin wani tsoro ba ya kama ɗaya ya yanka, ya kawo wa matarsa ta dafa masa ya cinye. Da ya ji daɗi sai kullum ya zagaya ya […] - [Tatsuniyar Talipaku Da Kurciya](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-talipaku-da-kurciya/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana tsuntsuwa Talipaku da Kurciya suka yi sheƙa a bishiya ɗaya. Da lokacin saka ƙwan da suka ɗauka ya zo, sai suka haɗa ƙwansu a wuri ɗaya. Bayan sun gama kwanci, sai suka ƙyanƙyashe ƙwayayensu, suka sami ’ya’yansu guda biyu. Suna nan a haka, kullum sai su fita neman abincin’yan tsakinsu. Kansu ya haɗu, komai na tafiya rumui-rumui. To ashe ita Talipaku ba ta jin daɗi da bakin ’yarta ya yi tsawo fiye da na’yar Kurciya, wadda ba wani abu da ya dami ’yarta, kyakkyawar gaske. Duk lokacin da za su fita neman abincin […] - [Tatsuniyar Yarima Da Labbi](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-yarima-da-labbi/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wani Bafulatani yana yawo a jeji sai ya tarar da wata mata a zaune a gindin wata kuka. Yau da gobe yana zuwa har suka saba. Kullum haka yakan same ta bayan azahar ko kuma dab da azahar. Duk sanda ya je takan ba shi ruwa ko kunu ya sha. Bayan sun yi hira kuma sai ya koma yaci gaba da kiwon dabbobinsa. Wani lokacin kuma yakan kai mata madarar shanu da dambu. Ashe da man matar nan ba mutum ba ce, kasa ce da ke zaune a cikin kogon wannan kukar take rikiɗa ta […] - [Tatsuniyar Budurwa Mai Neman Ganyen Miya](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-budurwa-mai-neman-ganyen-miya/): Ga ta nan, ga ta nanku. Akwai wata budurwa mai suna Yakadi a wani ɗan ƙauye da ke nan kusa da bakin rafi. Wata rana sai mahaifanta suka aike ta lambu ta samo ganyen miya. Ta shirya ta kama hanya tare da ƙannenta, suka je, suka samo ganyen miya. A kan hanyarsu ta dawowa gida sai suka haɗu da wata tsohuwa ta ce da su: “Sannunku ’yanmata, don girman Allah ku taimake ni da ganyen ɗan kaɗan mana.” Sai ita Yakadi ta ce: “Ba za a bayar ba.” Suka ci gaba da tafiya, da suka kai kusa da wani dutse sai […] - [Tatsuniyar Dagaci Da Malaminsa](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-dagaci-da-malaminsa/): Ga ta nan, ga ta nanku. An yi wani Dagaci a wani gari yana da matarsa, to amma matar ba ta taɓa haihuwa ba. Ba tare da saninsa ba, wata rana matar wani babban malami ta je wurin matar Dagaci hira a gidansa. Suna cikin hira sai matar Dagacin ta fara ba matar malamin labarinta shi ne halin da take ciki na rashin haihuwa. Kuma ga shi maigidanta, watau Dagacin, ya ce yana son ya sami ’ya’yan da za su zo su gaje shi. Kuma ya ba matar tasa wasu ’yan watanni, idan ba ta sami ciki ba zai kore ta, […] - [Tatsuniyar Yarinya Kyakkyawa Da Wanta](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-yarinya-kyakkyawa-da-wanta/): Ga ta nan, ga ta nanku. An yi wani mutum a wani ɗan ƙauye yana da mata da ’ya’ya. Ana nan, sai ɗaya daga cikin matansa ta haifa masa yarinya kyakkyawa. Bayan kwana bakwai sai ya raɗa mata suna Kwambal. Sannu a hankali, kwanci-tashi, yarinyar ta girma, kyanta ya ƙara bayyana, har ya kasance duk garin ba mai kyau kamar nata. Da ta isa aure sai mutane suka yi ta tururuwa suna zuwa neman aurenta, wancan ya zo, amma sai ta ƙi, haka aka yi ta fama amma babu wanda ya yi nasarar samunta. Kwatsam sai wani yayanta, wanda suke ’yan […] - [Tatsuniyar Kurege Da Kura (Na Uku)](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-kurege-da-kura-na-uku/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana Kurege ya je gidan Kura ya ce su tafi farautar kayan daɗi a jeji. Kura ta amince. Suka shirya suka kama hanyar daji. Da suka isa bakin rafi sai Kura ta ce, to su rabu a nan. Ta ce tunda shi Kurege ƙarami ne ya bi cikin ciyawa, ita kuma Kura da yake babba ce, za ta bi kan hanya. Da fari Kurege ya ƙi yarda, amma daga baya ya haƙura, ya bi cikin ciyawa yana tafiya har ya kai ga gidan zuma, ya tarar ƙudan Zuma suna ciki. Sai ya saurare su […] - [Tatsuniyar Cin Kasuwar Sama](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-cin-kasuwar-sama/): Ga ta nan, ga ta nanku. Da Zanzaro da Barangunda suka ƙulla abota. Wata rana suka je cin kasuwar sararin sama, da nufin su dawo da yamma. Da suka je suka dawo sai suka tarar Gizo ya fito ya zauna ya kame a kan kujera, yana shan iska. Da man hanyar ta bi ta ƙofar gidan Gizon ne. Da Gizo ya gan su sai ya tashi ya yi musu maraba, suka amsa masa, har suka ba shi tsarabar kasuwa. Gizo da matarsa Koƙi suka ji daɗin tsarabar, sai Koƙi ta shawarci Gizo da ya bi su ko shi ma ya samo […] - [Labari Mai Taken Fansar Hawayen Kakana](https://wikihausa.com.ng/labari-mai-taken-fansar-hawayen-kakana/): 15/5/2025. ADADIN KALMOMI:2876 Gidan mu na gado yana tsakiyar badalar garin mu, shahararru ne a sanaʼar sarrafa fata wacce aka fi sani da dukanci. A wata sharariyar unguwa da ke zagaye da kasuwanni. Kasuwanci da kiwo shi ne alʼfaharin mu, kamar kowanne gidan bahaushe kakana malam Gambo yana da mata biyu Hauwaʼu ita ce amarya Rakiya uwar gida. Amarya ‘ƴa’ƴanta biyu duk mata, uwar gida ‘ƴa’ƴanta uku maza biyu mace ɗaya. Kakana shaharren badukku ne duk garin mu kowa ya san shi kuma duk wanda ya iya aikin dukanci a garin mu, gurin sa ya koya, masauratar garin na alfari da […] - [Labari Mai Taken Wata Sabuwa](https://wikihausa.com.ng/labari-mai-taken-wata-sabuwa/): Taƙaitaccen labari ne duba da yanayin rayuwa da ake ciki don yin hannunka mai sanda ga alʼumma daga taskar uwar muminai💐💐💐💐. 07033941914. Yau ma kamar kullum na tashi raina a cunkushe kallon kowa nake kamar maƙiyi, nai ƙoƙari na jawo hisnulmuslim don yin azkar ɗin safiya. Duk halin da nake ciki ba ya hana ni yi, na gama na jawo wayata misalin 6am akwai Online classes na islamiya da nake bi duk safiya ina buɗe data telegram na shiga, inda na lalubo ajin da nake bi haka nan nake jin rai duk a ɓace cikin saʼa na samu Malam ya fara, […] - [Yadda Ake Addu'ar Nema Wa 'Ya'ya Tsari](https://wikihausa.com.ng/yadda-ake-adduar-nema-wa-yaya-tsari-2/): Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana nema wa Hasan da Husain tsari da wannan addu’ar: أُﻋ ِ ﯿﺬﱠِﺑِﻜَﻠِﻤَﺎتِﷲﻟﺘﱠﺎﻣﱠﺔﻣِﻦ ْﻛُﻞ ﺷَﯿْﻄَﺎن ٍﱢﱠو َھَﺎﻣﱠﺔٍ ِو َ ﻣِﻦ ْﻛُﻞ ﻋَﯿْﻦ ٍ ﻻَﻣﱠﺔٍ ُ Uʿīzu bikalimātillāhi t-tāmmati, min kulli shayṭānin wa hāmmah, wa min kulli ʿaynin lām. Ina neman muku tsari da Kalmomin Allah Cikakku daga dukkan Shaidan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa. Danna nan don karanta Yadda Ake Addu’ar Barka Ga Wanda Aka Yi Wa Haihuwa Edita@rumasau-kallamu - [Tatsuniyar Gizo Da Matarsa Ƙoƙi](https://wikihausa.com.ng/tatsuniyar-gizo-da-matarsa-%c6%99o%c6%99i/): Ga ta nan, ga ta nanku. Wata rana Koƙi matar Gizo ta fito fili ta matsa masa a kan zancen gona da amfanin yin noma. Gizo ya yi fushi, amma duk da haka ya je kasuwa ya auno tiya biyu ta irin gujiya ta shukawa. Da damina ta faɗi aka yi isasshen ruwa, sai ya ce da Koƙi ta je ta soya irin. Ta so ta yi masa musu, amma sai ta kanne, watau ta danne zuciyarta, ta je ta soya da gishiri kaɗan. Kamar da gaske, tun da asubar fari Gizo ya ɗauki sunguminsa da goransa cike da fura, sai […] - [Yadda Ake Addu'ar Barka Ga Wanda Aka Yi Wa Haihuwa](https://wikihausa.com.ng/gaisuwar-barka-ga-wanda-aka-yi-wa-haihuwa-da-abin-da-shi-kuma-zai-fa%c9%97a/): و َ ﺷَﻜَﺮ ْ ت َ ﻟَﻚ َ ،اﻟْﻤَﻮ ْ ھُﻮبِ ﻓِﻲﻟَﻚ َ ﷲَُ ﺑَﺎر َ ك َ.ﺑِﺮ َ هُ و َ رُزِﻗْﺖ َ ،أَﺷُﺪﱠهُ و َ ﺑَﻠَﻎَ ،اﻟْﻮ َ اھِﺐ َ Washakarat laka,al-mawhubi fīka,laka Allahu bāraka,bihī wa ruziqta,ashuddahu wa balagha, al-wāhibu. Allah ya yi albarka ga abin da aka azurta ka da shi, kuma Ya sa ka godewa Wanda ya ba ka (shi), kuma Ya sa shi ya rayu har zuwa ga matukar karfinsa, kuma a azurta ka da biyayyarsa. Karanta Yadda Ake Addu’ar Gamuwa Da Abokan Gaba Ko Wani Mai Iko  Edita@rumasau-kallamu ## Pages - [Login/Register](https://wikihausa.com.ng/tds-login-register/) - [Dora Rubutu](https://wikihausa.com.ng/tura-rubutu/) - [Abokan hulɗa](https://wikihausa.com.ng/abokan-hul%c9%97a/) - [Members](https://wikihausa.com.ng/members-2/): [ultimatemember form_id=”19572″] - [User](https://wikihausa.com.ng/user/): [ultimatemember form_id=”19571″] - [wpwBot Mobile App](https://wikihausa.com.ng/wpwbot-mobile-app/) - [Dora Rubutu](https://wikihausa.com.ng/dora-rubutu/) - [taimake mu](https://wikihausa.com.ng/taimake-mu/) - [Ƙa’idojin Rubutu](https://wikihausa.com.ng/kaidojin-rubutu/): Ka’idojin rubutun Hausa domin marubutan WikiHausa. A kiyaye domin ingantaccen rubutu Marubuta da dama na fama da ƙarancin fahimtar ƙa’idojin rubutun Hausa, hakan kuwa ya samo asali ne sakamakon mafi yawancinsu ba harshen Hausa suka karanta ba. Wasu sun fara rubutu ne kawai saboda suna da sha’awa, ba tare da sun san da zaman ƙa’idojin ba. Sanannen abu ne cewa da yawan mutane na yaudarar kansu ta hanyar tunanin za su iya amfani da kasantuwarsu Hausawa su yi rubutu da Hausa hakan nan ba tare da bin ƙa’idojin harshen ba. Irin waɗannan mutane da dama za ka same su cikin da […] - [Rijista](https://wikihausa.com.ng/rijista/) - [My account](https://wikihausa.com.ng/tds-my-account/) - [Tallafa mana da kudi](https://wikihausa.com.ng/tallafa-mana-da-kudi/) - [Ayyukan Mu](https://wikihausa.com.ng/ayyukan-mu/) - [Yara](https://wikihausa.com.ng/post-submit/): Tarbiyyar yara - [Blog](https://wikihausa.com.ng/blog/) - [Glossary](https://wikihausa.com.ng/glossary/): [glossary] - [tuntubemu_mobile](https://wikihausa.com.ng/tuntubemu_mobile/) - [home_mobile](https://wikihausa.com.ng/home_mobile/) - [Ƙamusu](https://wikihausa.com.ng/%c6%99amusu/): Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi - [Terms Dictionary](https://wikihausa.com.ng/terms-dictionary/) - [Bidiyo da Sautuka](https://wikihausa.com.ng/bidiyoyi/) - [Jagorori](https://wikihausa.com.ng/malamai/): Ma’aikatan WikiHausa Aiki da ƙwarewa shi ne ɗaya daga cikin dalilan da suka saka wikihausa ta yi fice a faɗin Nijeriya. Kuma haƙiƙa ba za mu taɓa barin kowane daya daga cikin maaikatanmu a baya ba domin da gudunmowarsu ne muka kawo yanzu. Muna ƙara godiya ga shahararrun ma’aikatan da muke aiki da su a wikiHausa. Jagorori - [Manufar Mu](https://wikihausa.com.ng/munufar-mu/) - [Dokoki](https://wikihausa.com.ng/dokoki/) - [Yi Tambaya](https://wikihausa.com.ng/yi-tambaya/) - [Ɓangarori](https://wikihausa.com.ng/bangarori/) - [Tuntuɓe mu](https://wikihausa.com.ng/tuntube-mu/): tuntubi wikihausa ta hanyar cike wannan fom din ko lambobin waya da suke a gefe. da adireshin ofishin mu domin ganawa da mu da suke a gefe. wikiHausa insakulofidiya ce (kundin ilimi) data tattaro ilimin bangarori da dama wanda ya shafi dukkan ilimins dan adam, ba manufarta bane tallata wata haja ta wata akidar siyasa ko rayuwa ba, kuma ba huruminta bane tallace tallacen rayuwa da kuma kayan kasuwanci ba, ba kuma labaran yau da kullum ba. wikiHausa ta kowace, kuwa zai iya taimakawa da ilimi ko gyara kuma ya kuma yi amfani da abubuwan dake cikinta. - [Shafin Farko](https://wikihausa.com.ng/) ## Optional - [Agent (MCP protocol)](websites-agents.hostinger.com/wikihausa.com.ng/mcp) [comment]: # (Generated by Hostinger Tools Plugin)